Sunday, December 21
Shadow

Duk Labarai

An bayyana abu daya da ya ragewa Atiku da Peter Obi su yi idan suna son kayar da Tinubu a zaben 2027

An bayyana abu daya da ya ragewa Atiku da Peter Obi su yi idan suna son kayar da Tinubu a zaben 2027

Duk Labarai
A yayin da komawar Kwankwaso jam'iyyar APC ke kara tabbata. Sannan mataimakin Atiku a zaben 2023, Ifeanyi Okowa shima ya koma APC. Sannan ake rade-radin shima mataimakin Peter Obi a zaben 2023, Datti Baba Ahmad wai zai koma APC, an bayyana abu daya da ya ragewa Peter Obi da Atiku Abubakar su yi shine su hade waje guda. Masu sharhi sun ce idan ba hadewa suka yi a waje guda ba, ba zasu iya kayar da shugaban kasa Bola Tinubu said a zaben 2027 ba.
Sharudan Komawar Kwankwaso shine, za’a bashi mataimakin shugaban kasa, Amma Kuma Gandujene zai kawo wanda za’a baiwa Gwamnan Kano

Sharudan Komawar Kwankwaso shine, za’a bashi mataimakin shugaban kasa, Amma Kuma Gandujene zai kawo wanda za’a baiwa Gwamnan Kano

Duk Labarai
Wasu rahotanni daga majiyoyi daban-daban dake ta yawo shine Tsohon Gwamnan Kano Dr. Rabiu Musa Kwankwaso zai koma APC. Saidai maganar tana ta jan kafa. A wata majiya, munji cewa sharudan da ake neman gindayawa ne yasa maganar ke jan kafa inda ake ci gaba da tattaunawa me zafi. Daya daga cikin sharudan shine za'a baiwa tsohon gwamnan Kanon mukamin mataimakin shugaban kasa a 2027. Saidai idan hakan ta faru, shi Kuma Ganduje shine zai kawo wanda zai zama Gwamnan Kano a 2027. Yayin da shi kuma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf bayan kammala wa'adin mulkinsa na farko, za'a bashi mukamin zama cikin kwamitin gudanarwa na jami'ar Yusuf Maitama Sule. Saidai duka wadannan bayanai ba'a hukumance aka sakesu ba, wata majiya ce ta bayyanasu.
An kori malamin jami’ar ATBU Bauchi Dr. Usman Mohammed Aliyu saboda zargin aikawa dalibarsa matar aure sakonnin batsa sannan yace idan bata yadda yayi lalata da ita ba zai kayar da ita jarabawa

An kori malamin jami’ar ATBU Bauchi Dr. Usman Mohammed Aliyu saboda zargin aikawa dalibarsa matar aure sakonnin batsa sannan yace idan bata yadda yayi lalata da ita ba zai kayar da ita jarabawa

Duk Labarai
Jami'ar ATBU dake Bauchi ta sallami daya daga cikin malamanta me suna Dr. Usman Mohammed Aliyu bisa zargin neman yin lalata da dalibarsa wadda matar aurece. Dalibar me suna Kamila Rufa’i Aliyu ta zargi malamin da cewa ya aika mata sakonnin batsa sannan ya nemi yayi lalata da ita. Data kiya, sai ya ce zai kayar da ita jarabawa duk da cewa yasan ita matar aurece. Saidai Dr. Usman ya shigar da kara kotu inda yake neman hakkinsa saboda a cewarsa, Kamila ta bata masa suna. Mijin Kamila, Ja’afaru Buba ta hannun lauyansa ya shigar da karan makarantar inda ya bayar da dukkan hujjojin da yake dasu na cewa Dr. Usman ya nemi yin lalata da matarsa. Bayan kammala bincike, Hukumar gudanarwar jami'ar ta ce ta samu Dr. Usman da laifi inda tace ta sallameshi daga aiki. Sannan ya mika duk ...
TURKASHI: Wasu Matasa Sun Taso Daga Jihar Katsina Zuwa Abuja A Kafa Domin Su Yi Ido Hudu Da Matar Kashim Shettima, Ministar Jinkai, Shugaban ‘Yan Sanda Na Kasa Da Kuma Ibrahim Kabiru Masari

TURKASHI: Wasu Matasa Sun Taso Daga Jihar Katsina Zuwa Abuja A Kafa Domin Su Yi Ido Hudu Da Matar Kashim Shettima, Ministar Jinkai, Shugaban ‘Yan Sanda Na Kasa Da Kuma Ibrahim Kabiru Masari

