Mijinta ya kamata tana yiwa dan kishiyarta me shekaru 15 fyade, saidai duk da haka ta sake kiran yaron inda take tambayarshi ta gamsar dashi kuwa?
Rahotanni sun bayyana cewa Mijin wannan matar wadda ma'aikaciyar Jinya ce ya kamata tana yiwa dansa, watau dan kishiyarta me shekaru 15 fyade.
Lamarin ya sanya matar me shekaru 35 ta rasa lasisinta na aikin jinya.
Rahoton yace matar ta kwashe kwanaki tana ta jan hankalin dan kishiyar tata, kamin daga bisani ta danneshi ta mai fyade.
Alexis Von Yates na zaunene a jihar Florida ta kasar Amurka inda a yanzu take jiran zuwa watan July dan yanke mata hukuncin wannan aika-aika da ta yi.
Ranar da abin zai faru matar baban nasa ta rika gaya masa cewa, tana jin sha'awa kuma bata yi juma'i ba na tsawon lokaci.
Anan ne dai har suka kai ga aikata abinda suka aikata, bayan da babban ya dawo sai ya iskesu tsirara a kwance a falo.
Anan ne ya dauki yaron ya mayar dashi gidan kakanninsa.
...








