Gwamna Abiodun ya baiwa iyalan ƴan wasan Kano da su ka rasu a hatsarin mota Naira Miliyan 31
Gwamna Abiodun ya baiwa iyalan ƴan wasan Kano da su ka rasu a hatsarin mota Naira Miliyan 31.
Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, a ranar Lahadi ya aike da tawaga zuwa Jihar Kano domin yi wa gwamnatin jihar da al’ummar Kano ta’aziyya bisa rashin wasu 'yan wasa da jami'ai da suka rasu yayin dawowa daga gasar wasanni ta kasa da aka kammala kwanan nan.
Gwamna Abiodun ya kuma ba da gudummawar Naira miliyan daya (N1m) ga kowanne iyali daga cikin iyalan mamatan a matsayin taimako na farko, wanda jimillar kudin ta kai Naira miliyan 31.
A cewar wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, mataimakiyar gwamna, Injiniya Noimot Salako-Oyedele ce ta jagoranci tawagar, da ta haɗa da Sakataren Gwamnatin Jihar Ogun, Mista Tokunbo Talabi; Kwamishinan Ci gaban Wasanni, Hon. Wasiu Isiaka; da Sakatar...







