Saturday, May 9
Shadow

Duk Labarai

Wata Sabuwa:Rikici ya barke tsakanin Jihohin Benue da Ebonyi, An kàshè mutane 6, wasu sun jikkata

Wata Sabuwa:Rikici ya barke tsakanin Jihohin Benue da Ebonyi, An kàshè mutane 6, wasu sun jikkata

Duk Labarai
Mutane 6 ne suka mutu a wani rikici da ya kunno kai tsakanin Al'ummar Ezza dake karamar Hukumar Ado a jihar Benue da kuma makwabtansu Effium na dake jihar Ebonyi. Wannan rikici ya dauki shekara da shekaru yana faruwa inda aka yi iya kokari dan kawo karshen shi amma lamarin ya faskara. Wata majiya daga yankin tace rikicin kwanannan ya barkene ranar Asabar da misalin karfe  2:30 p.m. inda wasu 'yan Bindiga da aka yi amannar daga Effium suke suka afkawa garin Ezza. 'Yan Bindigar sun bude wuta inda suke harbin kan mai uwa da wabi. Rahoton yace maharan sun kuma afkawa kayan mutane da sata. Kokarin jin ta bakin kakakin 'yansandan jihar ya ci Tura.
Kalli Bidiyon yanda kyamarar CCTV ta kama wani Barawon Kwamfuta a Abuja

Kalli Bidiyon yanda kyamarar CCTV ta kama wani Barawon Kwamfuta a Abuja

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wannan Bidiyon ya nuna yanda Kyamarar CCTV ta kama wani Barawon Kwamfuta a Abuja. Mutumin yayi satar ne a wani asibiti dake Abujan saidai ba'a kai ga gane ko wanene ba. https://www.youtube.com/watch?v=Z6fCBJsFiEk Dan haka ake neman duk wanda yasan inda za'w sameshi ya gaggauta sanar da jami'an tsaro.
Kungiyar Magoya bayan Peter Obi sun koma goyon bayan Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu inda suka ce shine zai kai Najeriya ga ci

Kungiyar Magoya bayan Peter Obi sun koma goyon bayan Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu inda suka ce shine zai kai Najeriya ga ci

Duk Labarai
Wata Kungiyar magoya bayan Peter Obi wadda Alhaji Ahmad Abulfathi ya kafa tace sun rushe kungiyar tasu inda suka koma goyon bayan kungiyar magoya bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Kungiyar tace duka rassanta na kasa an rushe su inda suka koma goyon bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Kungiyar tace ta yanke shawarar yin wannan hadaka ne sabida hadin kai sannan ta gano cewa duk da kalubalen da ake fuskanta a mulkin Tinubu amma ai sai an sha wuya akan sha dadi.
Gwamna Abba Gida-gida ya raba fom din JAMB kyauta guda 10,000 ga ɗalibai

Gwamna Abba Gida-gida ya raba fom din JAMB kyauta guda 10,000 ga ɗalibai

Duk Labarai
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya fara rabon don din JAMB ga ɗaliban makarantar sakandire su dubu 10 a jihar. A wajen bikin kaddamar da shirin, gwamna Yusuf, wanda Kwamishinan Ilimi, Ali Haruna Makoda ya wakilta, ya kuma kaddamar da fara bada horo kan zana jarrabawar ta na'ura mai ƙwaƙwalwa. Ya kuma ce gwamnan ya yi alkawarin daukar nauyin kai daliban wajen horon kyauta ba tare da sun biya kudin mota ba. Ya kuma ce duk waɗanda su ka lashe jarrabawar gwamnati za ta zaba musu makaranta mai kyau.
Karya kake, ‘Yansanda suka gayawa basaraken Yashikira na jihar Kwara bayan da yace sabuwar Kungiyar masu ikirarin jìhàdì sun bayyana a karkashin masarautarsa

Karya kake, ‘Yansanda suka gayawa basaraken Yashikira na jihar Kwara bayan da yace sabuwar Kungiyar masu ikirarin jìhàdì sun bayyana a karkashin masarautarsa

Duk Labarai
Basaraken Yashirika na karamar hukumar Baruten jihar Kwara ya bayyana cewa maganar bullar 'yan Bindiga a karkashin masarautarsa gaskiyane. Yace amma abin takaici shine yanda jami'an tsaro ke karyata ikirarin nasu. Yace sun sayo motar da 'yan banga ke amfani da ita suna samar da tsaro a yankin nasu amma wadannan sabbin 'yan Bindiga masu suna Mamuda sun lalata motar. Yace kuma maganar kisan da 'yan Bindigar sukawa mutanensu gaskiya ne amma bai kai 15 ba da ake cewa inda yace kuma kowane bangare ya fuskanci asara. Saidai hukumar 'yansandan jihar ta bakin kakakinta,  SP Adetoun Ejire-Adeyemi tace maganar kisan mutane 15 da aka ce an yi karyane. Sannan yace sun bincika basu gano wata sabuwar kungiyar 'yan ta'adda me suna Mamuda ba. Yace suna baiwa mutane tabbacin samar da tsar...
Matsalar tsaron Najeriya bata yi munin da za’a ce mutane su fara tashi suna kare kansu ba>>Inji Gwamnan jihar Jigawa

Matsalar tsaron Najeriya bata yi munin da za’a ce mutane su fara tashi suna kare kansu ba>>Inji Gwamnan jihar Jigawa

Duk Labarai
Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya bayyana cewa matsalar tsaron Najeriya bata yi munin da za'a fara cewa 'yan Najeriya su tashi su kare kansu ba. A hirar da aka yi dashi a Channels TV yace karfafa mutane su rika kare kansu daga harin 'yan Bindiga zai kai ga kara munana lamarin. Ya bayyana hakane biyi bayan maganar tsohon Ministan tsaro, T.Y Danjuma da yace mutane su rika tashi tsaye suna kare kansu daga masu kai musu hare-hare inda yace gwamnati ka dai ba zata iya ba Saidai Gwamna Umar Namadi yace Danjuma mutum ne wanda bai da wasa amma shi a nashi ganin Gwamnatin tarayya tana kokari duk da yake cewa ba duka matsalar take iya magancewa ba amma tana iya bakin kokarinta. Yace a kokarin magance matsalar rikicin makiyaya da manoma, yayi amfani da Sulhu wanda yace kuma an samu Na...
Ji yanda ‘yansanda suka kamo hadda matar aure a wani samame da suka kai Otal a Jihar Naija, Abinda mijin matar ya mata a ofishin ‘yansanda ya bayar da mamaki

Ji yanda ‘yansanda suka kamo hadda matar aure a wani samame da suka kai Otal a Jihar Naija, Abinda mijin matar ya mata a ofishin ‘yansanda ya bayar da mamaki

Duk Labarai
'Yansanda a jihar Naija sun kai samame a wani otal inda suka kama mutane maza da mata ciki hadda wata matar aure. 'Yansandan sun kai samame otal dinne bayan samun bayanan dake cewa 'yan sara suka na amfani da otal din a matsayin mafakarsu. Mataimakin Gwamnan jihar, Yakubu Garba ne ya bayar da umarnin kai samame maboyar 'yan sara sukan saboda yanda suka addabi mutane. Majiyar tace 'yansanda basu san matar na da aure ba, sai bayan da aka fara kiran dangin wadanda aka kama, mijinta ya je ofishin 'yansandan inda ya mata saki uku nan take. 'Yansandan sun ce basu san abinda ya kai matar auren otal din ba dan haka zasu gudanar da bincike