Sunday, December 21
Shadow

Duk Labarai

Na gama da Atiku, Har mataimakinsa Okowa ya dawo APC>>Inji shugaba Tinubu

Na gama da Atiku, Har mataimakinsa Okowa ya dawo APC>>Inji shugaba Tinubu

Duk Labarai
Kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya bayyana cewa ya gama da babban dan Adawa, Atiku Abubakar saboda har wanda yayi masa mataimaki a zaben shekarar 2023, Ifeanyi Okowa ya koma jam'iyyar su ta APC. Ya bayyana cewa ko gamayyar da suke hadawa a yanzu ta watse. Inda ya karkare da cewa, Ya sake yin nasara akan Atiku Abubakar. A jiyane dai Ifeanyi Okowa ya koma jam'iyyar APC daga PDP
A kama Fasto da ya dirkawa yarinya me shekaru 13 ciki, ya amsa laifinsa

A kama Fasto da ya dirkawa yarinya me shekaru 13 ciki, ya amsa laifinsa

Duk Labarai
A jihar Ondo Hukumomi na binciken wani fasto me suna Peter James saboda zargin dirkawa yarinya me shekaru 13 ciki. Yarinyar dai na daya daga cikin mas wake-wake a cocinsa. Lamarin ya farune a garin Oke-Gburowo, dake karamar hukumar Odigbo, ta jihar. Da farko dai jami'an Amotekun ne suka kama faston inda aka kaishi fadar sarkin garin kuma bayan gabatar masa da zargin da ake masa, ya amsa laifinsa Saidai daga baya ya murzawa idanunsa kwalli yace cikin ba nashi bane. Mahaifiyar yarinyar me suna Mrs. Victoria Bernard tace faston ya ki amsa laifinsa ne saboda yaga yarinyar na da nakasa. Ta yi kira ga hukumomi da su amsar musu 'yancinsu.
Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su gaggauta magance matsalar tsaro a Nijeriya

Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su gaggauta magance matsalar tsaro a Nijeriya

Duk Labarai
Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su gaggauta magance matsalar tsaro a Nijeriya. Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya umarci hukumomin tsaron ƙasar su gaggauta kawo ƙarshen matsalar tsaro da take ƙara ƙamari a jihohin Borno da Plateau da Benue da kuma Kwara. Wannan na zuwa ne bayan shugaba Tinubu ya gana da shugabannin tsaron ƙasar a fadarsa da ke Abuja, inda suka yi nazari a kan yanayin tsaro a Najeriya. A wata sanarwa da ɗaya daga cikin masu magana da yawun shugaban Najeriyan, Bayo Onanuga ya fitar, shugaba Tinubu ya bayyana damuwa kan kisan ƴan Najeriya da basu ji ba, ba su gani ba a sassan ƙasar. Shugaban ƙasan wanda ya shafe fiye da sa'oi biyu yana ganawa da shugabannin hukumomin tsaron Najeriya, ya ce dole ne su kawo ƙarshen kisan mutane a ƙasar. Sanawar ta ayyano shugab...
Kalli Bidiyo Yadda Sallah ta kama su Sheikh Ahmed Guruntum da Farfesa Isa Yelwa a cikin jirgin sama, a hanyarsu ta gabatar da Da’awa kuma suka yi sallar yayin da suke zaune a kujerar jirgin

Kalli Bidiyo Yadda Sallah ta kama su Sheikh Ahmed Guruntum da Farfesa Isa Yelwa a cikin jirgin sama, a hanyarsu ta gabatar da Da’awa kuma suka yi sallar yayin da suke zaune a kujerar jirgin

Duk Labarai
Yadda Sallah ta kama su Sheikh Ahmed Guruntum da Farfesa Isa Yelwa a cikin jirgin sama, a hanyarsu ta gabatar da Da'awa kuma suka yi sallar yayin da suke zaune a kujerar jirgin. https://www.tiktok.com/@mbabanislam/video/7496294294630731041?_t=ZM-8vmgnwzOzDD&_r=1 A kwanannan ne dai aka ga malaman sun je Da'awa kasashen Turai inda wani Bidiyo ya nunasu a kasar Faransa.
Kalli Bidiyo: An zargi dan Bello da kin biyan matasa hakkokinsu bayan sun masa aiki

Kalli Bidiyo: An zargi dan Bello da kin biyan matasa hakkokinsu bayan sun masa aiki

