Sunday, April 26
Shadow

Duk Labarai

Matan Jihar Bayelsa sun bayyana takaici da watsi da Shugaba Tinubu yayi dasu bayan da suka masa yakin neman zabe

Matan Jihar Bayelsa sun bayyana takaici da watsi da Shugaba Tinubu yayi dasu bayan da suka masa yakin neman zabe

Duk Labarai
Mata magoya bayan Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu sun bayyana takaici da jin Haushin watsi da aka yi dasu bayan da sukawa shugaban kasar yakin neman zabe. Matan sun nemi a sakasu cikin bayar da mukamin da shugaban kasar yake yi. Matan wadanda suka fito daga jihar Bayelsa sun bayyana hakane ta bakin wakiliyarsu a Abuja ranar Litinin. Tace a cikinsu akwai kwararrun mata da zasu taimaka wajan cimma muradun gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu idan aka basu dama. Ta bayyana takaicin yanda aka rasa mata a mukaman siyasa a Gwamnatin Tinubu duk da rawar da suka taka wajan yakin neman zabensa.
Kalli Bidiyo: Yanda shugaban kasar Amurka, Donald Trump yayi Tuntube ya kusa faduwa a yayin da yake hawa jirgin sama

Kalli Bidiyo: Yanda shugaban kasar Amurka, Donald Trump yayi Tuntube ya kusa faduwa a yayin da yake hawa jirgin sama

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi Tuntube inda ya kusa faduwa yayin da yake hawa matakalar jigin saman sa na Airforce One. Irin wannan lamari ya taba faruwa da tsohon shugaban kasar, Joe Biden inda akai ta masa tsiya da cewa tsufa ne ya masa yawa. https://twitter.com/LeadingReport/status/1931816469962035526?t=s7R7IHw5jPP7_Jz_id6weQ&s=19 Yanzu dai 'yan jam'iyyar Republicans dole bakinsu zai kulle saboda sune dama ke sukar Biden saboda hakan.
Tsohon Shugaban Sojoji, Janar Buratai yayi magana game da rahoton kai masa hàrì

Tsohon Shugaban Sojoji, Janar Buratai yayi magana game da rahoton kai masa hàrì

Duk Labarai
Tsohon shugaban sojojin Najeriya, Janar Yusuf Tukur Burataiya musanta rahoton dake cewa an kai masa hari ya sha da kyar. A baya dai an ruwaito Sanata Ali Ndume yana cewa An kaiwa Buratai hari, saidai daga baya yace yana nufin garin Buratai ne ba tsohon shugaban sojojin ba. Buratai a sanarwar da ya fitar yace a Abuja yayi bikin Sallah tare da iyalinsa da 'yan uwa da abokan arziki. Yace maganar an kai masa hari bata da tushe ballantana makama inda yace ayi watsi da labarin. Yace yana godiya ga wadanda suka kirashi dan jin halin da yake ciki bayan samun wannan labari.
Game da hatsarin da Jarumi Adam A. Zango ya yi, bayanai na nuna an samu wasu marasa Imani sun sace masa wayar sa da kuɗin sa har da ɗan cincin ɗin da mahaifiyar sa tayi masa guzuri da shi da sauran abubuwan amfani

Game da hatsarin da Jarumi Adam A. Zango ya yi, bayanai na nuna an samu wasu marasa Imani sun sace masa wayar sa da kuɗin sa har da ɗan cincin ɗin da mahaifiyar sa tayi masa guzuri da shi da sauran abubuwan amfani

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Game da hatsarin da Jarumi Adam A. Zango ya yi, bayanai na nuna an samu wasu marasa Imani sun sace masa wayar sa da kuɗin sa har da ɗan cincin ɗin da mahaifiyar sa tayi masa guzuri da shi da sauran abubuwan amfani. A wani labarin kuma an bayyana Ali nuhu ya taka rawar gani wajen ɗaukar nauyin kula da lafiyar sa.
Ba wanda yake da hujja kan mijina (Abacha) ya saci kuɗin Najeriya, kuma bai soke zaɓen Abiola ba – in ji Maryam Abacha

Ba wanda yake da hujja kan mijina (Abacha) ya saci kuɗin Najeriya, kuma bai soke zaɓen Abiola ba – in ji Maryam Abacha

Duk Labarai
Uwargidan marigayi tsohon shugaban Najeriya, Maryam Abacha, ta musanta zargin da ake yi wa mijinta, tsohon shugaban ƙasa na mulkin soji, Janar Sani Abacha, kan zargin satar kuɗin Najeriya. Abacha ya yi mulkin Najeriya ne daga shekarar 1993 zuwa 1998 kuma ya rasu ne a ranar 8 ga Yunin 1998. DailyTrust ta rawaito a cikin wata hira da gidan talabijin ɗin TVC ya yi ta yi a ranar Lahadi kan cikar Abacha shekaru 27 da rasuwa, uwargidan marigayin ta ce kuɗin da ake zargin mijinta ya sata, ba satar su ya yi ba, kawai ana yi masa mummunar fassara ce. A cikin waɗannan shekarun baya-bayan nan, gwamnatoci daban-daban sun sanar da gano miliyoyin kuɗin dalar Amurka a asusan ƙasashen waje waɗanda ake wa laƙabi da “Abacha loot.” Waɗannan kuɗaɗe, an dawo da su daga ƙasashen Switzerland da Amurk...
Gwamnatin Jihar Neja Ta Bada Tallafin Naira Bilyan Daya Ga Wadanda iftila’in Ruwa Ya Shafa A Garin Mokwa

