Ya kamata Najeriya ta gina katanga a kan iyakokinta>>Inji Shugaban Sojojin Najeriya, Christopher Musa
Babban hafsan sojin Najeriya, Janar Christopher Musa ya nuna buƙatar gina katanga a ilahirin iyakokin ƙasar da maƙwaftanta domin kare kwararar masu ɗauke da makami zuwa cikinta.
Yanzu haka dakarun sojin Najeriya na fafutikar ganin sun yaƙi matsalar tsaro da ke addabar ƙasar, musamman rikicin Boko Haram da ƙasar ta kwashe shekara 16 tana fama da shi a arewa maso gabas.
Mayaƙan ƙungiyar - wadda ta samo asali daga kungiyar IS reshen yammacin Afirka - sun kashe jami'an tsaro da dubban fararen hula, yayin da rikicin ya tagayyara miliyoyi.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato Janar Christopher Musa a wani taron tsaro da ke gudana a Abuja yau Talata a Abuja na cewa "kula da kan iyakoki abu ne mai muhimmanci," inda ya bayar da misali da iyakar ƙasar Pakistan mai katangar da ke ...








