Abin da ya sa na ajiye aiki a fadar shugaban ƙasa – Bayani dalla-dalla daga bakin Dr Baba-Ahmed
Tsohon mai bai wa shugaban Najeriya Bola Tinubu shawara kan harkokin siyasa Dr Hakeem Baba-Ahmed ya shawarci shugaban ƙasar ya haƙura da neman takarar wa'adin Mulki na biyu a 2027.
Dr Baba-Ahmed wanda ya yi wa shugaba Tinubu aiki a ofishin mataimakin shugaban ƙasa ya ce ya kamata yayi dattawan da ke riƙe da muƙaman siyasa a yanzu su fahimce cewa lokaci ya yi da za su janye jiki domin bai wa masu jini a jiki damar jan ragama.
Ya shaida wa BBC cewa tsawon lokacin da ya shafe a matsayin mai bayar da shawara ga gwamnatin shugaba Tinubu, ya ga kurakurai da dama da suka bayyana ƙarara cewa gwamnatin ba ta ɗauki hanyar gyara ɓarnar da ta tarar ba. Kuma wannan na cikin dalilansa na ajiye miƙamin sa na bayar da shawara.
Kwanaki kaɗan bayan ya fito ya tabbatar wa duniya cewa ya ajiye miƙami...








