Sunday, December 21
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyo: Wannan mutumin yayi ikirarin yin aiki a karkashin Kamfanin Sheikh Bala Lau inda yace an rike masa hakkinsa ba’a biyashi ba

Kalli Bidiyo: Wannan mutumin yayi ikirarin yin aiki a karkashin Kamfanin Sheikh Bala Lau inda yace an rike masa hakkinsa ba’a biyashi ba

Duk Labarai
Wani mutum ya dauki hankula sosai a kafafen sadarwa bayan da yayi zargin cewa yana aiki ne a wani kamfani dake karkashin shugaban Izala, Sheikh Bala Lau amma ba'a biyashi hakkinsa ba. Yace wasu daga cikin abokan aikinsa sun gudu saboda babu Albashi a aikin. Mutum ya bayyana cewa an kaisu aikin tsaron Titin Jirgin kasa ne. Kalli Bidiyon a kasa: https://www.tiktok.com/@najib.zubairu/video/7495804901910465797?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7495804901910465797&source=h5_m&timestamp=1745618943&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&ut...
Gaba daya Albashin mu ya kare a biyab kudin wuta da sakata katin waya>>Inji Kungiyar Kwadago

Gaba daya Albashin mu ya kare a biyab kudin wuta da sakata katin waya>>Inji Kungiyar Kwadago

Duk Labarai
Kungiyar kwadago NLC ta koka da cewa albashin dubu 70 da ake biyan ma'aikata a biyan kudin wutar Lantarki da sayen katin waya yake karewa. Shugaban kungiyar ta NLC, Joe Ajaero ne ya bayyana hakan ga manema labarai. Ya bayyana cewa hakanan masu gidajen haya da ababen hawa na haya duk sun kara kudi. Yace zasu hada kai da tawakararsu kungiyar TUC dan kwatarwa da talakawa 'yanci.
Ji yanda dan Najeriya ya cirewa dan sandan kasar Malaysia kunne ta hanyar cizo bayan da aka kamashi da karfin tsiya

Ji yanda dan Najeriya ya cirewa dan sandan kasar Malaysia kunne ta hanyar cizo bayan da aka kamashi da karfin tsiya

Duk Labarai
Wani dan Najeriya ya cirewa dan sandan kasar Malaysia kunne ta hanyar cizo bayan da aka kamashi a wani Asibiti. An kama dan Najeriyar ne a Metro Prima, Kepong, Kuala Lumpur, Malaysia. Shugaban 'yansandan birnin Kuala Lumpur Datuk Rusdi Mohd Isa ya tabbatar da kamen inda yace sun kama dan Najeriyar ne bayan da aka kirasu aka shaida musu cewa wani dan kasar waje ya tayar da hankali a wani Asibiti. Ya kara da cewa, lamarin ya farune ranar Juma'a da misalin karfe 10:03 na safe April 25, 2025. Yace bayan an kama mutumin me shekaru 38, an hadashi da dansanda ya kaishi Ofis inda aka ajiyeshi a bayan mota da ankwa a hannunsa. Saidai a hakanne ya kama kunnen dansandan ta baya ya cizge. Yace an kai dansandan Asibiti yayin da shi kuma wanda ake zargi ana ci gaba da bincike akansa.
Kalli Hotuna: Shugaba Tinubu ya aika wakili zuwa wajan daurin auren Rarara

Kalli Hotuna: Shugaba Tinubu ya aika wakili zuwa wajan daurin auren Rarara

Duk Labarai
Mallam Abdulaziz Abdulaziz Ya Wakilci Shugaban Ƙasa Tinubu Wajen Halartar Ɗaurin Auren Rarara Da A’isha Humaira. {"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya wakilta mai taimaka masa na musamman kan harkokin sadarwa, Mallam Abdulaziz Abdulaziz wajen halartar ɗaurin auren shahararren mawaƙin jam’iyyar APC, Dauda Adamu Abdullahi (Rarara) da amaryarsa, A’isha Humaira. Auren wanda aka ɗaura yau a garin Maidugurin Jihar Borno, ya samu halartar mataimakin shugaban majalissar dattawa ta ƙ...
Bill din wuta da akw kawo mana yayi yawa ba zamu iya biya ba shiyasa zamu koma amfani da Sola>>Inji Fadar shugaba Tinubu

