Matawalle ya yi wa Dauda Lawal tayin shiga APC
Karamin ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle ya yi wa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal tayin shiga jam'iyyar APC mai mulki.
Ministan ya yi tayin ne ranar Asabar a garin mahaifarsa ta Maradun, lokacin da ya karɓi bakuncin dubban magoya bayansa da suka kai masa gaisuwar barka da sallah.
Matawalle wanda ya kasance tsohon gwamnan Zamfara, ya ce APC jam'iyya ce ta mutanen kirki da dattako, don haka ya shawarci Dauda Lawal ya shiga jam'iyyar.
Ministan ya ce maimakon gwamnan ya bi ta ɓarauniya hanya, gara ya fito fili ya bi hanyar da ta dace wajen shiga APC.
"Ba ni da matsala da gwamnan idan yana son shiga APC. Ya zo ya bi sahun masu yunkurin kawo ci gaba a ɓangaren tsaro da zaman lafiya da kuma ayyukan raya ƙasa," in ji Matawalle.
Ya kuma ce shugaba Bola Tinubu jagora ne na...








