Sunday, December 21
Shadow

Duk Labarai

Kalli Hotuna: Mun cinye zaben shekarar 2027 mun gama>>Inji Ganduje Bayan da ya karbi ‘yan NNPP da suka koma APC

Kalli Hotuna: Mun cinye zaben shekarar 2027 mun gama>>Inji Ganduje Bayan da ya karbi ‘yan NNPP da suka koma APC

Duk Labarai
Shugaban jam'iyyar APC na Kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje ya karbi jiga-jigan jam'iyyar NNPP wadanda su ka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC. Mashawarci na musamman ga Dr. Ganduje, Aminu Dahiru ne ya wallafa hotunan yadda tarbar ta kasance. Ganduje bayan karbar sabbin 'yan APC din ya bayyana cewa sun lashe zaben shekarar 2027 sun gama. Ya bayyana cewa akwai karin Gwamnoni da manyan 'yan siyasa da zasu shiga jam'iyyar tasu. Daga cikin wadanda Abdullahi Umar Ganduje ya karba sun hada da Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila da dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Rano/Kibiya/Bunkure, Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum da tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano Dr. Baffa Bichi da tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Danbatta...
Bankin Duniya ya nada Dangote babban Mukami

Bankin Duniya ya nada Dangote babban Mukami

Duk Labarai
Babban Bankin Duniya (World Bank) ya nada Aliko Dangote tare da wasu manyan ‘yan kasuwa da masana daga sassa daban-daban na duniya zuwa mukamai na musamman a wani sabon kwamiti da aka kafa domin karfafa ci gaban tattalin arziki da rage talauci. An bayyana cewa wannan nadin na nuna yadda Bankin Duniya ke daraja ƙoƙarin da Dangote ke yi wajen bunkasa masana’antu da kuma tallafa wa ci gaban al’umma musamman a nahiyar Afirka. Baya ga Dangote, akwai wasu fitattun mutane da suka haɗa da shugabannin kamfanoni, masana tattalin arziki, da wakilan ƙungiyoyin kasa da kasa da za su yi aiki tare da bankin domin samar da hanyoyin warware matsalolin da ke hana ci gaba a duniya. Wannan ci gaba na daga cikin shirin Bankin Duniya na samar da tsayayyen tsarin ci gaba mai dorewa da kuma jawo hankalin...
Hoto: ‘Yan Bìndìgà sun kàshè Ango sun gudu da Amaryarsa

Hoto: ‘Yan Bìndìgà sun kàshè Ango sun gudu da Amaryarsa

Duk Labarai
' Yan Bindiga a garin Akaleku village dake karamar hukumar Obi ta jihar Nasarawa sun kashe wani Ango inda suka yi garkuwa da Amaryarsa. Harin ya saka fargaba a tsakanin mutane sosai. Maharan sun kai harinne ranar Laraba da misalin karfe 11 na dare. Sun kashe Angon me suna Alu Anzaku wanda aka daurawa aure ranar 12 ga watan Afrilu. Zuwa yanzu dai babu wata magana daga bakin jami'an tsaro game da lamarin.
Abin da ya sa na ajiye aiki a fadar shugaban ƙasa – Bayani dalla-dalla daga bakin Dr Baba-Ahmed

Abin da ya sa na ajiye aiki a fadar shugaban ƙasa – Bayani dalla-dalla daga bakin Dr Baba-Ahmed

Duk Labarai
Tsohon mai bai wa shugaban Najeriya Bola Tinubu shawara kan harkokin siyasa Dr Hakeem Baba-Ahmed ya shawarci shugaban ƙasar ya haƙura da neman takarar wa'adin Mulki na biyu a 2027. Dr Baba-Ahmed wanda ya yi wa shugaba Tinubu aiki a ofishin mataimakin shugaban ƙasa ya ce ya kamata yayi dattawan da ke riƙe da muƙaman siyasa a yanzu su fahimce cewa lokaci ya yi da za su janye jiki domin bai wa masu jini a jiki damar jan ragama. Ya shaida wa BBC cewa tsawon lokacin da ya shafe a matsayin mai bayar da shawara ga gwamnatin shugaba Tinubu, ya ga kurakurai da dama da suka bayyana ƙarara cewa gwamnatin ba ta ɗauki hanyar gyara ɓarnar da ta tarar ba. Kuma wannan na cikin dalilansa na ajiye miƙamin sa na bayar da shawara. Kwanaki kaɗan bayan ya fito ya tabbatar wa duniya cewa ya ajiye miƙami...
Allah Sarki: Idan baku ganni ba kawai a dora daga inda na tsaya, inada makiya da yawa>>Saurari Hirar da aka yi da Ahmad Isa(Ordinary President)

Allah Sarki: Idan baku ganni ba kawai a dora daga inda na tsaya, inada makiya da yawa>>Saurari Hirar da aka yi da Ahmad Isa(Ordinary President)

