Wednesday, February 18
Shadow

Duk Labarai

Za mu kawo ƙarshen Lakurawa cikin ƙanƙanin lokaci- Hedkwatar tsaro

Za mu kawo ƙarshen Lakurawa cikin ƙanƙanin lokaci- Hedkwatar tsaro

Duk Labarai
Rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da ɓullar ƙungiyar lakurawa waɗanda suke tayar da zaune tsaye a tsakanin jihohin Sokoto da Kebbi. Daraktan watsa labarai na hedkwatar ne ya tabbatar da hakan a Abuja, kamar yadda kafofin watsa labarai suka ruwaito, inda ya ƙara da cewa suna da tabbacin ɓullar ƙungiyar a Sokoto da Kebbi. Sai dai ya ƙara cewa ƙungiyar ba za ta yi wani tasiri ba, domin a cewarsa sojojin Najeriya a shirye suke, kuma za su ga bayansu cikin ƙanƙanin lokaci. Lakurawa wata ƙungiya ce ta ƴanbindiga da suka fara addabar mutanen Sokoto da Kebbi, kuma sun fito ne daga ɓangaren yankin Sahel da ya ƙunshi ƙasashen Nijar, da Mali, kuma mutane ne da suka ƙunshi ƙabilu daban-daban na Sahel.
Likitocin Kano sun dakatar da shiga yajin aiki

Likitocin Kano sun dakatar da shiga yajin aiki

Duk Labarai
A jihar Kano, ƙungiyar likitoci ta umarci likitocin jihar su koma bakin aiki bayan janye yajin aikin da aka wayi gari da shi a asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad a ranar Alhamis. Likitocin dai sun shiga yajin aikin ne bayan cikar wa’adin sa’o’i 48 da ƙungiyar ta baiwa gwamnan jihar, na ya kori kwamishiniyar jin ƙai ta jihar, Amina Abdullahi HOD, bisa zargin cin zarafin wata likita a asibitin, zargin da ta ce musanta. Duk da cewa likitocin sun janye yajin aikin amma ƴan sa’o’in da aka shafe babu likitoci a asibitin na Murtala Muhammad har an ga tasirinsa, inda ya shafa majinyata.
An yi hasashen ƴan Najeriya miliyan 33 za su yi fama da yunwa a 2025

An yi hasashen ƴan Najeriya miliyan 33 za su yi fama da yunwa a 2025

Duk Labarai
Wani rahoto da aka fitar ya nuna cewa yunwar da ake fama da ita a Najeriya zai iya tsananta a shekarar 2025, inda aka yi hasashen cewa aƙalla mutum miliyan 33 ne za su iya shiga yunwa a shekarar ta baɗi. Ƴan Najeriya a yanzu sun kai kusan miliyan 223.8. A rahoton, wanda Cadre Harmonisé ta yi a ƙarƙashin kulawar gwamnatin tarayya, da haɗin gwiwar shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ne ya bayyana hakan, inda rahoton ya yi hasashen cewa ƴan ƙasar aƙalla miliyan 33.1 ne za su fuskanci yunwa. Rahoton ya ta'allaƙa hasashen ne kan yanayin taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar da hauhawar farashin kayayyaki da sauyin yanayi da rikce-rikice a wasu yankuna na arewacin ƙasar. Rahoton ya ƙara da cewa tsakanin Oktoba zuwa Disamban 2024, kimamin mutum miliyan 25.1 ake hasashen za...
Koda mun gyara wutar Najeriya kara lalacewa zata yi saboda injinan wutar sun tsufa>>TCN

Koda mun gyara wutar Najeriya kara lalacewa zata yi saboda injinan wutar sun tsufa>>TCN

