Monday, February 23
Shadow

Duk Labarai

Kuma Dai:Kalli Bidiyon, Bayan Sanata Akpabio da Reno Omokri, Sanata Natasha tace akwai wani minista shima da ya nemeta da làlàtà

Kuma Dai:Kalli Bidiyon, Bayan Sanata Akpabio da Reno Omokri, Sanata Natasha tace akwai wani minista shima da ya nemeta da làlàtà

Duk Labarai
A yayin da ake tsaka da zargin da Sanata Natasha Akpoti kewa kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio na cewa yana son lalata da ita, An gano cewa ta tabata zargin tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri da irin wannan zargi. Saidai duk ba'a gama da wannan ba, har ila yau, Wani bidiyon Sanata Natasha Akpoti ya bayyana inda aka jita tana kuma zargin wani minista da neman yin lalata da ita. https://www.youtube.com/watch?v=olzYFAEd6EM?si=y29YEntQW7Mmle9V Saidai a wannan karin bata fadi sunan Ministan ba. Kalli Bidiyon anan
Bamu yadda ba zamu je kotu, Kungiyar Kiristoci kan hutun Ramadan da jihohin Arewa suka bayar a makarantu

Bamu yadda ba zamu je kotu, Kungiyar Kiristoci kan hutun Ramadan da jihohin Arewa suka bayar a makarantu

Duk Labarai
Kungiyar Kiristocin Najeriya ta ce bata yadda ba kuma ta yi Allah wadai da kulle makarantu da jihohin Bauchi, Katsina, Kano, da Kebbi suka yi saboda zuwan Ramadana. A sanarwar da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh ya bayyana cewa wannan mataki zai kawo koma baya ga ci gaban ilimi da hadin kai a Najeriya. Kungiyar tace kulle makarantun zai taba harkar ilimi wadda 'yanci ne na dan adam kuma sannan ginshiki ne na ci gaban al'umma kuma hakan zai kara tabbatar da koma baya ga harkar ilimi a jihohin. Yace ba'a tuntubesu dan neman shawara kamin daukar wannan mataki ba kasancewa akwai kiristoci a wadanan jihohin. Yace kuma wani abin mamaki shine kasashen da musulmai suka fi yawa irin su UAE, da Saudi Arabia da sauransu duk basu kulle makarantu ba saida...
”Yan Bìndìgà sun kashe daliba Maryam da suka sace a jami’ar jihar Zamfara duk da karbar kudin Fansa

”Yan Bìndìgà sun kashe daliba Maryam da suka sace a jami’ar jihar Zamfara duk da karbar kudin Fansa

Duk Labarai
'Yan Bindiga da suka yi garkuwa da daliba a jami'ar jihar Zamfara, Zarah Abubakar Shehu sun kasheta duk da karbar kudin fansa. An sace tane tare da 'yan uwanta biyu a ranar Nov. 3, 2024 inda suka nemi Naira Miliyan 35 a matsayin kudin fansa, saidai daga baya an koma Miliyan 10 bayan tattaunawa. Saidai bayan da aka kai kudin fansar sun rike Zarah inda suka ce sai an sake kai musu mashina 4 da Engine oil. Saidai bayan da aka kai musu, sunce Zahra ta rasu har sun binneta.
An kama matashi me suna Haruna yawa yarinya me shekaru 3 fyàdè a ranar 1 ga Ramadana

An kama matashi me suna Haruna yawa yarinya me shekaru 3 fyàdè a ranar 1 ga Ramadana

Duk Labarai
' Yansanda a jihar Ogun sun kama wani matashi me suna Muniru Haruna dan kimanin shekaru 25 bisa zargin yiwa yarinya me shekaru 3 fyade a ranar 1 ga watan Ramadana. Lamarin ya farune a Orile-Ilugun dake karamar hukumar Odeda ta jihar Ogun. Kakakin 'yansandan jihar, CSP Omolola Odutola ya tabbatar da faruwar lamarin. Yace mahaifiyar yarinyar, Alaba Abdullahi me shekaru 20 ce da kanta ta kai karar wanda ake zargi da misalin karfe 11 na safiyar ranar Asabar, 1 ga watan Maris wadda ta yi daidai ga 1 ga watan Ramadana. Tace suna zaune a gida daya da matashin inda tace yarinyar na wasane kamin matashin ya zakke mata, tace ta ji kukan diyarta inda ta fito bata iya tafiya kuma tana cikin firgici. Hakan yasa ta kira dauki inda aka kama wanda ake zargin, an garzaya da yarinyar z...
Hisba ta kama matasan da ba sa yin azumi da masu askin banza a Kano

Hisba ta kama matasan da ba sa yin azumi da masu askin banza a Kano

Duk Labarai
Jami’an Hukumar Hisba a jihar Kano sun kama wasu matasa gandaye da ake zargi da kin yin azumi a ranar farko ta watan Ramadan. Mataimakin babban kwamandan hukumar, Dakta Mujahideen Abubakar ne ya tabbatar da kamen ga manema labarai a jihar. Ya kara da cewa an kama matasan ne yayin sintiri da jami’an hukumar ke yi a sassa daban-daban na birnin Kano. Haka kuma, hukumar ta cafke kimanin mutane 60 da ke da askin banza, wanda ya sabawa dokokin shari’a da al’adun gari. Bugu da kari, Hisba ta kama wasu direbobin baburan adaidaita sahu (keke napep) da ake zargi da cakuda maza da mata a baburansu, lamarin da hukumar tace ba za ta lamunta da shi ba. Hukumar ta Hisba ta bayyana cewa za ta ci gaba da gudanar da sintiri don tabbatar da bin dokokin shari’a a cikin watan Ramadan.
Kalli bidiyon yanda wani yayi kashin kullin Kwàyòyì 120 da ya hadiya yana shirin fita dasu kasashen waje

