Tsohon hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya bayyana cewa jam'iyyar su ta APC a Kano na shirin karbar Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf da Kwankwaso.
An dai jima ana maganar cewa, Kwankwaso zai koma APC.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour party, Peter Obi ya je Rome dan halartar binne gawar marigayi Fararoma Francis.
Nan da ranar Asabar ne dai ake tsammanin binne gawar Fafaroman.
"
Jita-jitar da ake yi kan komawa ta APC gaskiya ne. Ni dama siyasata ta mutane ce. Kare muradun al'ummar da nake wakilta shi na sa a gaba…," Kawu Sumaila.
Gwamna Bago ya janye matakin da ya ɗauka akan samari masu tara gashin dada a Neja.
Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya janye umarninsa na baya da ya bayar ga jami’an tsaro da su kama masu gashin dada da maza masu Kitso a Minna, babban birnin jihar.
Bago, yayin da yake magana a wani taron tsaro tare da masu ruwa da tsaki a gidan gwamnati ranar Talata, ya umarci jami’an tsaro da su yanke gashin dada na mutanen da aka kama tare da cin tarar kudi.
Ya ce: “Duk wanda kuka gani da Gashin Dada, ku kama shi, ku yanke masa gashi, sannan ku ci shi tara.
“Babu wanda zai rika yawo da irin wannan gashi a cikin Minna. Na riga na ba da umarni ga jami’an tsaro,” in ji gwamnan.
Sai dai a ranar Laraba, gwamnan ya janye wannan umarni bayan ya fuskanci suka daga 'yan Najeriya da dama.
Yayin...
Dr. Ifeanyi Okowa, mataimakin Atiku a takarar shugabancin ƙasa a zaben 2023 ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Okowa ya koma APC din ne tare da Sheriff Oborevwori, gwamnan jihar Delta Kuma magajin sa.
Hakazalika gaba ɗaya shugabancin PDP na jihar ta Delta ya narke cikin APC, kamar yadda sanarwa ta gabata a yau Laraba.
Da Dumi-Dumi : Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya fice daga PDP zuwa APC
Gwamnan Jihar Delta, Rt. Hon. Sheriff Oborevwori, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyar APC.
Sanarwar ta fito ne bayan wani taro na manyan gwamnati da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Asaba, babban birnin jihar a yau Laraba.
Wata sabuwar masifa da ta shigo kafafen sada zumuntar Arewa itace ta amfani da wani AI ana saka hotunan malamai ana sawa su yi rawa.
Wannan AI a baya 'yan siyasa kawai akewa amfani dashi amma yanzu lamarin ya kai har kan malamai.
https://www.tiktok.com/@sanusi_lauwali/video/7494342086968462647?_t=ZM-8vmO2enRDGw&_r=1
Wasu daga cikin Malam da muka ci karo an yi Amfani da wannan AI din an sa sun yi rawa sun hada da Marigayi Shaikh Jafar Adam, da Sheikh Bala Lau da Sheikh Maqari.
https://www.tiktok.com/@sanusi_lauwali/video/7495429012479659319?_t=ZM-8vmO9SppUg9&_r=1
Wani abin takaici ma shine lamarin ya koma gasa tsakanin matasa mabiya akidu, idan wannan ta saka malamin wannan akida rawa, sai shima wancan ya rama.
https://www.tiktok.com/@sanusi_lauwali/video/7494...
Dan Gwamnan Jihar Neja, Marwan Bago Ya Zama Babban Matukin Jirgin Sama Na Kamfanin Jirage Na 'Overland Airways', Inda Har Ya Yi Sawu Daya Zuwa Abuja.
Wace fata za ku yi masa?
Aƙalla mutane 151 ne suka samu raunuka bayan sun durgo daga dogayen gine-gine saboda tsoron da girgizar ƙasa ta haifar, a cewar ofishin gwamnan Istanbul.
https://www.tiktok.com/@live_news00/video/7496509730362281238?_t=ZM-8vmJNkmOYiL&_r=1
Ofishin ya kuma wallafa a shafinsa na X, cewa ba a samu asarar rayuka ba, kuma babu wani gini da mutane ke zaune a ciki da ya ruguje.
Sai dai wani gini wanda babu kowa a ciki ya ruguje sakamakon girgizar ƙasar.
https://twitter.com/The_NewArab/status/1915025667365683236?t=7ep6E-k1HezvWfbB4qwjPQ&s=19
Ministan ilimi na Turkiyya, Yusuf Tekin ya sanar da cewa za a rufe makarantu na kwana biyu Alhamis da Juma'a.
Aƙalla an samu girgiza sau 51 a birnin a ranar Laraba, inda mafi girmansu ya kai ƙarfin maki 6.2, wanda ya shafi Istambul...