Bill din wuta da akw kawo mana yayi yawa ba zamu iya biya ba shiyasa zamu koma amfani da Sola>>Inji Fadar shugaba Tinubu

Duk Labarai
Fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa, kudin wutar lantarkin da suke biya a duk shekara ya kai Naira Biliyan 47. Fadar tace dan haka ba zata iya ci gaba da biyan wadannan kudi bane shiyasa shugaba Tinubu ya amince a saka solar. Shugaban Hukumar makamashi ta kasa, Mustapha Abdullahi ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Juma'a. Yace kuma wannan na kan hanyar kokarin Gwamnati na samar da makamashi wanda baya gurbata Muhalli.
Ƴan wasan Barca da Real da za su kara a wasan ƙarshe na Copa del Rey

Ƴan wasan Barca da Real da za su kara a wasan ƙarshe na Copa del Rey

Duk Labarai
A ranar Asabar ne manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Sifaniya, Real Madrid da Barcelona za su ɓarje gumi a wasan ƙarshe na gasar Copa del Rey. Wasan wanda ake yi wa laƙabi da el-classico - na ɗaya daga cikin wasannin da suka fi jan hankalin masoya ƙwallon ƙafa a faɗin duniya. Ƙungiyoyin sun kawo wannan matakin ne bayan da Real ta doke Real Sociedad da ci 5-4 a wasa gida da waje. Ita ma Barcelona ta kawo matakin ne bayan fitar da Atletico Madrid da ci 5-4 gida da waje. Barcelona ce ƙungiyar da ta fi ɗaukar kofin na Copa del Rey a tarihi, bayan da ta ɗauki kofin har sau 31, yayin Real Madrid ta ɗauki kofin sau 20. A yanzu haka Barcelona ce ta ɗaya a kan teburin La Liga da maki 76, yayin Real Madrid ke matsayi na biyu da maki 72, inda ya rage wasa biyar a ƙarƙare gasar ta bana. ...
Akpabio zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa jana’izar Fafaroma Francis

Akpabio zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa jana’izar Fafaroma Francis

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike da wata tawaga ta musamman ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisar dattawan ƙasar Godswill Akpabio zuwa birnin Vatican domin halartar jana’izar Fafaroma Francis a ranar Asabar 26 ga watan Afrilu. Wata sanarwa da ta fito daga ofishin mai magana da yawun shugaban ƙasa Bayo Onanuga ta ce tawagar za ta miƙa wata wasiƙa ta musamman da ke ɗauke da sakon jaje daga shugaba Tinubu zuwa ga muƙaddashin shugaban fadar Vatican. Sauran mambobin tawagar sun haɗa da ƙaramar ministar harkokin waje, Ambasada Bianca Odumegwu Ojukwu da Archbishop Lucius Iwejuru Ugorji da Shugaban Majalisar Bishop-bishop ɗin Katolika na Najeriya kuma Babban Bishop na cocin katolika na Sokoto, Archbishop Matthew Hassan Kukah da kuma Archbishop na Abuja, Archbishop Ignatius Ayua ...
Za a sake zaɓar Tinubu a 2027 – Gwamnan Edo

Za a sake zaɓar Tinubu a 2027 – Gwamnan Edo

Duk Labarai
Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa za a sake zaɓar Shugaba Tinubu a 2027, musamman yanzu da jam'iyar APC ke ƙara samun yawan jihohi a ƙasar. Yayin da yake maraba da takwaransa gwamnan jihar Delta Sheriff Oborevwori, wanda ya koma jam'iyyar APC mai mulki cikin makonnan, Mista Okpebholo ya ce kasancewar a yanzu APC na iko da jihohi uku cikin shida na yankin kudu maso kudancin ƙasar yankin zai samu kulawar gwamnatin tarayya. Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Fred Itua ya fitar, gwamnan ya ce yana da ƙwarin gwiwar cewa nan ba da jimawa ba gwamnonin jihohin Bayelsa da Rivers da kuma Akwa Ibom za su koma APC, wani abu da ya ce zai ƙara wa yankin tasiri a siyasance. Gwamnan ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa jam'iyyar APC za ta lashe yankin k...