Kungiyar IPMAN ta cimma matsaya da Dangote kan sayen fetur
Ƙungiyar dillalan man fetur ta Najeriya mai zaman kanta IPMAN ta ce mambobinta sun kammala cimma matsaya domin fara siyan tataccen man fetur daga matatar man Dangote kai tsaye.
Sun bayyana haka bayan uwar ƙungiyar ta gudanar da taro da mambobinta domin bin bahasin yarjejeniyar da suka cimma da matatar da kuma hanyoyin samun man cikin sauki.
Alhaji Zarma Mustapha, wani jigo a ƙungiyar ta IPMAN ya shaidawa BBC shirin da suka yi bayan tattaunawar da suka yi da shugabannin matatar a ranar litinin, inda ya ce wannan mataki da suka ɗauka zai haifar da wadatan man fetur a duk faɗin ƙasar.
''Ina bayar da tabbacin cewa muddin muka fara sayen mai kai-tsaye daga Dangote, ba za a rika samun ƙarancin man fetur a ƙasar nan ba, kuma muna sa ran cewa matatan gwamnati ma za su fara aiki nan bada j...








