Bishop Kukah Wanda babban malamin Kiristane ya bayyana goyon bayansa da amincewa da kudirin dokar canja yanda ake karba da raba Haraji a Najeriya.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV.
Kuka yace sabuwar dokar zata bayar da damar kawo canji kan yanda ake kashe kudi ba kai ba gindi.
Yace kuma dokar zata karfafa gasa tsakanin jihohi ta hanyar samun kudin shiga.
Maganar kwace gidaje 753 daga hannun tsohon gwamnan babban banking Najeriya, CBN, Godwin Emefiele ta jawo cece-kuce tsakanin hukumar EFCC da mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore.
EFCC a yayin da ta wallafa maganar kwace gidajen tace an kwacesune kawai daga hannun wani babban jami'in Gwamnati ba tare da fadar sunanshi ba.
Dalilin hakane Sowore ya zargi EFCC da yin rufa-rufa akan lamarin inda yace daga hannun Emefiele ne aka kwace gidajen.
Saidai EFCC ta musanta hakan, a martaninsa, Sowore ya wallafa takardun kotun Wanda suka nuna yanda aka zartar da hukuncin kwace gidajen da sunayen mutanen sake da hannu a lamarin.
A jiyane muka samu labarin cewa, kotu a Abuja ta kwace wasu gidaje 753 daga hannun wani tsohon ma'aikacin gwamnati inda ta mallakawa gwamnatin tarayya su.
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC ce ta bayyana haka a wata sanarwa data fitar inda tace kamen shine mafi girma da aka taba yi a tarihinta.
Saidai bata bayyana sunan jami'in gwamnatin data kwace wadannan kadarorin daga hannunsa ba.
A sabon rahoton da muka samu, Mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore ya bayyana cewa, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele ne aka kwace wadannan gidaje daga hannunsa.
Emefiele dai tun hawan mulkin shugaba, Bola Ahmad Tinubu ake bincikensa da laifuka daban-daban.
Wasu hotuna daga wajan da take daukar wani film din Hausa sun jawo cece-kuce.
Dalili kuwa shine an ga dan kamfai(pant) a wajan daukar film dinne inda aka shanyashi akana taga.
Da yawan masu bayyana ra'ayi sun fadi abubuwa iri-iri kan lamarin.
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci EFCC ta yi babban kamun da bata taba yin irinsa ba run bayan kafata a shekarar 2003.
Hukumar CE ta sanar da haka a shafinta na sada zumunta.
Tace kotu ta kwace wasu gidaje 753 da aka Gina da kudin sata.
Saidai EFCC bata bayyana sunan Wanda ta kwace kadarorin daga hannunsa ba, Inda kawai race babban jami'in gwamnatine.
Tace taba ci gaba da bincikensa.
Wannan bidiyon ya dauki hankula inda aka ga wani mutum shi kadai ya gagari 'yansandan Najeriya su biyu.
A bidiyon dai an ji yanda 'yan kallo suka rika ihu.
Kalli bidiyon anan
Wannan wani barawon wayane da ala kama ya dura hannu cikin mota zai warcewa wani wayarsa.
https://twitter.com/wakajugbe/status/1861493842756698348?t=0n0tnj4_lmMmJwGVwuqQEQ&s=19
Mutanen motar sun rikeshi inda akai ta tafiya dashi a haka.
Wasu daga cikin sojojin Najeriya dake yaki da kungiyar Boko Haram a dajín Sambisa dake jihar Borno sun koka da yanda aka barsu suka da de a dajin ba tare da canjasu ba.
Sunce tun shekarar 2018, watau shekaru 6 kenan har yanzu ba'a canjasu an kai wasu wajan ba.
Sojojin sunce dadewar da suka yi a wajanne yasa gwiwarsu ta yi sanyi da yaki da kungiyar Boko Haram har take samun galaba a kansu.
Sannan sunce matansu dake gida sun fara yin lalata da abokansu sojoji da kuma fararen hula saboda dadewar da suka yi basu gansu ba.
Sojojin sun yi rokon cewa wannan dadewa da aka bari suka yi a fagen daga ta sabawa dokar aikinsu dan haka suke kiran manyansu dasu canjasu ko sun samu sa'ida.
Sojojin sun bayyana hakane a wata hira da jaridar Sahara Reporters saidai basu yadda an fadi sunayensu...
Matar tsohon gwamanan jigar Ondo, Rotimi Akeredolu, Betty Akeredolu na fuskantar zargin hannu a mutuwar mijin nata.
Betty dai a baya wadda inyamurace, ta bayyana kabilar Yarbawa da cewa basu da asali saboda yawan zinace-zinace da matan aure da mazajensu ke yi, tace da yawa yaran yarbawa basu san ubanninsu ba.
Wannan magana tawa yarbawa da yawa zafi inda suka yi ta mata raddi.
Ana cikin hakane kuma sai aka sake samun Betty ta mayarwa wani martani da yace mijin nata tsohon me kwakulo kawunan matattu me a kabari, wani zargi da Inyamurai ke yiwa yarbawa saboda yin tsafi.
Dalilin hakane yarbawa da yawa ke neman ya kamata a binciki Betty akan mutuwar mijinta saboda yanda take nuna bata damu ba dan anci zarafinsa.