Matashiya Joy Amarachi Ihezie, Mai Tuka Keke Napep A Jihar Delta, Tana Da Digirinta Kuma Ta Fara Tukin Kurkura A Shekaru Uku Da Suka Gabata.
Daga Jamilu Dabawa
Sabuwar rawar da gwamnan Osun, Ademola Adeleke yayi ta dauki hankula a shafukan sada zumunta.
Gwamna Adeleke ya shahara wajan rawa a guraren taruka da yake halarta.
Gwamnan dai kawu ne ga shahararren mawakin Najeriya, Davido.
A wannan karin ma ya sake taka rawar a wajan taron karrama mutane da jaridar Vanguard ta yi.
Kalli Bidiyon a kasa:
https://www.tiktok.com/@gbaramatuvoice/video/7372692648819215622?_t=8mnncGdWWP8&_r=1
Yayin da wasu ke yaba mai, wasu na ganin hakan bai dace ba a matsayinsa na gwamna.
Kotu Ta Saka Ranar 13 Ga Watan Yuni Domin Suraren Bukatar Tsige Ganduje Daga Shugabancin Jam'iyyar APC
Jam'iyyar APC reshen Arewa Ta Tsakiya ne suka shigar da bukatar tsoge Gandujen.
Mene ne fatan ku ga Ganduje?
Jami’an ‘yan sanda a jihar Adamawa sun kama wasu matasa biyu da ake zargi da karbar babur mai uku na sata.
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta samu ranar Alhamis, inda ta ce ta kuma kwato babur din da aka sace.
“A ranar 28 ga watan Mayu, 2024, rundunar ‘yan sandan Adamawa ta samu bayanai game da wani keken napep da aka sace a kan titin Chochi, Rumde, Yola ta Arewa” in ji rundunar a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai daukar hotonta na SP Suleiman Nguroje.
“Bayan samun labarin, an tura tawagar ‘yan sanda masu sanya ido a hedikwatar Jimeta Divisional ba tare da bata lokaci ba. An yi sa’a, an kama wani Yusuf Adamu mai shekara 18 da kuma Abdul Salam Abubakar mai shekaru 18 a lokacin da suke kokarin sayar da babur din,” in ji ‘yan sandan.
...
YANZU - YANZU: Shugaba Tinubu ya roƙi kungiyar dattawan Arewa su ja kunnen Gwamnonin yankin dake zuwa su tare a Abuja bayan sun ci zabe.
Majiyar mu ta a yau ta ruwaito Shugaban ya ce yana bakin ƙoƙarinsa a matakin tarayya amma ya kamata a sanya ido kan Gwamnoni su ma su riƙa yin abunda ya dace, su taimaki talakawa, "A lokacin zaɓe ana bin mutane lungu-lungu, gida-gida don neman ƙuri'unsu amma da zaran anci zabe sai kaga Gwamna ko dan siyasa ya tare a Abuja ya mance da talakawansa" inji Tinubu.
Me zaku ce?
Sojojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram 4 a harin da suka kai musu a garin Pulka dake karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.
Lamarin ya farune ranar 30 ga watan Yuni bayan da soiojin sukawa Boko Haram din kwantan Bauna.
Rahoton yace an gwabza kazamin yaki wanda ya kare da Boko Haram din suka tsere.
Kalli hotunan gawarwakin nasu:
Tsohon Ministan Sadarwa Da Tattalin Arzikin Zamani, Professor Isa Ali Pantami Ya Ziyarci Tsohan Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari A Gidansa Dake Daura, Jihar Katsina Yau Alhamis.
Daga Jamilu Dabawa
Rahotanni sunce a jiya, Laraba, 'yan Bindigar da ake kira da wanda ba'a sani ba amma ake kyautata zaton 'yan kungiyar IPOB ne dake son kafa kasar Biafra sun kai hari kan kasuwar Nkwo Ibagwa dake karamar hukumar Igbo-Eze South ta jihar Enugu.
'Yan bindigar sun rika harbi a iska wanda yayi sanadiyyar kisan wannan matashin da hotonsa ke kasa.
'Yan uwa da abokan arziki da yawa sun koka da rashin wannan matashi da aka yi inda da yawa suka hau shafukan Facebook suke alhinin rashin matashin.
Hakanan rahoton Sahara Reports yace 'yan Bindigar sun kona kayan 'yan kasuwa da motoci wanda aka yi kiyasin sun kai na miliyoyin Naira.
A jiya Laraba, wasu majiyoyi sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta gayyaci kungiyar Kwadago ta dawo a ci gaba da tattaunawa kan maganar mafi karancin Albashi.
A zama na karshe dai an tashi baram-baram bayan da NLC din taki amincewa da Naira dubu 60 a matsayin mafi karancin Albashi.
Hakanan wata majiyar tace kungiyar kwadagon ta amince da cewa zata amsa gayyatar ta gwamnati.
Kungiyar dai ta baiwa Gwamnati nan da karshen watan Mayu da muke ciki a gama maganar mafi karancin Albashin ko kuma ta tafi yajin aiki.
Jirgin kasan daya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya kashe kananan yaran wanda tagwayene mata a karamar hukumar Tafa.
Lamarin ya farune da misalin karfe 10 na safe ranar Asabar, kamar yanda jaridar The Cable ta ruwaito.
Yaran, Hassana and Hussaina Baro shekarar su daya da watanni 6.
Kakakin 'yansandan jihar Naija, Wasiu Abiodun ya tabbatar da daruwar lamarin.
Yace yaran suna wasa ne akan titin jirgin kasan kamin lamarin ya faru.