Friday, February 20
Shadow

Duk Labarai

Gwamnatin tarayya ta warewa kamfanij kera makamai na sojoji DICONS Naira Biliyan 8 duk da baya aikin azo a gani

Gwamnatin tarayya ta warewa kamfanij kera makamai na sojoji DICONS Naira Biliyan 8 duk da baya aikin azo a gani

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta warewa kamfanin kera makamai na sojojin Najaria, DICONs Naira N7,940,323,192. Kamfanin wanda aka kirkira a shekarar 1963 a samar dashine dan ya rika kerawa sojojin Najaria makamai. Hakanan dukkan gwamnatocin da aka yi a Najeriya na warewa kamfanin makudan kudade dan ingantashi, saidai har yanzu baya yin wani aikin azo a gani. Duk da kasancewar kamfanin, Har yanzu Najeriya na siyo mafi yawancin makamanta da ake amfani dasu ne daga kasashen waje.
Na ga yanda Manya a gidan yari ke yin Lùwàdì da Kananan yara

Na ga yanda Manya a gidan yari ke yin Lùwàdì da Kananan yara

Duk Labarai
Matashi Segun Olowookere wanda aka yankewa hukuncin kisa saboda satar kaza da kwan kazar a jihar Osun amma daga baya gwamnan jihar, Ademola Adeleke ya yafe masa ya bayyana yanda rayuwar gidan yari ta kasance masa. Ya bayyana hakane a yayin ganawarsa da wakilin jaridar Punchng. Segun ya kwashe shekaru 14 a gidan yari kuma tun yana dan shekara 17 aka kaishi gidan yarin. Daya daga cikin labarin da ya bayar da yace yana damunshi shine yanda manya a gidan yarin ke lalata da kananan yara maza ta hanyar luwadi. Yace daki daya da ya kamata ace mutane 10 ne zasu kwanta a ciki amma sai a tura mutane 50 a ciki. Saidai yace a tsawon shekarun da yayi a gidan yari, bai bari yayi zaman banza ba, yayi karatu sannan yayi aiki tare da asibitin dake gidan yarin.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fara bin manyan Arewa yan rokon su amince da kudirin Haraji da yake son aiwatarwa

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fara bin manyan Arewa yan rokon su amince da kudirin Haraji da yake son aiwatarwa

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fara aika wakilai ga manyan mutane a Arewa dan ya jawo hankalinsu su amince da sabon kudirin dokar canja fasalin Haraji da yake son aiwatarwa. Rahotanni daga fadar shugaban kasa, Kamar yanda jaridar Punchng ta samo sun ce shugaban yana aikawa mutane daidaiku da kungiyoyi wakilai dan jawo hankalinsu su amince da kudirin dokar tasa. Hakan na zuwane a yayin da gwamnonin Arewa suka ki baiwa shugaban kasar hadin kai game da sabuwar dokar harajin. Sabuwar dokar Harajin dai ana ganin zata fi amfanar jihohin kudu wadanda suka fi kawo kudin shiga inda ake maganar jihar data fi kawo kudin shiga itace zata samu kudi masu yawa.
BABBAR MAGANA: Wani Magidanci Ya Taho Tun Daga Kasar Waje Zuwa Ofishin ‘Yan Sandan Jihar Kano Dake Bompai Saboda Shamsiyya

BABBAR MAGANA: Wani Magidanci Ya Taho Tun Daga Kasar Waje Zuwa Ofishin ‘Yan Sandan Jihar Kano Dake Bompai Saboda Shamsiyya

Duk Labarai
BABBAR MAGANA: Wani Magidanci Ya Taho Tun Daga Kasar Waje Zuwa Ofishin 'Yan Sandan Jihar Kano Dake Bompai Saboda Shamsiyya A gobe ne dai hukumar 'yan sandan ta jihar Kano za ta fitar da bayanin dalilin zuwan nasa saboda Shamsiyyar, kamar yadda Kakakin rundunar 'yan sandan Abdullahi Kiyawa ya sanar. Allah Ya sa a ji alkairi.
DARASIN RAYUWA: Fitacçìyaŕ ‘Ýar Tiktok, Khadija Gulma Ta Makançè

DARASIN RAYUWA: Fitacçìyaŕ ‘Ýar Tiktok, Khadija Gulma Ta Makançè

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} DARASIN RAYUWA: Fitacçìyaŕ 'Ýar Tiktok, Khadija Gulma Ta Makançè Wani iko na Allah shine, Khadija ta bayyana cewa sai ta rufe ido daya sannan take gani. Sannan kuma wani sashe na jikinta ya fara şhànyewà. Allah Ya ba ta lafiya.
Jaruman Kannywood da suka rasu a 2024

Jaruman Kannywood da suka rasu a 2024

Duk Labarai
Har yanzu masana'antar Kannywood da masu bibiyarta suna tunawa tare da jimamin rasuwar fitaccen mawaƙi El'mu'az Birniwa, wanda ya rasu a daren Laraba, 4 ga Disamban 2024 a Kaduna. Irin yanayin da mawaƙin ya yi rasuwar fuju'a ce ta sa jimaminsa da ake yi ya ɗauki lokaci, kamar yadda ake yi idan an yi mutuwar farat-ɗaya. Mawaƙi El-Mu'aza ya shiga sahun irin su Saratu Daso da Mustapha Waye da darakta Aminu S. Bono wajen yin irin rasuwar ta fuju'a. A daidai wannan lokaci da muka yi ban-kwana da shekarar 2024, BBC ta tattaro wasu ƴan masana'antar da suka bar duniya a shekarar. Fatima Sa’id (Bintu) A ranar Lahadi 11 ga Fabrairun 2024 ne Allah ya yi wa jaruma Fatima Sa'id, wadda aka fi sani da Bintu Dadin Kowa rasuwa. Jarumar wadda ta fi yin fice a shirin na tashar Arewa24 t...
Lakurawa sun kashe ƴan sanda biyu, sun yi awon gaba da shanu sama da 500 a Kebbi

Lakurawa sun kashe ƴan sanda biyu, sun yi awon gaba da shanu sama da 500 a Kebbi

Duk Labarai
Ana ci gaba da samun bayanai game da harin da ƴan ƙungiyar nan ta Lakurawa suka kai garin Na-tisne na yankin ƙaramar hukumar Arugungun ta jihar Kebbi. Harin wanda suka kai a ranar Alhamis da daddare, ya janyo mutuwar ƴan sanda biyu inda kuma suka kore shanu fiye da 500. Sai dai an samu nasarar murƙushe maharan, a sakamakon wani ƙoƙari na haɗin gwiwar gwamnatin jihar Kebbi da jam'an tsaro. Shugaban ƙaramar hukumar Arugungun ta jihar Kebbi, Honarabul Aliyu Gulma ya shaida wa BBC cewa tun bayan faruwar sojoji da sauran jami'an tsaro sun bi sahun ƴan bindigar tare da kashe da dama daga cikinsu. "Hankali ya fara kwanciya zuwa yanzu. Ana kuma ƙoƙarin mayar da sauran dabbobi da aka ƙwato daga hannunsu," in ji Gulma. Ya kuma ce gwamnatin jihar ta girke jami'an tsaro da yawa a yankin...