Friday, December 5
Shadow

Duk Labarai

Hoto:An kamashi Saboda sayar da ‘ya’yanshi har guda 6 a jihar Sokoto

Hoto:An kamashi Saboda sayar da ‘ya’yanshi har guda 6 a jihar Sokoto

Duk Labarai
'Yansanda a jihar sokoto sun kama wani mutum saboda siyar da 'ya'yansa 6. Mutumin ya sayar da jimullar kananan yara 28 ciki hadda 'ya'yan cikinsa 6. Kwamishinan 'yansandan jihar, CP Ali Hayatu Kaigama ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace an kubutar da 21 daga cikin yaran. Mutumin me suna, Bala Abubakar yana baiwa wasu mata, Kulu Dogon yaro da Elizabeth Ojah yaranne inda su kuma suke bashi Naira dubu dari da hamsin ko kuma Naira dubu dari biyu da hamsin. Ana cewa wai za'a kaisu Abujane wajan wani mutum da zai rika kula dasu.
Kalli Hotuna: An kamashi da ma-ka-mai wanda yake shirin sayarwa da ‘yan Bindiga

Kalli Hotuna: An kamashi da ma-ka-mai wanda yake shirin sayarwa da ‘yan Bindiga

Tsaro
'Yansanda a jihar Filato sun kama wani mutum me matsakaitan shekaru da makamai da yake shirin kaiwa 'yan Bindiga. Mutumin ya taho ne daga jihar Zamfara. An kama mutuminne a tashar mota ta NTA park dake Jos. Shugaban tashar, Ibrahim Maikwudi ya tabbatarwa da manema labarai da faruwar lamarin. Yace kadan ya rage mutane su kashe wanda ake zargin amma jami'an tsaro suka tseratar dashi.
A cikin shekara daya da muka yi muna mulki, mun yi maganin Boko Haram>>Gwamnatin Tinubu

A cikin shekara daya da muka yi muna mulki, mun yi maganin Boko Haram>>Gwamnatin Tinubu

Tsaro
Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa ta yi nasarar yin maganin kungiyar Boko Haram. Gwamnatin ta bayyana hakane ta bakin sakataren gwamnatin tarayyar, George Akume. Ya bayyana hakane a Abuja wajan kaddamar da wani Littafi da aka yi kan cika shekara daya da kafuwar Gwamnatin Tinubu. Yace babu wanda zai yi jayayyar cewa gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta yi nasarar gamawa da Kungiyar Boko Haram. Saidai yace har yanzu suna yaki da Kungiyar masu garkuwa da mutane.
An kama mahaifi dan Najeriya saboda zane diyarsa

An kama mahaifi dan Najeriya saboda zane diyarsa

Duk Labarai
'Yansanda a jihar Legas sun kama wani mahaifi me suna Olamide Fatumbi me kimanin shekaru 25 saboda dukan diyarsa me shekaru 3. Mutumin na zaunene a Afeez Street, Akesan, Igando, Lagos State kuma an zargeshi da cutarwa ga diyar tasa. Saidai ya musanta zarge-zargen da akw masa. Mai Shari'a, Mrs E. Kubeinjeya bayar da belin wanda akw zargi akan Naira dubu dari(100,000) da kuma mutane 2 da zasu tsaya masa. An dage sauraren karar sai nan da zuwa 25 ga watan Yuni.
Zamu rama kashe mana sojoji 5 da kungiyar IPOB suka yi, zamu tabbatar mun yi maganinsu>>Inji Hukumar sojojin Najeriya

Zamu rama kashe mana sojoji 5 da kungiyar IPOB suka yi, zamu tabbatar mun yi maganinsu>>Inji Hukumar sojojin Najeriya

Tsaro
Hukumar sojojin Najeriya ta tabbatar da kisan sojoji 5 da kungiyar IPOB suka yi. Hukumar tace an kashe sojojin ne dake rundunar Operation UDO KA da aka kai Obikabia. Tace akwai kuma farar hula 6 da suma aka kashe a yayin harin. Kakakin hedikwatar tsaro, Majo Janar Edward ne ya bayyana hakan inda yace zasu tabbatar sun rama wannan kisan da aka musu. Hukumar sojin tace maharan sun je wajanne a motocin Prado 3 dake da bakin gilashi sannan akwai wasu kuma a yankin da suma suka farwa sojojin.
Ba lallai sai kana da Karatun Bo-ko bane sannan zaka yi nasara a rayuwa>>Inji Shugaban kasar Ingila

Ba lallai sai kana da Karatun Bo-ko bane sannan zaka yi nasara a rayuwa>>Inji Shugaban kasar Ingila

Siyasa
Britain's Prime Minister and Conservative Party leader Rishi Sunak reacts after bowling a ball during a Conservative general election campaign event at the Market Bosworth Bowls Club in Market Bosworth, central England, on May 28, 2024. (Photo by Alastair Grant / POOL / AFP) Firai kinistan Ingila, Rishi Sunak ya bayyana cewa, ba lallai sai mutum na da karatun boko bane zai yi nasara a rayuwa. Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta. Screenshot Saidai lamarin ya jawo cece-kuce sosai inda wasu suka goyi bayansa, wasu kuma suka ce hakan ba daidai bane.
Gwamnatin tarayya ta samo bashin Dala Miliyan dari biyar($500 million) dan gyaran wutar Lantarki

Gwamnatin tarayya ta samo bashin Dala Miliyan dari biyar($500 million) dan gyaran wutar Lantarki

Siyasa
Gwamnatin tarayya ta ciwo bashin dala Miliyan dari biyar, $500 million dan karfafawa kamfanonin rarraba wutar lantarki na kasa. Hukumar BPE tace an ciwo bashinne dan magance matsalolin da suka mamaye kamfanonin rarraba wutar lantarki na kasarnan. Wakiliyar hukumar BPE, Amina Othman ce ta bayyana haka inda tace za'a yi amfani da kudadenne wajan sayo mitocin wuta da sauransu.