Shekara daya bayan da Gwamnatin Tinubu tace an gyarasu ‘Har yanzu matatun man fetur na Fatakwal da Wari basu fara fitar da man fetur ba’
Masu hada-hadar man fetur a Najeriya na kokawa kan yadda suke samun matsala wajen samun fetur daga matatun gwamnati guda biyu da aka gyara kwanan nan—matatar Fatakwal da na Warri—shekara daya bayan da aka bayyana cewa sun fara aiki.
Najeriya, wadda ta shafe shekaru tana fama da ƙarancin man fetur, ta kashe kimanin dala biliyan 2.4 tun daga shekara 2021 domin farfaɗo da waɗannan matatun da ke yankin Niger Delta, da nufin dakatar da dogaro da shigo da man fetur daga ƙasashen waje. Sai dai har yanzu, ba su fara fitar da man fetur ba.
Kungiyar 'yan kasuwa masu gidajen mai ta Najeriya, PETROAN, ta bayyana wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa sama da mambobinta 6,700 har yanzu na dogaro da shigo da mai daga waje da kuma matatar Dangote.
Bisa bayanan ƙungiyar, har zuwa watan Maris ...








