Rundunar ƴansandan Abuja ta musanta garƙame hedikwatar PDP
Newly deployed Nigerian Formed Police Unit (FPU) personnel under the African Union Mission in Somalia (AMISOM) arrive at Aden Abdulleh International Airport, Mogadishu, Somalia on January 6, 2016. AMISOM Photo / Ilyas Ahmed
Rundunar ƴansandan Abuja ta musanta rahotannin da ke cewa jami'anta sun karɓe iko da hedikwatar jam'iyyar PDP ta Wadata Plaza a ranar Litinin.
Rundunar ta ce tana son "ta nuna cewa babu gaskiya a rahotonnin sannan ba haka al'amarin yake ba. An kai jami'an ƴansandan ne zuwa wurin taron domin wanzar da doka da oda kamar yadda tsarin mulki ya tanada.
A wata sanarwa, rundunar ta ce "babu wani lokaci da jami'an ƴansanda suka kulle sakateriyar jam'iyyar ta PDP."
A sanarwar, kwamishinan ƴan sanda na Abujar ya buƙaci kafafen watsa labarai da su yi kaffa-kaffa wajen ...