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wani Bidiyo ya bayyana inda ake zargin shahararren me watsa labarai ta kafafen sadarwa Dan Bello da kin biyan wasu matasa hakkokinsu bayan sun masa aiki. Dan Bello kamar yanda aka ji a bidiyon yayi amfani da matasanne wajan kaiwa kwastomominsa kayayyakin da suka saya a hannunsa. Saidai bayan da suka kammala masa aiki suka ji shiru, sai suka tuntubeshi, amma sai yace ai kyauta suka masa. Daga baya dai ya tambayesu nawane kudin aikinsu i da suka gaya mai dubu dari biyar a...
Ba su El-Rufai bane ya kamata ace suna yakin nemawa talakawa hakkokinsu ba, saboda mayunwatane da an basu abinda suke so zasu koma gidan jiya>>Sowore

Ba su El-Rufai bane ya kamata ace suna yakin nemawa talakawa hakkokinsu ba, saboda mayunwatane da an basu abinda suke so zasu koma gidan jiya>>Sowore

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Dan takarar shugaban kasa kuma mawallafin Jaridar Sahara reporters Omoyele Sowore ya bayyana cewa su El-Rufai basu ne ya kamata ace suna nemawa talaka hakkinsa ba. Sowore yace saboda mayunwatane ana basu abinda suke so zasu koma inda suka fito. Yace Su El-Rufai kamata yayi ace suna daure a gidan yari saboda da su aka yi duk abinda aka yi a gwamnatin Buhari.
Shugaba Tinubu yayi Allah wadai da Kàshè-Kàshèn da suka faru a Najeriya bayan ganawa da shuwagabannin tsaro

Shugaba Tinubu yayi Allah wadai da Kàshè-Kàshèn da suka faru a Najeriya bayan ganawa da shuwagabannin tsaro

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi Allah wadai da kashe-kashen da suka faru a Najeriya musamman a jihohin Benue, Filato da Borno. Shugaban yace a yiwa tsarin tsaron kasar garambawul inda yace abin ya isa haka. Babban me baiwa shugaban kasar shawara akan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu ne ya bayyana hakan i da yace yayin ganawar, shuwagabannin tsaron sun baiwa shugaba Tinubu bayanai kan yanda lamarin tsaron ya kasance. Yace shugaba Tinubu ya kuma bayar da umarnin a canja salo game da yanda ake yaki da matsalar tsaron.
Kalli Bidiyon Sadiya Haruna tana fadar cewa zata sha Jini saidai ta fito tace wasa ne take

Kalli Bidiyon Sadiya Haruna tana fadar cewa zata sha Jini saidai ta fito tace wasa ne take

Duk Labarai
Tauraruwar kafafen sada zumunta, Sadiya Haruna ta dauki hankula sosai bayan da aka ji muryarta tana gayawa mijinta maganar shan Jini. Saidai daga baya ta fito ta karyata lamarin inda tace wasa ne take. https://www.tiktok.com/@zainabsadam8/video/7496178214386142519?_t=ZM-8vmdlmiIqjH&_r=1 https://www.tiktok.com/@sayyada_sadiya_haruna/video/7496181775794720005?_t=ZM-8vmdi00aBi3&_r=1 Tace tsokanar mijintane take. Sannan tace kishiyartace ta fitar da maganar ta dora a kafafen sada zumunta inda ta yi fatan Cewa, Allah ya rabamu da sharrin Kishiya.
Legas da Kanone kan Gaba wajan yawan masu rijistar NIN

Legas da Kanone kan Gaba wajan yawan masu rijistar NIN

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa jihohin Legas da Kano ne kan gaba wajan yawan masu rijistar katin zama dan kasa NIN. Yawan wanda suka yi rijistar a Najeriya sun kai Miliyan 118.4. Legas ce kan gaba wajan yawan masu rijistar inda take da mutane miliyan 12.7 da suka yi rijistar. Sai kuma jihar Kano ta zo ta biyu inda take da mutane miliyan 10.4 kamar yanda hukumar kididdigar kasa ta NBS ta bayyana. Kaduna ce ta zo ta 3 da mutane miliyan 6.9 da suka yi rijista. Sauran jihohin na da mutanen da suka yi rijista kamar haka: Ogun mutane 4.9 million Oyo Mutane 4.5 million Katsina Mutane 4 million FCT Mutane 3.8 million Rivers 3.5 million Delta 3.2 million Jigawa 3.1 million. Imo 2 million Kwara 2 million Enugu 1.9 million Kogi 1.9 million Yobe 1.8 mill...