'Yar Najeriya kuma ma'aikaciyar Kwastam, Akpevwe Ogboru data tafi kasar Belgium a mashin ta dawo Najeriya bayan kwashe kwanaki 72.
Bayan dawowarta ta samu kyakkyawar tarba a hannun abokan aikinta.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Lura da irin Arzikin ma'adanan karkashin kasa da Allah yawa kasarnan, bai kamata ace akwai talaka a kasarba
Shugabab ya bayyana hakane a wajan taro kan Arzikin ma'danan karkashin kasa da Allah yawa Najeriya da ya gudana a Abuja.
Sakataren Gwamnatin tarayya, George Akume ne ya wakilci shugaban kasar a wajan taron.
Ya bayyana cewa, Gwamnatin tarayya zata yi dukkan mai yiyuwa wajan samar da yanayi me kyau na zuba hannun jari a kasarnan ta bangaren ma'adanan karkashin kasa.
Sannan ya yi kira ga kasashen Afrika dasu yi amfani da ma'adannan karkashin kasar da Allah ya hore musu dan karfafa tattalin arzikin su.
Wani ba'amurke me suna Martin ya bayyana cewa, kwanaki 4 da suka gabata ya shiga addinin Musulunci.
Yace amma kuma an matsa masa a wajan aikinshi cewa sai ya bar addinin Musulunci.
Yace shi kuma ya zabi ya ci gaba da kasancewa a addinin Musulunci.
ya wallafa hakane a shafinsa na sada zumunta.
https://twitter.com/D_Maaartin/status/1978489878590406762?s=19
Rahotanni sun ce, cocin Vatican ta samar da wajan Sallah a dakin karatunta dan musulmai masu kai ziyara.
Daya daga cikin jagororin cocin Giacomo Cardinali ne ya tabbatar da hakan.
Sanarwar tace an dauki matakinne dan samar da dama ga kowa ya kai ziyara dakin karatun dan gudanar da bincike.
Rahotanni sun ce Laiyukan ababen hawa sun fara yawa a gidajen Man fetur a sassa daban-daban na Najeriya a yayin da ake fama da hauhawar farashin man a garuruwa daban-daban.
Rahoton yace Farashin litar man fetur din ya kai Naira 1000.
'Yan kasuwar man fetur sun zargi Depot dake sayar musu man a farashin sari da cewa, sune suka sa man yayi tsada dan sun kara farashin da suke sayar musu da man.
Hakan na zuwane duk da ga matatar man fetur ta Dangote a Najeriya kuma ya fara kai man fetur din zuwa wasu gidajen man kyauta ba kudin dako.
Lauyoyin Nnamdi Kanu sun bayyana cewa, basu yadda da sakamakon gwajin Lafiyar da aka masa ba inda suka ce ta yaya gashi an tabbatar bashi da lafiya amma ace wai zai iya tsayawa a gaban Kotu.
Lauyoyin bayan zaman kotun a yau, Alhamis sun bayyana cewa, suna kira ga kungiyar Likitoci ta kasa data kiyaye kada ta batawa kanta suna.
https://twitter.com/General_Somto/status/1978774791155806233?t=L8YzAemwn84Rd-Nqt73sww&s=19
A baya dai sakamakon da likitoci suka fitar akan Lafiyar Nnamdi Kanu sun ce zai iya ci gaba da tsayawa a gaban kotu dan ci gaba da masa shari'a sannan kuma Asibitin sha ka tafi na DSS zai iya ci gaba da dubashi saboda rashin lafiyar tasa bata yi tsanani ba.
Malam ya bayyana cewa, Bayan da Malam Lawal Triumph ya kare kansa a gaban Kwamitin Shura na Kano, akwai 'yan darika Guda 6 da suka kirashi suka ce sun daina Darika.
Yace cikinsu hadda mace.
Malam Yayi kira ga Gwamnan Kano da ya daina yadda ana sakashi a wannan rikicin inda yace ya barsu da 'yan Darikar su sun san yadda zasu yi dasu.
https://www.tiktok.com/@ali_d_abba/video/7561178610330045718?_t=ZS-90b3UnM1PUn&_r=1
Matashinnan na Maiduguri da yayi ridda ya koma Kirista ya jawo cece-kuce sosai a kafafen sada zumunta.
Wasu sun rika tambayar ko yana cikin hayyacinsa ya dauki wannan mataki?
Saidai a nasa sharhin, Abdullahi yayi zargin cewa, Kudi aka baiwa matashin ya bar Addinin Musulunci.
Saurari Sharhin Abdullahi a Bidiyon kasa
https://www.tiktok.com/@abdallahtoyota0/video/7561065754917899528?_t=ZS-90b1uA5bpzM&_r=1
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour Party a zaben shekarar 2023, Peter Obi ya bayyana cewa, shekaru 4 sun isheshi ya gyara Najeriya idan aka zabeshi shugaban kasa.
Peter Obi ya kuma baiwa magoya bayansa tabbacin zai tsaya takarar shugaban kasa a 2027.
Ya bayyana hakane a ganawar da yayi da manema labarai a Abuja ranar Laraba.
Ya kuma ce yana da Kwarewa da cancantar zama shugaban kasa a Najeriya.
Obi ya kuma bayar da tabbacin cewa, duka 'yan Najeriya dake son Najeriya da arziki zasu taru ne dan kayar da Gwamnati me ci.
Rahotanni sun bayyana cewa, alkaluman farashin kayan abinci ya sauka a Najeriya inda a yanzu yake a maki 18.02 a watan Satumba daya gabata.
Idan aka kwatanta da watan Augusta daya gabata, Alkaluman na matsayin maki 20.12 wanda hakan ke tabbatar da an samu sauki sosai.
Hukumar kula da kididdiga ta kasa, NBS ce ta bayyana hakan a sanarwar data fitar ranar Laraba. Rabon da makin na NBS ya sakko kasa da 20, shekaru 3 kenan.