Wednesday, February 18
Shadow

Duk Labarai

Gwamnan Kano ya gabatar da kasafin kuɗin sama da naira biliyan 500

Gwamnan Kano ya gabatar da kasafin kuɗin sama da naira biliyan 500

Duk Labarai
A jihar Kano, wacce ta fi yawan al’umma a arewacin Najeriya, gwamnan jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kasafin kuɗin shekara ta 2025 a gaban majalisar dokokin jihar. Kasafin kuɗin na bana wanda shi ne na biyu da gwamnan ya gabatar ya kai fiye da naira biliyan 500B. Duk da kasancewar jihar cibiyar harkokin kasuwanci amma ta na sahun gaba wajen yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, abin da ya sa gwamnati ta ware fiye da kashi 31 na kasafin ga ilimi. Ma'aikatu da kuɗin da aka ware musu: Ilimi: Naira biliyan 168.4 (kashi 31%) Lafiya: Naira biliyan 90. 6 Sufuri: Naira biliyan 12. 2 Harkokin noma: Naira biliyan 21.03 Albarkatun ruwa: Naira biliyan 27. 23 Samar da ababen more rayuwa: Naira biliyan 70.78
Trump ya ce ba shi da wani zaɓi illa korar dubun dubatar baƙin haure

Trump ya ce ba shi da wani zaɓi illa korar dubun dubatar baƙin haure

Duk Labarai
Zaɓaɓɓen Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba shi da wani zaɓi "da ya wuce" korar dubun dubatar baƙin haure da ba su da izinin zama a ƙasar. Cikin wata tattaunawa da NBC ranar Alhamis, shugaban ya ce: "Ba magaanr abin da za mu samu ko rasawa ba ce. Ba haka ba ne - ba mu da wani zaɓi ne. Idan ana kashe mutane, jagororin 'yanƙwaya na lalata ƙasashe, to yanzu za su koma ƙasashensu saboda ba za su zauna mana a nan ba." Ko da gwamnatin ta yi nasarar koro baƙin a hukumance, to za ta sha fama wajen yadda za ta aiwatar da hakan. Ƙwararru na ganin hakan zai laƙume biliyoyin dala kafin a iya mayar da mutum miliyan ɗaya gida. A shekarar 2021 aka dakatar da shirin kai samame kan wuraren ayyukan baƙin, wanda gwamnatin Trump ta aiwatar. Adadin mutanen da ake kamawa a cikin Amurka tare da ma...
Gwamnan Katsina ya ƙaddamar da ƙarin dakarun tsaro na jihar

Gwamnan Katsina ya ƙaddamar da ƙarin dakarun tsaro na jihar

Duk Labarai
Gwamnan Katsina ya ƙaddamar da ƙarin dakarun tsaro na jihar. Gwamnatin jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta ƙaddamar da sabbin rukunin jami’an tsaro na da ake kira KTS C-Watch. Dakarun tsaron unguwannin 550 su ne kashi na biyu da Gwamna Dikko Umaru Radda ya ƙaddamar a yau Juma'a da zimmar yaƙi da 'yanfashin daji masu sacewa da kashe mutane haka kawai. "Mun ɗauki mutum 6,652 domin daƙile matsalar tsaro. Sannan mun nemi masu gari, da limamai, da ladanai, tare da ba su albashi a matsayin wani ɓangare na shirin samar da tsaro a unguwanni," a cewar gwamnan.
Gwamnan Kano Abba zai kori kwamashinonin da ba su da himma

Gwamnan Kano Abba zai kori kwamashinonin da ba su da himma

Duk Labarai
Gwamnan Kano Abba zai kori kwamashinonin da ba su da himma. Gwamnan jihar Kano a arewacin Najeriya ya bayyana aniyarsa ta sauke duk wani kwamashinansa da "aka gano ba shi da himm" a aikinsa nan gaba kaɗan. Wata sanarwa da mai magana da yawunsa Sanusi Bature ya fitar ta ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamatin da ke duba ƙwazon kwamashinonin. "Nan gaba kaɗan al'umma za su ji matakin da gwamnatin za ta ɗauka," in ji sanarwar. Ya ƙara da cewa “gwamnan ya ce rahoton ma ba zai yi wani amfani ba yanzu saboda tsawon shekara ɗaya da rabi da ya yi yana aiki ntare da su ya ba shi damar gane himmarsu ciki da baya, saboda haka da kansa zai yanke hukuncin”. Yanzu haka dai jam’iyyar NNPP mai mulki a Kanon na fama da rikici, musamma a ɓangaren ƙungiyar Kwankwasiyya da tsoho...
Me ya sa gwamnatin Malaysia za ta hana amfani da motocin CNG?

Me ya sa gwamnatin Malaysia za ta hana amfani da motocin CNG?

