Wata Sabuwa:Ji yanda na kusa da Buhari ke nuna basu tare da Tinubu
A wani lamari mai kama da na ba-zata a fagen siyasar Najeriya, sunan tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ne ya sake dawowa yake amo, musamman bayan alamu sun fara nuna akwai ɓaraka a tsakanin makusantansa.
Alamu sun fara bayyana ne a lokacin da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar SDP, inda ya ce da amincewar tsohon shugaban ƙasar ya sauya sheƙar ta siyasa.
Sai dai daga baya Buhari ya fito ta bakin kakakinsa, Garba Shehu, cewa shi ɗan APC ne, kuma yana alfahari da kasancewarsa ɗan jam'iyyar, inda ya ce yana godiya ga magoya bayan APC, sannan zai yi duk mai yiwuwa domin samun nasararta.
Sai dai daga lokacin aka samu wata goguwar siyasa ta tashi a ƙasar, inda aka fara maganar jiga-jigan ƴansiyasar ƙasar za su koma ...