Duk Labarai
Sun shirya wannan tafiya ce domin yabon gwani ya zama dole. Domin a cewar su kowa ya san yadda Alhaji lbrahim Kabir Masari yake kokari sosai da kuma jarincewa wajen alki da nuna kishin yankinshi. Dan haka a matsayinmu na Katsinawa za mu zo mu gaida shi kuma muna son ganin shi idon da ido. Kuma a matsayinshi na ubanmu shi zai kai mu wajen shugaban 'yan sanda na kasa bisa kokari da hukumar 'yan sanda ke yi domin dada tsaro ga a'lummar kasa bakin daya. Wanda bisa haka ne muka yanke shawara gani IGP na kasa don mu yaba masa. Daga Shi ma IG ya kai mu wajen tsuhuwar Ministar 'yan sanda bisa namiji kokari da ta yi wajen nuna kishi da kuma taimako da ta yi wa kasa, musamman fanninmu Katsina ta bada waje domin tallafawa matan 'yan sanda da suka rasu. Da kuma taya ta murnar samu wani matsayi n...
DA ƊUMI-ƊUMINSA: Zanga-zanga Ta Barke A Birnin Tarayyar Abuja

DA ƊUMI-ƊUMINSA: Zanga-zanga Ta Barke A Birnin Tarayyar Abuja

Duk Labarai
Gungun Malaman Firamare da sauran ma'aikatan ƙananan hukumomin Abuja sun gudanar da zanga-zangar lumana a kan tituna, kan rashin biyan su mafi ƙarancin albashi, da sauran haƙƙoƙin da suke bin shugabannin ƙananan hukumomi 6 da ke Abuja. Sun gudanar da zanga-zangar ne a yau Alhamis a ƙarƙashin ƙungiyar malaman makaranta ta NUT, da kuma ƙungiyar ma'aikatan ƙananan hukumomi ta NULGE.
Ƴansanda biyu sun jikkata yayin artabu da ƴandaba a Kano

Ƴansanda biyu sun jikkata yayin artabu da ƴandaba a Kano

Duk Labarai
Ƴansanda biyu sun jikkata yayin artabu da ƴandaba a Kano. Ƴansanda biyu, Abdullahi Ibrahim da Yahaya Saidu, sun samu raunuka yayin wani kazamin fada da wasu gungun 'yan fashi da makami a jihar Kano. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kano, SP Abdullahi Kiyawa, ya fitar wa manema labarai a Kano a jiya Laraba. “Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta amsa kiran gaggawa a ranar 22 ga Afrilu, 2025, da misalin karfe 1 na rana dangane da wani gungun ‘yandaba da ake zargi Halifa Baba-Beru daga unguwar Gwammaja, karamar hukumar Dala, ya na jagoranta. “An rawaito cewa gungun yandaban na dauke da muggan makamai kuma su ka rika kai hari kan al'umma a unguwar Gwammaja, Dala LGA, Kano. “Lokacin da ‘yansanda suka isa wurin, sai yan...
Gwamnatin Tinubu zara dawo da shirin ciyar da dalibai na tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Gwamnatin Tinubu zara dawo da shirin ciyar da dalibai na tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Duk Labarai
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da cewa za ta sake ɗaddamar da shirin ciyar da ɗalibai a makarantu, ranar 29 ga watan Mayu. Ƙaramin Ministan ma'aikatar jin-ƙai da rage talauci, Dr Yusuf Sununu ne ya bayyana hakan a ranar Larabar da ta gabata yayin wata ganawa da ƙungiyoyi masu zaman kansu da kuma jami’an gwamnati a Abuja. Sununu ya sanar da cewa za a sake kaddamar da shirin ne domin murnar cikar shugaba Bola Tinubu shekara ta biyu akan karagar mulki. Ya ce shirin na da nufin magance yunwa da kuma inganta ɓangaren ilimi a faɗin ƙasar baki ɗaya. ''Shirin na nufin amfanar yara miliyan 10 kuma zai iya ƙara yawan yaran da ke shiga makarantu da kashi 20 cikin 100 sannan kuma ya bunƙasa hazaƙar yara a ɓangaren karatu da kashi 15 cikin 100 ,” in ji shi. Sake ƙaddamar da shirin ...
Dalla-Dalla: Ji Yanda Kawu sumaila ya fadi dalilan da suka sa ya koma APC

Dalla-Dalla: Ji Yanda Kawu sumaila ya fadi dalilan da suka sa ya koma APC

Duk Labarai
Bayan jan ƙafa na tsawon lokaci, ɗaya daga cikin ƴan majalisar dattawa na jam'iyyar NNPP Sanata Abdurahman Kawu Sumaila ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC. Matakin na zuwa ne bayan shafe watanni ana takun saƙa tsakanin Sanatan da jam'iyyarsa ta NNPP a jihar Kano. A makon da ya gabata ne Sanata Kawu Sumaila ya jagoranci wata tawagar yanmajalisar tarayya na NNPP inda suka gana da shugaban jam'iyyar APC mai mulki kuma tsohon gwamnan jihar Kano. A hirar da ya yi da BBC, Sanatan ya bayyana dalilansa na ficewa daga jam'iyyar NNPP, inda ya tabbatar da cewa ya ɗauki matakin ne domin samar da ci gaba ga al'ummar mazaɓarsa. Ya ce ''Wasu daga cikin dalilan da za su sa mu fice shi ne yankin da muka fito. Ya za mu iya samar wa mutanen yankin mu wani abu da zai amfanar da su, kuma ai ita siya...