A yayin da ta fara yajin aiki a yau, Kungiyar Kwadago ta NLC ta kulle tashar wutar Lantarki ta Najeriya inda hakan ya jefa kasar cikin duhu.
Rahoton TheCable ya bayyana cewa, dauke wutar ya faru ne da misalin karfe 2: 19 na tsakar daren daya gabata.
Ministan kudi Wale Edun ya bayyana cewa duk da hauhawar farashin kayayyaki da ake fama dashi, ana tsammanin nan gaba kadan matsalar zata ragu.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV a jiya Lahadi.
Yace gwamnatin Tinubu ta dauki matakai na magance matsalar kuma tattalin arzikin kasarnan na tafiya ta hanyar dake nuna ci gaba.
Ya bayar da tabbacin cewa, cikin 'yan watanni masu zuwa za'a ga canji da ci gaba ta fannin tattalin arzikin
Hukumar 'yansandan Najeriya sun roki kungiyar kwadago ta NLC da ta rungumi sulhu ta janye yajin aikin data shiga.
Hukumar a wata sanarwa data fitar tace tabbas kungiyar kwadago ta NLC na da ikon shiga yajin aikin amma ya kamata a bi dokar da kasa ta tanadar dan kaucewa take doka da oda.
Hukumar 'yansandan tace wannan yajin aikin zai jawo fargaba da kuma dumamar yanayin siyasa.
Dan hakane 'yansandan ke kira da NLC ta janye yajin aikin ta koma teburin sulhu da gwamnati.
Hukumar 'yansandan ta kuma baiwa jama'a tabbacin samar da tsaro inda tace ta kai jami'anta gurare da yawa dan tabbatar da ba'a karya doka ba.
Gwamnatin tarayya ta jaddadawa Kungiyar Kwadago cewa, ba zata iya biyan Sama da Naira Dubu 60 ba a matsayin mafi karancin Albashi ba.
Hakan na zuwane a Yau, Litinin da kungiyar ta kwadago ta fara yajin aikin sai baba ta gani.
Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi ya bayyanawa kungiyar kwadagon da ma'aikatan gwamnatin tarayya cewa tafiya zuwa yajin aiki sabawa doka ne.
Yace kuma zasu iya fuskantar daurin watanni 6 saboda tafiya yajin aikin.
Ya bayyana cewa, har yanzu akwai tattaunawa tsakanin gwamnati da kungiyar kwadagon kuma ba'a kammala ba dan haka bai kamata kungiyar ta tafi yajin aiki ba.
Ya roki kungiyar kwadagon data sake tunani kan wannan mataki data dauka inda yace bai kamata ba dan zai jefa da yawan 'yan Najeriya cikin halin kaka nikayi da wah...
An dakatar da dan kwallon kungiyar Monaco Mohamed Camara Saboda yaki yadda yayi tallar Luwadi.
An dai baiwa 'yan Kwallon kaya da tambarin Luwadi a jiki shine ya samu wani abu ya rufe nashi tambarin na luwadi dake jikin rigarsa.
Dalilin hakane yasa aka dakatar dashi na tsawon wasanni 4.
Camara wanda musulmi ne ya ki yadda yayi tallar luwadinne dan kare martabar addininsa.
Gwamna Bala na Jihar Bauchi Ya Halarci Jana'izar Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Allah Ya Karɓi Rayuwarsa A Daren Jiya
Gwamna Bala Mohammed ya halarci Sallar Jana’izar Marigayi Alh Ahmad Aliyu Jalam Kwamishinan ƙananan Hukumomi na jihar Bauchi wanda ya Rasu a sakamakon hatsarin Mota Daga Bauchi Zuwa Jalam
Gwamna Bala Mohammed ya bayyana shi a matsayin abokin aiki mai himma da kwazo da bayar da gudunmawar ci gaban Gwamnatin PDP a Jihar Bauchi.
Ya ƙara da cewa Rasuwar Ahmed Aliyu Jalam ta haifar da zullumi tare da yin zaman makoki, yana mai rokon Allah ya ba shi AlJannati Firdausi, ya kuma baiwa iyalansa kwarin guiwar jure wannan babban rashi.
Sai dai ya jajantawa ‘yan uwa da al’ummar Jalam a madadin Gwamnatin jihar da jam’iyyar PDP da daukacin al’ummar jihar Bauchi.
Manyan ja...
Aminu Waziri Tambuwal ya ce sun gargaɗi ƴan Najeriya kan sake zaɓen APC a 2023.
Tsohon gwamnan na Sokoto ya bayyana cewa halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan yanzu, kin ɗaukar shawara ne ya kawo shi.
Tambuwal ya bayyana hakane a wajan wani taron maau ruwa da tsaki na jam'iyyar a jihar Sokoto.
Yace sun gayawa mutane, APC mulki kawai take aon samu ta ganta a ofis.
Yace gashi yanzu sun samu amma sun rasa yanda zasu yi dashi.
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN
Hazikin Dansanda ASP Usman Lawal Tangible Ya Rasu A Katsina
Allah Ya Yi Wa Hazikin Dansanda ASP Usman Lawal Tangible Rasuwa A Garin Malumfashi, Jihar Katsina Yau Lahadi.
An Yi Jana'izarsa Kamar Yadda Addinin Musulunci A Gidansa Dake Bisije Babban Gida, Karamar Hukumar Malumfashi Jihar Katsina.
Allah Ya Jikansa Da Rahama!
Daga Jamilu Dabawa, Katsina