Tuesday, December 16
Shadow

Duk Labarai

Gwamnonin APC sun kai wa Muhammadu Buhari ziyara

Gwamnonin APC sun kai wa Muhammadu Buhari ziyara

Duk Labarai
Kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya karkashin jagorancin shugabanta gwamnan Imo Sanata Hope Uzodinma, ta kai wa tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ziyarar ban girma a gidansa da ke Kaduna. Bayan shugaban kungiyar, sauran gwamnonin da suke cikin tawagar ma su ziyarar sun hada da gwamnan Kaduna da na Gombe da Kwara da Nasarawa da Ebonyi da Kebbi da Edo da Kogi da Ondo da Ekiti da kuma Benue. Sauran 'yan tawagar sun hadar da mataimakin gwamnan Jigawa da ministan kasafin kudi da tsare-tsare.
Najeriya da Saudiyya sun ƙulla yarjejeniyar yaƙi da miyagun ƙwàyòyì

Najeriya da Saudiyya sun ƙulla yarjejeniyar yaƙi da miyagun ƙwàyòyì

Duk Labarai
Najeriya da Saudi Arabiyya sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimta domin karfafa yaki da hada-hadar kwayoyi. A ranar Litinin Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta Najeriya da kuma Hukumar da ke yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Saudiyya GDNC, suka sanya hannu kan yarjejeniyar a Riyadh. Cikin wata sanarwar da daraktan yada labarai na hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar ya ce kasashen biyu sun amince su kara karfafa yaki da fataucin miyagun kwayoyi a dukkan iyakokinsu. Da ya ke magana a wajen sanya hannu kan yarjejeniyar, shugaban hukumar ta NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa, mai ritaya, ya ce dukkan kasashen sun jima suna yin hadaka da bangarori daban daban. Marwa, wanda ya samu rakiyar darakta a sashen bincike da gudanarwa na hukumar, Ahmed Ning...
Mun san ana cutar mu, ba sai wani dan iska Munafiki Dan Bello ya fito ya gaya mana ba>>Inji Sheikh Adam Muhammad Albaniy Gombe

Mun san ana cutar mu, ba sai wani dan iska Munafiki Dan Bello ya fito ya gaya mana ba>>Inji Sheikh Adam Muhammad Albaniy Gombe

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Babban malamin Addinin Islama, Sheik Adam Muhammad Albany Gombe ya soki Dan Bello kan labarin zargin daya wallafa na cewa, an baiwa shugaban kungiyar Izala, Sheik Bala Lau kudin gina Azuzuwan makarantu daga Gwamnatin tarayya amma bai gina ba. Malam ya bayyana Dan Bello a matsayin wanda yake can kasar waje yake gayawa mutane cewa wai ana cutarsu inda yace 'yan Najeriya sun san ana cutarsu ba sai wani Dan Bello ya fito yana gaya musu ba. Hakanan ya gargadi Dan Bello da cewa zasu ma...
Nijar ta ayyana Hausa a matsayin harshen da za’a rika amfani dashi a ƙasar

Nijar ta ayyana Hausa a matsayin harshen da za’a rika amfani dashi a ƙasar

Duk Labarai
A Jamhuriyar Nijar gwamnatin kasar ta bayyana Hausa a matsayin harshen da za a rinka amfani da shi a kasar yayin da sauran harsuna ta ayyanasu a matsayin na magana. Kazalika an kuma bayyana harshen Ingilishi da Faransanci a matsayin harsunan aiki. To sai dai kuma ba dukkanin 'yan kasar ne ke maraba da wannan mataki ba. An kiyasta cewa akwai mutum miliyan 18 da ke jin harshen hausa a Jamhuriyar Nijar, abin da ake ganin wannan ne ya sanya gwamnatin kasar ta ayyana shi a matsayin harshen da za a rinka amfani da shi a kasar. To sai dai kuma ba dukkanin 'yan kasar ne wannan mataki ya yi wa dadi ba, inda wasu ke cewa ya kamata a yi nazari sosai a kai. Harshen Hausa shi ne ke matsayin na uku a Afirka inda kasashe da dama a Afirka a ke samun masu jin harshen. Akwai dai masu jin h...
Trump ya yi barazanar kara wa China harajin kashi 100

Trump ya yi barazanar kara wa China harajin kashi 100

Duk Labarai
Shugaba Donald Trump, na Amurka, ya yi barazanar zafafa yaƙin kasuwanci da ke tsakaninsu da China, ta hanyar kakaba karin harajin kashi 50 cikin 100 na kayayyakinsu, muddin Beijing ba ta jingine shirinta na mayar da martani ba. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Mista Trump, ya ce zai kawo karshen duk wata yarjejeniya da ke tsakaninsu, muddin China ba ta yi biyayya ba. Wannan harajin da Trump ke shirin sanya wa China zai haura kashi 100 cikin 100. A mako mai zuwa ne haraje-harajen da China ta sanya ita ma kan kayayyakin Amurka za su soma aiki.
Tun farko gayyatar da shelkwatar ƴansanda ta yi wa Sarki Sanusi ba ta da amfani – Peter Obi

Tun farko gayyatar da shelkwatar ƴansanda ta yi wa Sarki Sanusi ba ta da amfani – Peter Obi

