Ban yi kuskure ba wajen zaɓen Kashim a matsayin mataimaki – Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yaba da jajircewar mataimakinsa, Kashim Shettima, wanda ya bayyana da mutum mai amana da gaskiya da yake jin daɗin aiki da shi.
A wata sanarwa da ya fitar kan taya mataimakin nasa murnar cika 59 a duniya, Tinubu ya ce, "tun da na sanka har zuwa yanzu, ba ka nuna gajiyawa wajen aiki tuƙuru domin sake gina ƙasarmu. A dukkan muƙaman da ka riƙe a baya, ka nuna jajircewa wajen aiwatar da abubuwan da suka dace duk runtsi duk wahala."
Tinubu ya ce yana godiya bisa irin goyon bayan da yake samu daga Shettima, "lokacin da na zaɓe ka a matsayin mataimakina, na san ban yi zaɓen tumun-dare ba, na san na ɗauko nagartacce wanda Najeriya za ta yi alfahari da shi. Kullum a aikinka na mataimaki, kana ƙoƙari wajen kawo shawarwari da tsara sababbin abubuwa da za su taim...








