Friday, December 5
Shadow

Duk Labarai

Hoto: An kamashi da ka-wu-nan mutane 8 dan yin tsafi

Hoto: An kamashi da ka-wu-nan mutane 8 dan yin tsafi

Duk Labarai
Jami'an 'yansanda a jihar Ondo sun kama wani matashi me suna Yusuf Adinoyi bayan samunsa da kawunan mutane 8. Kwamishinan 'yansandan jihar, Abayomi Oladipo, ya tabbatar da kamen inda yace an kama wanda ake zarginne ranar Litinin bayan an kafa shingen bincike. Mutumin na kan hanyar zuwa Akure ne kamin aka tare motarsu wadda yayi kokarin tserewa amma aka bishi aka kamoshi. Ya amsa laifinsa inda yace a baya yana sana'ar sayar da manja ne amma rashin lafiyar mahaifiyarsa tasa ya shiga harkar sayar da kawuna. Yace wannan ne karo na 3 da yake son sayar da kawunan inda a farko ya sayar da guda 4, sannan ya sayar da guda 3 hakanan sai yanzu zai sayar da guda 8. Kwamishinan 'yansandan yace za'a gurfanar dashi a kotu bayan kammala bincike.
Ya kamata EFCC ta kyale Bobrisky ta koma kan ‘yan siyasa>>Inji Peter Obi

Ya kamata EFCC ta kyale Bobrisky ta koma kan ‘yan siyasa>>Inji Peter Obi

Siyasa
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour party, Peter Obi ya bayyana cewa, ya kamata EFCC ta kyale Bobrisky da Obi Cubana ta je ta kama 'yan siyasa masu sata. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV. Yace idan da a yanzu gwamnati zata ce zata ciyar da mata kadai a Najeriya, saboda yunwar da ake ciki, maza da yawa zasu saka kayan mata su je karbar abincin. Bobrisky dai yana can daure a gidan yari saboda lika kudi a wajan biki yayin da shi kuma Obi Cubana aka gurfanar dashi ...
Atiku ya jajanta wa Tinubu dangane da “zamewar” da ya yi

Atiku ya jajanta wa Tinubu dangane da “zamewar” da ya yi

labaran tinubu ayau, Siyasa
Mutumin da shugaba Tinubun ya kayar a zaɓen 2023, Atiku Abubakar na jam'iyyar adawa ta PDP, ya ce yana jajanta wa Bola Tinubu dangane da "zamewar" da ya yi. "Ina matukar jajanta wa shugaba Bola Tinubu dangane da ɗan hatsarin da ya samu a lokaci da yake ƙoƙarin zagaya masu fareti ranar dimokaraɗiyya. Ina fatan lafiyar lau." A baya-bayan nan dai an ga yadda tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar ke ƙara ƙaimi wajen yin hamayya ta fuskar sukan abubuwan da yake ganin gwamnatin ba ta yi daidai ba.
Shettima ya buƙaci likitocin Najeriya su taimaka wajen inganta ƙasar

Shettima ya buƙaci likitocin Najeriya su taimaka wajen inganta ƙasar

Siyasa
Mataimakin shugaban ƙasar, Kashim Shettima ya yi kira ga likitocin ƙasar, su riƙa zama a ƙasar, don taimaka wa magance matsalar da ƙasar ke fuskanta ta ƙarancin likitoci. Shettima ya yi kiran ne a lokacin da ƙungiyar likitocin ƙasar - ƙarƙashin jagorancin sabon shugabanta, Farfesa Bala Audu - suka kai masa ziyara a ofishinsa ranar Talata. Mataimakin shugaban ƙasar ya nuna damuwa kan yadda likitocin ƙasar ke yawan ficewa daga ƙasar domin neman ayyuka a ƙasashen waje. A baya-bayan nan dai ana samun yawaitar ficewar likitocin Najeriya daga ƙasar, zuwa ƙasashen wajen domin samun ingantaccen albashi da yanayin aikin mai kyau. Sai dai mataimakin shugaban ƙasar, ya jaddada cewa gwamnatinsu na iya bakin ƙoƙarinsu wajen inganta yanayin aikin likitoci a ƙasar, musamman waɗanda suka zaɓi ...
Hajji 2024: Fiye da maniyyata miliyan ɗaya da rabi ne za su sauke farali