Duk Labarai
A yayin da matsalar wutar lantarki ta zama ruwan dare a Najeriya, Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin yin gyaran gaba dayan matsalar wutar. Gyaran dai zai dauki nan da zuwa watanni 6 har shekara 1. Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ne ya bayyana hakan inda yace a canja injinan wutar lantarkin da magance matsalar wutar gaba daya. Kakakin Ministan, Bolaji Tunji ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar. Dama a baya an kafa wani Kwamiti da ya gano matsalolin wutar wanda suka hada da tsaffin injina da rashin kula da injinan yanda ya kamata da kuma karancin Injinan da zasu samarwa Najeriya ingantacciyar wutar lantarkin. Kwamitin dai ne ya bayar da shawarar yanda za'a kawo karshen matsalar wutar wanda ministan yace a gaggaura yin amfani da shawarar kwamitin.
Kalli Hotuna: Matashiya ta hau gini me tsawo ta fado ta mùtù bayan da aka hanata shigar banza a kasar Iràn

Kalli Hotuna: Matashiya ta hau gini me tsawo ta fado ta mùtù bayan da aka hanata shigar banza a kasar Iràn

Duk Labarai
Wata matashiya 'yar kasar Afghanistan da ke karatu a jami'ar kasar Iran ta hau saman gini me tsawo ta fado ta mutu bayan da aka hanata yin shigar banza. Matashiyar dai me suna Arezo Khavari 'yar Kimanin shekaru 16 tana da son saka wando saidai jami'an da'a na Iran sun hanata sawa, sannan bata son saka dankwali inda aka ce mata idan dai ba zata rika saka dankwali ba za'a koreta daga makarantar. Abokan ta dai sun ce barazanar korar ta daga makarantar ya daga mata hankali sosai inda ta yi ta amai. Babanta yace ta sameshi hankalinta a tashe inda ta rika gaya mai cewa,ya tayata da addu'a Allah yasa kada a koreta daga makarantar. Hakanan abokanta sunce a baya makarantar ta rika takurawa dalibar inda ake mata fada saboda ta cika wasa da yawan dariya da yawan abokai. A ranar da la...
Gwamnatin Najeriya za ta fara yi wa mata tiyatar haihuwa kyauta

Gwamnatin Najeriya za ta fara yi wa mata tiyatar haihuwa kyauta

Duk Labarai
Ma'aikatar lafiya a Najeriya ta ƙaddamar da wani shiri na yi wa mata masu ciki tiyata kyauta a faɗin ƙasar. Shirin da aka yi wa take da Maternal Motality Reduction Innovation Initiative Mamii), an ƙaddamar da shi yayin wani taron bita na shekara-shekara a Abuja. Ministan Lafiya Muhammad Ali Pate ya bayyana shirin da zimmar rage mutuwar mata yayin haihuwa a faɗin Najeriya. "Babbar manufar wannan shiri ita ce yi wwa mata marasa ƙarfi tiyatar haihuwa kyauta, amma waɗanda suka cika ƙa'ida a asibitocin gwamnati da na kuɗi," a cewar ministan. "Ta hanyar cire matsalolin kuɗi, muna ganin babu wata mace da ya kamata a bari ba tare da an kula da ita ba ko da ba ta da kuɗi." Ya ƙara da cewa mutuwa yayin haihuwa na ci gaba da zama barazana, inda ƙananan hukumomi 172 ke haifar da kashi 5...
Abubuwa bakwai da Trump ya ce zai yi a matsayin shugaban Amurka

Abubuwa bakwai da Trump ya ce zai yi a matsayin shugaban Amurka

Duk Labarai
Donald Trump na kan hanyar komawa fadar White House bayan da ya alƙawarta kawo ƙarshen wasu matsaloli ciki har da batun 'yan cirani, da tattalin arziki, da yaƙin Ukraine. Da alama ya samu ɗimbin magoya baya sakamakon manufofinsa na siyasa, musamman a majalisar dokokin ƙasar bayan da jam'iyyarsa ta Republican ta sake ƙwace iko da majalisar dattawan ƙasar. A jawabin murnar lashe zaɓe da ya gabatar, Mista Trump ya sha alwashin ''yin mulkin bisa taken: 'Cika alƙawuran da muka ɗauka'. Amma a wasu fannonin, ya bayar da taƙaitaccen bayanin yadda zai cimma manufofin nasa. A lokacin da kafar yaɗa labarai ta Fox News ta tambaye shi a 2023, ko zai yi amfani da kujerarsa ta hanyar da ba ta dace ba, ko muzguna wa 'yan adawar siyasa? Sai ya ce ba zai yi ba, ''in ban da a ranar farko''. "A...