Sunday, December 21
Shadow

Duk Labarai

Wata Sabuwa: An gano Makudan kudaden da shugaba Tinubu ya ware Kusa Tiriliyan 2 na gyaran Titunan Najeriya, Fiyade da rabin kudin Legas da kudancin Najeriya za’awa aiki dasu inda Arewa ta samu kaso kadan

A zaman majalisar Zartaswa na Ranar Litinin din data gabata, ta Amince da fitar da Naira Biliyan N787.14 da Dala Miliyan $651.7 dan yin gyaran Tutuna a fadin Najeriya. Saidai binciken tsanaki da Dan Gidan Tanko Yakasai yayi ya nuna cewa Gaba dayan Dala miliyan $651.7, kusan Naira Tiriliyan daya duk Legas za' kashewa. Hakanan daga cikin Naira Biliyan N787.14 ita kuma Naira Biliyan N420Billion sama da kaso 50 cikin 100 na kudin kenan, Kudancin Najeriya za'a kashewa. https://twitter.com/dawisu/status/1919652843373441175?t=Zz8CdbwI_NdBm7UFbZ2FUw&s=19 Hakan na nufin gaba daya baifi Naira Biliyan dari 3 bane za'a kashewa Arewa. Dama dai a baya An so canja fasalin rabin kudin Haraji dan baiwa jihar data fi kawo kudi rabo me tsoka.
Dalla-Dalla: Yaronnan dan shekaru 18 da ya dirkawa mata 10 ciki yayi bayanin dabarar da yakewa matan suna yadda dashi

Dalla-Dalla: Yaronnan dan shekaru 18 da ya dirkawa mata 10 ciki yayi bayanin dabarar da yakewa matan suna yadda dashi

Duk Labarai
Yaronnan dan jihar Anambra wanda aka ruwaito ya dirkawa mata 10 ciki a cikin watanni 5 yayi bayani dalla-dalla game da irin dabarar da yake amfani da ita wajan yaudarar matan suna yadda dashi. Yaron mai shekaru 18 an daukoshi daga kauyene aka kaishi wajan wani dan kasuwa dan ya koya masa kasuwanci. Saidai yaron ya dirkawa diyar me gidan ciki sannan ya dirkawa yarinyar shagon me gidan nasa ciki. Megidan ya koreshi inda ya mayar dashi kauye, saidai watanni biyu bayan mayar dashi kauyen, a camma ya dirkawa mata 8 ciki. Kwamishiniyar mata da walwala ta jihar Anambra, Ify Obinabo tace mahaifiyar yaron ce da kanta ta kaishi kara wajenta. Tace abin ya bata mamaki dan hakane ma ta kira yaron take tambayarsa shin wai yana da wani lakani ne ko Asiri da yake amfani dashi wajan yaudarar ma...
“Babu ƙanshin gaskiya a cewar da ake yi ƴan ta’adda na da makaman da su ka fi na jami’an tsaron Nijeriya” Inji Ministan Tsaron Nijeriya Muhammad Badaru Abubakar.

“Babu ƙanshin gaskiya a cewar da ake yi ƴan ta’adda na da makaman da su ka fi na jami’an tsaron Nijeriya” Inji Ministan Tsaron Nijeriya Muhammad Badaru Abubakar.

Duk Labarai
“ Babu ƙanshin gaskiya a cewar da ake yi ƴan ta'adda na da makaman da su ka fi na jami'an tsaron Nijeriya” Inji Ministan Tsaron Nijeriya Muhammad Badaru Abubakar. A Cikin Shekaru Biyu Na Gwamnatin Tinubu An Sami Cìkakken Tsaro Akan Hanyar Abuja Zuwa Kaduna, Wanda A Baya Ya Taɓa Kasancewa Tungar Masu Ģarkuwa Da Mutane, Inji Ministan Tsaro, Badaru "Daga watan Mayun 2023 zuwa yanzu mun yi nasarar murƙushe ƴan ta'adda har 13,000, kazalika an kawar da shugabannin Boko Haram sama da 300 "A Maiduguri, a baya da an ce Gambaru, Bama, ka san an ambaci hanya mai hatsarin gaske, amma a yanzu hakan ya zama tarihi, duk wannan ya faru ne a cikin shekaru 2 na wannan gwamnatin". Sojojin Nijeriya Sun Cancanci Lambar Yabo Fiye Da Wanda Ake Yi Musu A Yanzu, Duba Da Yadda Suke Yin Nasara Àka...
Da Duminsa: Shugaban Sojojin Najeriya ya koma da zama jihar Borno dan magance matsalar tsaro

Da Duminsa: Shugaban Sojojin Najeriya ya koma da zama jihar Borno dan magance matsalar tsaro

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban sojojin Najeriya, General OO Oluyede ya koma jihar Borno da zama dan kula da yanda sojoji ke aikin magance matsalar tsaro. A 'yan Kwanakinnan dai Hare-haren kungiyar Bòkò Hàràm sun yawaita inda aka gansu da makamai na zamani. Majalisar tarayya ma ta bayyana cewa, 'Yan Bòkò Hàràm din sun fi sojojin Najeriya makamai masu kyau. Wasu na ganin komawar shugaban sojojin zuwa jihar Borno zai taimaka matuka wajan magance matsalar tsaron jihar da makwabciyarta Yobe.
A hukumance Sanata Kawu Sumaila mai wakiltar mazaɓar Kano ta Kudu ya koma jam’iyyar APC daga NNPP bayan Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Godswill Akpabio ya karanta wasiƙar sauya sheƙarsa a yayin zaman majalisar na yau Laraba

DAGA ZAUREN MAJALISA : Sanata Kawu Sumaila (Kano ta Kudu) ya sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC a zaman majalisar dattawa na yau. Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya karanta wasikar sauya shekar tasa. Inside Bauchi State07-05-2025
Ina gama Wa’adina na Mulki zan koma sana’ar da nake yi kamin in zama Gwamna watau Walda>>Inji Gwamnan jihar Nasarawa

Ina gama Wa’adina na Mulki zan koma sana’ar da nake yi kamin in zama Gwamna watau Walda>>Inji Gwamnan jihar Nasarawa

Duk Labarai
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi karin haske kan sana’ar da zai fara bayan ya kammala wa’adin mulkinsa zango na biyu. Gwamna Sule yace zai koma sana’ar da ya fara yi tun kafin fara mulkin jihar Nasarawa wato sana,ar walda, da zarar ya kammala wa’adin mulkinsa a shekarar 2027. Yace akwai alkairi a cikin Sana’ar ta walda sosai ,Inda ya nemi matasa da su dage da Sana’a Gwamna Sule ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron tattaunawa da hukumar samar da wutar lantarki ta karkara ta shirya tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar Nasarawa. Ya kuma yi amfani da damar wajen tabbatarwa da masu sha’awar zuba jari cewa jihar Nasarawa na da ƙwararrun ma’aikata, inda ya nuna cewa jihar na da ɗimbin matasa masu horo da shaidar ƙwarewa da za su iya tallafawa mas...