Duk Labarai
Peter Obi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP), ya yaba wa Rundunar ‘Yansandan Najeriya bisa janye gayyatar da ta aikewa Muhammadu Sanusi, Sarkin Kano. A makon da ya gabata ne, ‘yansanda suka gayyaci Sanusi zuwa hedikwatar rundunar domin yi masa tambayoyi kan zargin kashe-kashe da suka faru a lokacin bikin Eid-el-Fitr da ya gabata. Da yake mayar da martani a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, Obi ya ce hanyar warware matsalar a matakin ƙasa-ƙasa (wato ba tare da tursasawa daga sama ba) zai ƙara kawo zaman lafiya da amincewar jama’a. Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce ba bu buƙatar wannan gayyata tun da farko, kuma hakan na iya tayar da hankali a lamarin da tuni ya ɗauki zafi. “Ina so in yaba wa Rundunar ‘Yansandan Najeriya sab...
Hotuna: Wani mai tallar Goro ya shiga damuwa jim kaɗan bayan ya gama liƙawa Alan Waka kudin cinikinsa a bikin Sallar aka aka gabatar a fadar sarkin Kano dake Nasarawa

Hotuna: Wani mai tallar Goro ya shiga damuwa jim kaɗan bayan ya gama liƙawa Alan Waka kudin cinikinsa a bikin Sallar aka aka gabatar a fadar sarkin Kano dake Nasarawa

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wani mai tallar Goro ya shiga damuwa jim kaɗan bayan ya gama liƙawa Alan Waka kudin cinikinsa a bikin Sallar aka aka gabatar a fadar sarkin Kano dake Nasarawa Menene ra'ayoyin ku?
‘Yansanda sun Tarwatsa masu zanga-zangar adawa da tsare-tsaren gwamnatin Tinubu da ‘yan Jarida suka banka musu barkonon tsohuwa a jihar Rivers da Abuja

‘Yansanda sun Tarwatsa masu zanga-zangar adawa da tsare-tsaren gwamnatin Tinubu da ‘yan Jarida suka banka musu barkonon tsohuwa a jihar Rivers da Abuja

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa 'yansanda a Jihar Rivers sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da tsare-tsaren gwamnatin Tinubu da suka fito a yau, Litinin. Rahoton yace da misalin karfe 9 na safe ne matasan masu zanga-zangar suka fito inda suka ci karo da dandazon 'yansanda a filin Isaac Boro Park dake birnin na Fatakwal. 'Yansandan aun gayawa matasan cewa ba zasu barsu su yi zanga-zangar ba amma matasan sun ce sai sun yi. 'Yansandan sun harbawa matasan barkonon tsohuwa sannan suka bisu da duka ciki hadda 'yan jarida da suka je daukar lamarin. Hakanan a babban birnin tarayya, Abuja ma, 'yansandan sun bankawa matasa masu zanga-zangar barkonon tsohuwa da suka fito yin zanga-zangar a maitama. Wannan rana ta Zanga-zangar dai ta zo daidai da ranar 'yansanda ta Najeriya. Dan haka n...
‘Yansanda sun kama wanda suka fito zanga-zangar adawa da tsare-tsaren gwamnatin Tinubu a jihar Yobe

‘Yansanda sun kama wanda suka fito zanga-zangar adawa da tsare-tsaren gwamnatin Tinubu a jihar Yobe

Duk Labarai
A jihar Yobe dake Arewacin Najeriya, 'yansanda sun kama shugaban kungiyar da suka fito zanga-zanga inda suke adawa da sabuwar dokar saka ido akan kafafen sada zumunta da ake son zartaswa. Wanda aka kama din shine Abubakar Jawa wanda shine ya jagoranci masu zanga-zangar na jihar Yobe. Bayan shi, akwai kuma mutane 4 da aka kama tare dashi wanda aka bayyana sunayensu kamar haka, Mohammed Kayeri Adam, Suleiman A. Gambo, Maimuna Abba, and Abubakar Jawa.  Da aka Tuntubi kakakin 'yansandan jihar, Dungus Abdulkarim ya musanta kamen inda yace su suna ma neman masu zanga-zangar ne dan basu kariya.
Matasa sun fito zanga-zangar adawa da tsare-tsaren gwamnatin Tinubu duk da gargadin ‘yansanda

Matasa sun fito zanga-zangar adawa da tsare-tsaren gwamnatin Tinubu duk da gargadin ‘yansanda

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Legas sun bayyana cewa, matasa a jihar Legas din sun fito zanga-zangar adawa da wasu tsare-tsaren gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Haka lamarin yake ma a jihar Rivers, matasa sun fito inda suka hau kan tituna suna nuna rashin amincewarsu da tsare-tsaren gwamnatin musamman dakatar da gwamnan jihar Rivers da kuma dokar sanya ido akan kafafen sada zumunta. 'Yansandan dai sun yiwa matasan rakiya tare da basu Kariya musamman a Legas, a baya dai hukumar ta 'yansanda ta hana matasan fitowa zanga-zangar inda suka ce ba'a sakawa zanga-zangar lokacin da ya dace ba. Hakanan a jihar Oyo, da babban birnin tarayya, Abuja ma, masu zanga-zangar sun fito sun nuna damuwarsu.