Gwamnatin Jihar Neja Ta Bada Tallafin Naira Bilyan Daya Ga Wadanda iftila’in Ruwa Ya Shafa A Garin Mokwa

Duk Labarai
Gwamnatin Jihar Neja Ta Bada Tallafin Naira Bilyan Daya Ga Wadanda iftila’in Ruwa Ya Shafa A Garin Mokwa. A yau ne Gwamna Bago ya bayyana haka a daidai lokacin da ya ziyarci garin, inda ya bukaci mazauna yankunan dake kusa da kogin da su kaura, sannan ya ba su filaye su gina da tallafin kudin da ya ba su. Daga Rashida Bala Suleja
Ka Daina Boye-Boye Ka Fito Fili Ka Koma Jam’iyyar APC, Matawalle Ga Gwamnan Zamfara

Ka Daina Boye-Boye Ka Fito Fili Ka Koma Jam’iyyar APC, Matawalle Ga Gwamnan Zamfara

Duk Labarai
Ministan kasa a ma'aikatar tsaron Nijeriya, kuma tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Dr. Bello Mohammed Matawalle, ya bukaci Gwamna mai ci, Dr. Dauda Lawal, da ya fito fili ya bayyana cewa ya shiga jam’iyyar APC ya daina wani boye-boye. Da yake jawabi a gidansa da ke Maradun yayin wata ziyarar gaisuwar Sallah da dubban magoya baya suka kai masa, Matawalle ya ce lokaci ya yi da Gwamna Lawal zai daina “kumbiya-kumbiya" yana rufa-rufa” ya fito fili ya bayyana matsayarsa a jam'iyyance. “Kofar jam’iyyarmu a bude take ga duk wanda ke neman ci gaban gaskiya ga jihar Zamfara da Nijeriya,” inji Matawalle, yana mai jaddada cewa bai dauki komai a ransa ba dangane da zabin siyasar Gwamna Lawal. Ya ce APC jam’iyya ce da ke kan turbar tawali’u, gaskiya da shugabanci nagari. “Muna kira gare shi ya ...
‘Idan ba a yashe Alo Dam ba za mu iya fuskantar matsala a Borno’

‘Idan ba a yashe Alo Dam ba za mu iya fuskantar matsala a Borno’

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Borno ta yi kira ga gwamnatin shugaba Tinubu ta hanzarta daukar mataki kan ɗan kwangilar da ta baiwa aikin yashe dam din Alou da ya haifar da ambaliya a bara. Ta ce duk da cewar sun yashe wani sashe na dam din amma, har yanzu akwai babbar barazana da za a iya fuskantar mumunar ambaliya. Kwamishinan yaɗ labarai da harkokin tsaro na jihar Borno, Farfesa Umar Tar da harkkokin tsaro ya shaida wa BBC cewa an bayar da kwantaragin kuma minista ya je ya ƙaddamar da aikin. "Har yanzu ba mu ga ƴan kwangila sun zo domin fara aikin ba kuma yanzu ga damuna ta riga ta sauka. Idan ba a yi aikin nan da wuri ba to idan ruwa ya zo ya yi halinsa to lallai za a samu matsala. Ya kamata ace an yashe ruwan saboda irin cunkushewar da ya yi. Idan aka yashe shi to ko ruwa ya zo da yawa ba z...
Ƴansanda sun kama mutum 27, sun ƙwàtò màggàn màkàmài a Kaduna

Ƴansanda sun kama mutum 27, sun ƙwàtò màggàn màkàmài a Kaduna

Duk Labarai
Ƴansanda a jihar Kaduna sun ce sun kama mutum 27 waɗanda ake zargi da aikata laifuka daba-daban. Wata sanarwar da mai magana da yawun ƴansandan jihar DSP Mansir Hassan ya fitar, ta ce an samu nasarar kama ɓata-garin ne bayan wani samame da ta kai maɓoyarsu a yankin Kawo. "Mun kai samamen ne jiya Lahadi a lungu da sako na yankin Kawo. Abin ya kai ga kama mutum 27 da ake zargi da aikata laifuka har ma da ƙwato muggan makamai," in ji Mansir. Ya ce cikin makaman da suka ƙwato sun haɗa da wuƙaƙe da adduna da fartanyu da kuma ƙunshin ganyayyaki da ake kyautata zaton tabar wiwi ce da kuma sauran kayan maye. Kwamishinan ƴansandan jihar, CP Rabiu Muhammad ya ƙara nanata ƙoƙarin rundunar wajen ganin an mutunta doka da oda a faɗin jihar. Ya ƙara da cewa Kaduna jiha ce mai zaman lafiya,...
Kaf masu neman takarar shugabancin Najeriya babu Gwani wanda ya cancanta kamar ni>>Inji Peter Obi

Kaf masu neman takarar shugabancin Najeriya babu Gwani wanda ya cancanta kamar ni>>Inji Peter Obi

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar Labour party a zaben shekarar 2027, Peter Obi ya bayyana cewa, babu Dimokradiyya a mulkin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Ya bayyana cewa idan aka lura da abinda ya faru a jihar Rivers da zaben jihar Edo za'a iya gane cewa, babu Dimokradiyya a Najeriya. Peter Obi ya bayyana hakane a wata ganawa da aka yi dashi a Arise TV. Yace shiyasa yake ta neman ya zama shugaban kasa, saboda ya gyara wannan matsalar, yace a kaf cikin masu neman takarar shugaban kasar, babu gwani wanda ke da kwarewa kamarsa saboda yayi aiki da kamfanoni kuma ya zama gwamna.