Hajji 2024: Fiye da maniyyata miliyan ɗaya da rabi ne za su sauke farali

Duk Labarai
Hukumomin Saudiyya sun ce fiye da mutum miliyan ɗaya da rabi ne suka isa ƙasar, daga sassan duniya daban-daban domin gudanar da akin hajjin bana. Jaridar Saudi Gazzet, ta ruwaito babban daraktan ofishin kula da bayar da biza na ƙasar, na cewa maniyyata miliyan 1,547,295 ne suka isa ƙasar ta sama da kan iyakokin ƙasa da kuma tasoshin jiragen ruwa. Ya ƙara da cewa maniyyata miliyan 1,483,312 ne suka shiga ƙasar ta jiragen sama, yayin dan mutum 59,273 suka shiga ƙasar ta kan iyakokin ƙasa, sai kuma maniyyata 4,710 da suka je ta jiragen ruwa. A ranar Juma'a 8 ga watan Dhul-Hijja ne za a fara gudanar da aikin Hajji na wannan shekarar.
YANZU-YANZU: Gwamnan Jihar Sokoto Ahmad Aliyu Ya Bada Umarnin Biyan Naira Dubu Talatin A Matsayin Kyautar Goron Sallah Ga Dukkanin Ma’aikatan Jihar Da Na Kananan Hukumomi A Gobe Alhamis

YANZU-YANZU: Gwamnan Jihar Sokoto Ahmad Aliyu Ya Bada Umarnin Biyan Naira Dubu Talatin A Matsayin Kyautar Goron Sallah Ga Dukkanin Ma’aikatan Jihar Da Na Kananan Hukumomi A Gobe Alhamis

Siyasa
Gwamnan Jihar Sokoto Ahmad Aliyu Ya Bada Umarnin Biyan Naira Dubu Talatin A Matsayin Kyautar Goron Sallah Ga Dukkanin Ma'aikatan Jihar Da Na Kananan Hukumomi A Gobe Alhamis. A yayin da masu karbar fansho da alawus za su more kyautar naira dubu ashirin duk a matsayin goron sallah. Daga Real Buroshi Mawaka Sokoto
Faduwar da Tinubu yayi zata iya faruwa akan kowa, Cewar Sheikh Pantami, saidai da yawa sun sokeshi akan bai ce komai ba kan kashe-kashen da ake a Arewa amma gashi yana kare shugaban kasa

Faduwar da Tinubu yayi zata iya faruwa akan kowa, Cewar Sheikh Pantami, saidai da yawa sun sokeshi akan bai ce komai ba kan kashe-kashen da ake a Arewa amma gashi yana kare shugaban kasa

Siyasa
Babban malamin Addinin Islama, sheikh Isa Ali Pantami ya yi martani kan faduwar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yayi a wajan bikin ranar dimokradiyya. Sheikh Pantami ya bayyana cewa, faduwar shugaban kasar bata da alaka da shugabanci kuma zata iya faruwa akan kowa. Ya bayar da shawarar cewa a rika kawar da akai akan irin wadannan labarai zai fi kyau. "This can happen to any of us. It has nothing to do with governance. The earlier we ignore this kind of news, the better. May the Almighty make Nigeria a better place for us." https://twitter.com/ProfIsaPantami/status/1800855807711645873?t=2C5Wqjfz1fhBeyMVkRXelw&s=19 Malam yayi martanine bayan da jaridar Vanguard ta wallafa labarin faduwar shugaban kasar. Saidai malam ya sha martani daga bakin wasu dake cewa bai yi mag...

Alamun ciki a watan farko

Duk Labarai, Gwajin Ciki
Watakila kinga canji a jikinki kin fara tambayar me ya faru? Ko kuma watakila batan wata ko daukewar jinin al'adane kadai kika fuskanta. Wasu matan na ganin alamun shigar ciki a watan Farko yayin da wasu basa gani. Ga alamun da ake gani na shigar ciki a watan Farko: Rashin zuwa jinin Al'ada ko batan wata: Musamman idan kina ganin jinin al'adarki akai-akai amma baki ganshi ba wannan karin, zai iya zama kina da ciki. Canjawar Dabi'a: Zai zamana kina saurin fushi ko kuma haka kawai ki rika jin bacin rai, hakanan zai iya zama kina dariya akan abinda bai kai ayi dariya akansa ba. Cikinki zai rika kuka ko kuma kiji kamar kinci abinci: Cin abinci irin su Aya, Tuwon masara, dawa, ko gero wanda ba'a barza ba, Kwakwa, wake zasu taimaka miki magance wannan matsalar. Zaki ji gabobink...