Kalli bidiyon yanda wani yayi kashin kullin Kwàyòyì 120 da ya hadiya yana shirin fita dasu kasashen waje

Duk Labarai
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA ta kama wani mutum da me suna Mbala Dajou Abuba a filin sauka da tashin jiragen sama na Mallam Aminu Kano dake Kano yana shirin fita da kwayoyi zuwa kasashen waje. An kama mutumin da ya hadiyi kullun Hodar Iblis da yawa yana shirin fita da ita zuwa Istanbul babban birnin kasar Turkiyya. Mutumin dan asalin Zaire ne ta kasar Angola kuma an kamashine ranar Talata, February 25, 2025 inda yake shirin hawa jirgin sama zuwa kasar Egypt wanda daga can zai wuce zuwa kasar Turkiyya. Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ya bayyana cewa mutumin yace yana aikin kai sakonnine a kasarsa ta Angola kamin ya fada harkar safarar kwaya. alli Bidiyon anan
Ji yanda ‘yan Bìndìgà suka yi shiga irin ta EFCC suka je wani Otal suka kwashe mutanen ciki a jihar Naija

Ji yanda ‘yan Bìndìgà suka yi shiga irin ta EFCC suka je wani Otal suka kwashe mutanen ciki a jihar Naija

Duk Labarai
' Yan Bindiga masu garkuwa da mutane sun yi basaja inda suka yi shiga irin ta jami'an hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC suka shiga otal din White Hill Hotel dake Chanchaga a jihar Naija suka yi garkuwa da mutane. Lamarinnya farune ranar Talata February 27, 2025 da misalin karfe 4:58 na dare. 'Yan Bindigar sun lalata kyamarorin CCTV dake ital din kamin suka shiga daki-daki suka dauki mutane akalla 10 suka yi awon gaba dasu Hukumar 'yansandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace suna kan kokarin gano wadanda suka yi wannan aika-aika da kuma kubutar da wadanda aka sace.
Kalli Hotuna: Gagga-gaggan ƴan Bìndìgà 5 da rundunarsu a yankin Jibia sun tuba sun aje makami sun ayyana ba za su kara kai hari ba

Kalli Hotuna: Gagga-gaggan ƴan Bìndìgà 5 da rundunarsu a yankin Jibia sun tuba sun aje makami sun ayyana ba za su kara kai hari ba

Duk Labarai
Gagga-gaggan ƴan bindiga 5 da rundunarsu a yankin Jibia sun tuba sun aje makami sun ayyana ba za su kara kai hari ba Sun kuma mika bindigar AK49 har guda biyu don tabbatar da tubansu An kai ƙarshen zaman tattaunawa tareda da tubabbun yan dindiga a karamar hukumar Jibia ta jahar Katsina. A ranar Juma'a 28/2/2025, ne aka kai ƙarshen zaman tattaunawa da yan dindigar da suka shirya karɓar zaman lafiya a karamar hukumar Jibia a jihar Katsina. Anyi zaman a karkashin jagorancin Chairman na karamar hukumar Jibia da Jibiya Peoples Froum da (NCSOSACK) da rundunar sojin Nigeriya ta jihar Katsina, daga cikin tubabbun yan dindigar da a kayi zaman tattaunawar dasu akwai.1- Audu Lanƙai2- Kantoma3- Ori4- Tukur Dan Najeriya5- Bammi. A yayin zaman an tattauna batutuwa da da dama da kuma shimf...
Yan bìndigà sun sace dalibai 4 maza na Jami’ar FUDMA a jihar Katsina

Yan bìndigà sun sace dalibai 4 maza na Jami’ar FUDMA a jihar Katsina

Duk Labarai
Wasu 'yan bindi-gà masu garkuwa da mutane sun kutsa gidan ƙwanan daliban Jami'ar gwamnatin Tarayya ta FUDMA da ke garin Dutsin-ma, a jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da dalibai 4 maza zuwa daji don neman fudin fansa. Lamarin ya faru a daren ranar Lahadi 2 ga watan March 2025 a rukunin gidajen dake unguwar bayan gidan Radio kusa da mazaunin jami'ar na wucin gadi. Ya zuwa yanzu dai ba a san inda aka nufa da daliban ba. Kalli bidiyon anan MUN DAUKO RUBUTUN DAGA SHAFIN KATSINA REPORTS
Ni zan kayar da Tinubu a zaben shekarar 2027>>Inji Sowore bayan da ya shiga aka yi gudun fanfalaki dashi

Ni zan kayar da Tinubu a zaben shekarar 2027>>Inji Sowore bayan da ya shiga aka yi gudun fanfalaki dashi

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar AAC a zaben shakerar 2019 da 2023, Omoyele Sowore kuma mawallafin jaridar Sahara Reporters ya shiga gudun yada kanin wani da aka yi a Abuja. Ya bayyana cewa shine zai kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da sauran 'yan takarar shugaban kasa a zaben 2027. Yace ya kamata Gwammati ta baiwa bangaren wasannin motsa jiki muhimmanci inda yace suma zasu iya kawo kudaden shiga kamar yanda fetur ke kawowa kasarnan.