Friday, May 15
Shadow

Duk Labarai

Kalli Bidiyo Da Duminsa: Gawar Marigayi Dantata ta Isa Madina da safiyar yau

Kalli Bidiyo Da Duminsa: Gawar Marigayi Dantata ta Isa Madina da safiyar yau

Duk Labarai
Rahotanni daga Madina birnin Ma'aiki na cewa, gawar marigayi Aminu Dantata ta isa birnin. Bayan Saukar Gawar Marigayi Alh Aminu Dantata Tareda da Iyalensa; Alh Tajudeen Dantata da Hassan Dantata da Yaya, Jikoki da Yan Uwa Da Abokan Arziki duk Suna Wannan Guri Domin Mika Marigayi zuwa ga Ma'aikatan Kula Da Makabartar Baki'ah Inda akesa Rai Zasuyi masa Suttura. Allah yajikan sa Da Rahma. https://twitter.com/GASHASHCOLLECT2/status/1939964376754057576?t=i0_KkOxpnECK4Dy5VN-ZiQ&s=19 Me magana da yawunsa yace zasu jira hukumomin Madina au basu lokacin da za'a masa sallah.
Kalli Bidiyo Da Duminsa: An Sàcè kanin Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare>>Inji Mahdi Shehu

Kalli Bidiyo Da Duminsa: An Sàcè kanin Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare>>Inji Mahdi Shehu

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Dan siyasa, Mahdi Shehu yace an sace kanin Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare. Ya bayyana hakane a shafinsa na X inda ya wallafa Bidiyon wani mutum da aka gani zagaye da 'yan Bindiga rike da muggan makamai yana fadar cewa uwarsu daya ubansu daya da Gwamnan jihar Zamfara. Mahdi dai yayi tambayar cewa shin ko Gwamnan zai biya kudin fansa. Ko kuwa zai yi sulhu da 'yan Bindigar? Kalli Bidiyon anan Babu dai wata sanarwa data tabbatar da cewa wannan mutumin dan uwa...
Matatar man Dangote ta kara rage farashin man fetur dinta

Matatar man Dangote ta kara rage farashin man fetur dinta

Duk Labarai
Matatar man fetur din Dangote ta rage farashin man fetur dnta inda a yanzu take sayar dashi akan Naira 840 maimakon 880 da yake a baya. Hakan na wakiltar ragin kaso 4.5. Bincike ya bayyana cewa Dangote ya rage farashin nasa ne bayan da farashin danyen man fetur ya fadi a kasuwar Duniya zuwa dala $67.50 daga Dala sama da $70 da yake a baya. Wasu sauran kamfanonin ma sun rage farashin man fetur din nasu kamar yanda Dangote yayi.
Shin wai ina Kwankwaso? Ana ta cece-kuce bayan da manyan mutanen Kano suka je jana’izar Aminu Dantata Madina amma ba’a ga Kwankwaso ba

Shin wai ina Kwankwaso? Ana ta cece-kuce bayan da manyan mutanen Kano suka je jana’izar Aminu Dantata Madina amma ba’a ga Kwankwaso ba

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"square_fit":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false} Yayin da manyan mutanen jihar Kano suka hallara a Madina wajan jana'izar Marigayi Aminu Dantata, ana ta daga wuya dan ko za'a hango Kwankwaso amma ba'a ganshi ba. Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya jagoranci tawagar Gwamnan Jigawa da Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero zuwa jana'izar. Da yawa sun yi tsammanin za'a ga Kwankwaso a cikin tawagar amma ba'a ganshi ba. Hakan yasa ake ta cece-kuce akai. Wasu dai na ganin zuwan Abba Gida-Gida ya isa ya wakilci Kwankwa...
Ji Bayani Dalla-Dalla: Shin waye zaiwa gawar marigayi Dantata Sallah a Madina?

Ji Bayani Dalla-Dalla: Shin waye zaiwa gawar marigayi Dantata Sallah a Madina?