Duk Labarai
Matakin da gwamnatin ƙasar Malaysia ta ɗauka cewa daga ranar 1 ga watan Yulin 2025 za ta daina amfani da motoci masu amfani da makamashin iskar gas na CNG ya haifar da fargaba a Najeriya. A farkon makon nan ne ministan sufurin ƙasar, Loke Fook, ya bayyana haka a wani taron manema labarai a ƙasar. Ya ce babban kamfanin mai na ƙasar zai hana sayar da makamashin na NGV (da ya ƙunshi CNG da LPG) a gidajen man da ake sayar da shi a faɗin Malaysia. Mista Look ya ce an ɗauki matakin ne domin kare rayukan masu ababen hawa da sauran al'ummar ƙasar. “Tankunan waɗannan motoci masu amfani da makamashin NGV a yanzu sun kai adadin shekarun da ya kamata a ce sun daina aiki, don haka dole mu sake su, saboda sun kai shekara 15 da aka saka wa motocin''. An ɓullo da amfani da makamashin NGV a ...
Wutar Lantarkin Najeriya bata kara lalacewa ba a yau,Juma’a labarin karyane ake yadawa>>Inji Gwamnati

Wutar Lantarkin Najeriya bata kara lalacewa ba a yau,Juma’a labarin karyane ake yadawa>>Inji Gwamnati

Duk Labarai
Hukumar dake kulabda tsayuwar wutar Lantarki a Najeriya ta musanta cewa wutar lantarkin Najeriya ta sake lalacewa. A sanarwar data fitar ta kafar Twitter, tace a yi watsi da duk wani labari dake cewa wutar lantarkin Najeriya ta sake samun matsala. https://twitter.com/NationalGridNg/status/1854858514759405927?t=rMAr896DbG_IQl_kpeN_6g&s=19 A ranar Alhamis ne dai wutar lantarkin ta samu matsala a Najeriya wanda hakan ya jefa kasar cikin duhu.
Masu zanga-zanga sun je majalisar tarayya suna neman a kori shugaban NNPC Mele Kolo Kyari daga aiki

Masu zanga-zanga sun je majalisar tarayya suna neman a kori shugaban NNPC Mele Kolo Kyari daga aiki

Duk Labarai
Wasu kungiyoyin dake ikirarin fafutuka sun je majalisar tarayya suna neman a kori shugaban Kamfanin mai na kasa, NNPCL Mele Kolo Kyari daga aiki. Sun kuma nemi a yi bincike dan gano masu yiwa shirin gyaran matatun man fetur zagon kasa a Najeriya. Sun ce shugabancin Mele Kolo Kyari ya yiwa Matatun man fetur na Najeriya illa sosai. Shugaban kungiyar, Segun Adebayo, ya jawo hankalin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya jawa shugabancin kamfanin man fetur din na kasa, NNPCL kunne kan kasa su kara daukar wasu matakai da zasu kara jefa tattalin arzikin kasarnan cikin matsi. Kungiyar tace Najeriya zata iya tace man da za'a yi amfani dashi a cikin kasarnan amma saboda zagon kasa an hana hakan faruwa. Ta kara da cewa Misali ga Aliko Dangote ya bude matatar man fetur amma masu zago...
Kalli yanda wannan mutumin yawa kansa dan ya daina shan taba

Kalli yanda wannan mutumin yawa kansa dan ya daina shan taba

Duk Labarai
Wani mutum dan kasar Turkiyya da shan taba yawa katutu ya rasa yanda zai yi ya kulle kansa a cikin keji dan ya daina wannan dabi'a. Mutumin me suna Ibrahim Yucel, bayan ya kulle kansa ya baiwa matarsa makullin inda take budeshi kawai idan zai ci abinci. Saidai zuwa yanzu ba'a san ko hakan ya taimaka masa wajan cimma burinsa ba. Rahotanni sun bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne bayan da cutar dajin huhu ta kashe mahaifinsa.
Shugaban ‘Yansandan Najeriya ya bayar da umarni ga ‘yansanda su daura bakin kyalle dan nuna Alhinin rayuwar shugaban sojoji

Shugaban ‘Yansandan Najeriya ya bayar da umarni ga ‘yansanda su daura bakin kyalle dan nuna Alhinin rayuwar shugaban sojoji

Duk Labarai
Shugaban 'yansandan Najeriya, IGP Kayode ya bayar da umarni ga 'yansandan kasarnan da su daura bakin kyalle na tsawon kwanaki 7 dan nuna alhinin rasuwar shugaban sojoji Lt. Gen. Taoreed Lagbaja. Kakakin 'yansandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai. Yace wannan matakine da aka dauka dan girmama tsohon shugaban sojojin da kokarin da ya nuna wajan yaki da matsalar tsaro.