Janar Ibrahim Babangida ya amince Abiola ne ya ci zaɓen 1993 da ya rushe
A karon farko, tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya amince cewa Cif Mashood Bashorun Abiola, ɗantakarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin jam'iyyar SDP a 1993 ne ya ci zaɓen da aka soke.
Janar Babangida wanda ya bayyana hakan a cikin littafinsa da ya rubuta wanda kuma aka ƙaddamar a Abuja.
Littafin mai suna " A Journey in Service" wanda tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi bitarsa, ya ce Cif Abiola na jam'iyyar SDP ne ya samu nasara kan Alhaji Bashir Othman Tofa na jam'iyyar NRC .
"Lallai Mashood Abiola shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 1993 bayan da ya samu ƙuri'u fiye da miliyan takwas inda ya samu nasara a kan Bashir Othman Tofa na jam'iyyar NRC mai ƙuri'a fiye da miliyan biyar." In ji Janar Babangida a cikin ...