Duk Labarai
Shugaban gidan Rediyon Berekete Family Ahmad Isa wanda aka fi sani da Ordinary President ya fito yayi magana bayan dadewa da aka yi ba'a ji duriyarsa ba. Mutane da yawa sun damu da rashin ji daga gareshi i da aka rika yada labaran cewa bashi da lafiyane. Saidai a wata hira da aka yi dashi wadda ta rika yawo, an jishi yana cewa, idan ba'a ganshi ba a ci gaba daga inda ya tsaya. Saurari hirar a nan https://www.tiktok.com/@yarbaba68/photo/7496424141969427729?_d=secCgYIASAHKAESPgo8rHIAL2YVd0%2B5JzFbG%2BKNkWRQVo%2BiAoJJQNPdStnG0r%2B1Fkd9aSsX63PcmniZLjfIz1zw%2FO9ges2x%2B9WLGgA%3D&_r=1&_svg=1&aweme_type=150&checksum=c4b529189383f2bd9f7b9976cd0c2badbf021874b96303fbbec873cca56e8895&cover_exp=v1&link_reflow_popup_iteration_sharer=%7B%22click_empty_to_play%22%3A1%...
INEC Na Duba Yiwuwar Bai Wa ’Yan Najeriya Damar Kada Kuri’a Ba Tare da Katin Zabe (PVC) Ba

INEC Na Duba Yiwuwar Bai Wa ’Yan Najeriya Damar Kada Kuri’a Ba Tare da Katin Zabe (PVC) Ba

Duk Labarai
INEC Na Duba Yiwuwar Bai Wa ’Yan Najeriya Damar Kada Kuri’a Ba Tare da Katin Zabe (PVC) Ba. Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC) tana nazarin sabon tsari da zai bai wa ’yan ƙasa damar kada kuri’a ba tare da katin zabe na dindindin (PVC) ba a babban zaɓen 2027. A cewar hukumar, sabon tsarin zai dogara ne da amfani da fasahar zamani kamar BVAS (Bimodal Voter Accreditation System) da kuma takardun tantancewa da za a iya saukewa daga shafin INEC. Wannan zai rage wahalhalu, rage kashe kuɗi, da hana saye da satar katin zabe. Sai dai, kafin wannan tsari ya fara aiki, ana buƙatar gyara dokar zabe wanda ya shafi Majalisar Dokoki domin samun doka da izinin amfani da tsarin. Wannan mataki na INEC na nuni da kokarinta wajen saukaka tsarin zabe da kara amfani da fasaha don tabbatar da gaskiya da...
Nan da shekarar 2027 za’a samu karin Talakawa a Najeriya>>Inji Bankin Duniya

Nan da shekarar 2027 za’a samu karin Talakawa a Najeriya>>Inji Bankin Duniya

Duk Labarai
Bankin Duniya ya bayyana cewa talauci a Najeriya zai karu da kaso 3.6 a cikin 100 nan da shekaru 5 masu zuwa. Bankin Yace hakan zai farune duk da ci gaban da aka samu ta fannin tattakin Arziki. Bayan Najeriya akwai kuma kasashe irin su DR. Congo da suma ake tsammanin zasu fada cikin wannan matsanancin hali. Lamarin dai na zuwane a daidai lokacin da matsalar tsaro ke kara ta'azzara a tsakanin jihohin Arewa.
Ji yanda wani mutum kan zargin kàshè matar ƙaninsa a Jigawa

Ji yanda wani mutum kan zargin kàshè matar ƙaninsa a Jigawa

Duk Labarai
Rundunar ƴansanda a jihar Jigawa sun ce sun kama wani mutum bisa zargin kashe matar ƙaninsa a ƙauyen Gunka da ke karamar hukumar Jahun a jihar. Wata sanarwa da kakakin ƴansandan jihar SP Lawan Shiisu Adam ya fitar ranar Alhamis, ya ce ana zargin mutumin mai suna Buhari Sule mai shekara 25 da far wa matar ƙanin nasa - inda ya lakaɗa mata shegen duka har ta kai ga mutuwarta. Sai dai ya ce ana tunanin cewa ba shi da lafiyar kwakwalwa, saboda baya ga kashe matar, ya kuma raunata ɗiyar makwabciyarsa ta hanyar yi mata duka da taɓarya. Sanarwar ƴansandan ta ce lamarin ya faru ne ne ranar Laraba, 23 ga watan Afrilu da misalin karfe 5:30 na yamma a ƙauyen na Gunka. "Bayan da muka je wurin da lamarin ya faru ne muka garzaya da waɗanda lamarin ya rutsa da su zuwa babban asibitin Jahun dom...
Sojojin Najeriya sun dakile yunkurin kai hàrì tare da kàshè ɗan bindiga a Filato

Sojojin Najeriya sun dakile yunkurin kai hàrì tare da kàshè ɗan bindiga a Filato

Duk Labarai
Rundunar sojin Najeriya ta Operation Safe Heaven ta ce ta daƙile wani yunkurin kai hari a ƙauyen Teegbe da ke karamar hukumar Bassa na jihar Filato, tare da kashe ɗaya daga cikin maharan. Sanarwar da mai magana da yawun rundunar Manjo Samson Nantip Zhakom ya fitar ranar Alhamis, ya ce lamarin ya faru ne ranar Laraba 23 ga watan Afrilu, inda artabun da sojojin suka yi da maharan ne ya janyo wasu suka tsere. "Wani mazaunin yankin ne ya kira mu ya faɗa mana abin da ke faruwa, daga nan dakarun mu suka garzaya wurin. Sun fafata da ƴan bindigar har ta kai ga kashe ɗaya daga cikinsu, tare da kama wasu mutum biyu waɗanda ake ci gaba da bincike a kansu," in ji Manjo Samson. Ya ƙara da cewa dakarun sun kuma samu nasarar kama wasu ƴan fashi uku a wani samame da suka kai hanyar Katnan- Burata...