Muguntar da El-Rufai yayi a baya ce take binsa saboda Alhaki kwikwiyo ne, Kuma ba zai yi nasara ba, saboda mutane da yawa basu yadda dashi ba saboda mayaudari ne kuma maciyin amanane>>Buba Galadima
Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa, Tsohon gwamnan Kaduna, Malan Nasiru Ahmad El-Rufai ba zai yi nasara ba a kokarin da yake na hada kan 'yan jam'iyyar Adawa da kuma kalubalantar Gwamnatin Tinubu a zaben shekarar 2027.
Buba Galadima ya bayyana hakane a wata hira da jaridar Punchng ta yi dashi wadda shafin hutudole ya bibiya.
Yace El-Rufai ya saba ya shiga jam'iyya wadda me karfi ce tana kan hanyar Nasara shima ya samu Nasara.
Yace amma yanzu da yake kokarin farowa daga farko a yanzu ne zai gane wahalar da ake sha wajan gina jam'iyya da siyasa.
Yace amma matsalar El-Rufai itace bashi da alaka me kyau da mutane, ya taka mutane da yawa kuma mayaudari ne maci yin amanane dan haka babu wanda ya yadda dashi kuma dalili kenan da yasa ba zai yi nasara ba.
Yace El-Rufai yayi maga...