Duk Labarai
A yayin da manyan mutane musaman daga jihar Kano suka hallara a Madina dan halartar jana'izar marigayi Aminu Dogo, Dantata. Ana tababar wanene zai yiwa marigayin sallar gawa? Wasu rahotanni sun ce marigayin ya bar wasiyyar tsohon sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya mai sallar gawa wanda tuni shima yana can Madina. Saidai Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II duk suma suna can Madinan. Zuwa anjima zami samu bayani kan yanda ta kaya.
Kalli Bidiyon: Shima tsohon shugaban APC, Ganduje ya tafi Madina dan halartar jana’izar Dantata

Kalli Bidiyon: Shima tsohon shugaban APC, Ganduje ya tafi Madina dan halartar jana’izar Dantata

Duk Labarai
Rahotanni daga Madina na cewa, Tsohon shugaban jam'iyyar APC da tawagarsa sun isa birnin dan halartar jana'izar Marigayi Aminu Dantata. A cikin tawagar Ganduje akwai sanata Barau Jibrin da sauransu. Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan saukar Ganduje daga shugabancin jam'iyyar APC. https://twitter.com/tudunwada__mi/status/1939767084486951292?t=xz6XVz4xauDslIATf5EErw&s=19 Sauran wanda suka tafi Madina sun hada da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, Gwamnan jihawa, Umar Namadi, da sauransu. Akwai kuma tawagar shugaban kasa wadda ministan tsaro, Abubakar Badaru ya jagoranta. Tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero shima ya tafi Madinan.
APC ta saka Naira Miliyan 20 a matsayin kudin fom din takarar Sanata sannan Naira Miliyan 10 a matsayin kufin Fom din takarar dan majalisar wakilai

APC ta saka Naira Miliyan 20 a matsayin kudin fom din takarar Sanata sannan Naira Miliyan 10 a matsayin kufin Fom din takarar dan majalisar wakilai

Duk Labarai
Jam'iyyar APC ta saka Naira Miliyan 20 a matsayin kudin sayen fom din takarar sanata sannan ta sa Naira Miliyan 10 a matsayin kudin fom din takarar dan majalisar wakilai a zabukan cike gurbi da ake shirin yi. Hakan na kunshene a cikin takardar bayanan ya da za'a gudanar da zaben da jam'iyyar ta fitar ta hannun babban sakatarenta, Sulaiman Argungu. Fom din tsayawa takarar dan majalisar jiha kuwa an sakashi akan Naira Miliyan 2. Matasa dake tsakanin shekaru 25 zuwa 40 zasu samu ragin kaso 50 cikin 100 na kudin sayen fom din. Jam'iyyar tace tana sayar da fom din a ofishinta dake Wuse II, Abuja
An saka ranar da shugaba Tinubu zai mayar da gwamban Rivers, Simi Fubara kan kujerarsa ta Gwamna

An saka ranar da shugaba Tinubu zai mayar da gwamban Rivers, Simi Fubara kan kujerarsa ta Gwamna

Duk Labarai
Rahotanni na cewa, a watan Yuli ne shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai mayar da gwamnan Rivers, Simi Fubara kan mukaminsa. Hakanan itama majalisar jihar a wannan watanne ke tsammanin mayar da ita kan aiki. Hakan na zuwane bayan da aka yi sasanci tsakanin Fubara da Wike. A ranar 18 ga watan Maris ne dai shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara da 'yan majalisar jihar inda ya bayyana cewa sun samu bayanan sirri musamman game da fasa bututun man fetur a jihar kuma Gwamnan ya kasa magance matsalar.
Kasar Saint Lucia ta girmama shugaba Tinubu

Kasar Saint Lucia ta girmama shugaba Tinubu

Duk Labarai
Kasar Saint Lucia ta girmama shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da lambar girmamawa mafi girma a kasar. Hakan ya farune yayin da shugaba Tinubu ke ziyarar aiki a kasar kuma an karramashi ne dan kokarinsa wajan kyautata zumunta tsakanin kasashen biyu. Ba kasafai kasar Saint Lucia ke baiwa kowa wannan kyautar karramawar ba wanda hakan ke nuna muhimmancin da shugaba Tinubu ke dashi a wajansu.
Matatar man fetur ta Fatakwal ta dawo aiki

Matatar man fetur ta Fatakwal ta dawo aiki

Duk Labarai
An barke da murna a Eleme dake Birnin Fatakwal na jihar Rivers bayan ganin wutar matatar man fetur dake garin na ci balbal. Lamarin ya farune ranar Lahadi, 29 ga watan Mayu na shekarar 2025, wasu rahotanni na cewa, ana gwajin matatar man fetur dinne. 'Yan kasuwar man fetur dake kusa da matatar sun ce alamace matatar man fetur din na daf da dawowa da aiki dan ana kwacin ta ne. Rahotanni sun ce fiye da dala Biliyan 1 ne gwamnatin tarayya ta kashe Akan gyaran matatar man fetur din tun daga shekarar 2021 zuwa yanzu.