Tuesday, February 17
Shadow

Duk Labarai

Ba zamu yadda a saka shari’ar Musulunci a cikin tsarin kudin mulkin Najeriya ba>>Inji Lauya Kola Alapinni

Ba zamu yadda a saka shari’ar Musulunci a cikin tsarin kudin mulkin Najeriya ba>>Inji Lauya Kola Alapinni

Duk Labarai
Lauya Kola Alapinni ya aikewa da ofishin kakakin majalisar dattijai, Godswill Akpabio cewa basu amince da saka shari'ar Musulunci cikin kudin tsarin mulkin Najeriya ba. Yayi hakan ne bayan kudirin dokar da dan majalisa Aliyu Bappa Misau ya gabatar a gaban majalisar cewa ya kamata a saka shari'ar Musulunci a tsarin kasuwanci da kwangila da sauransu. An yi muhawara sosai a farfajiyar majalisar kan lamarin inda hakan ya jawo cece-kuce. Lauyan ya kawo misali da cewa a kwanakin baya an rika kisa da kama wasu da suke aikata abubuwan da suka sabawa shari'ar Musulunci a Arewa inda yace su a kudu ba zasu akince da hakan ba.
Kuma Dai: An kara kara farashin Man Fetur

Kuma Dai: An kara kara farashin Man Fetur

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa a yayin da 'yan kasuwar man fetur ke shirin fara dauko mai daga matatar man fetur ta Dangote gidajen man fetur da yawa sun kara farashin litar man. Hakan na zuwane bayan da gwamnatin tarayya ta amince 'yan kasuwar su dauki man fetur kai tsaye daga matatar man fetur ta Dangote ba tare da dillancin kamfanin man fetur na kasa NNPCL ba. Wasu gidajen man fetur din sun mayar da farashin litarsu zuwa Naira 1,250 inda wasu kuma suka mayar da farashin zuwa 1,300. Wasu na sayarwa akan farashin 1,150 inda wasu ke sayarwa akan farashin 1230. Majiyar Hutudole ta yi hira da wasu masu ababen hawa da suke shan man fetur inda suka rika bayyana rashin jin dadinsu akan lamarin hauhawar farashin man fetur din a kusan duk kwanaki kalilan. Cire tallafin man fetur dai na...
Yabon Tinubu ya kamata a yi game da cire tallafin man fetur ba zagi ba saboda sauran shuwagabanni Najeriyakasa cirewa suka yi amma shi ya cire>>Inji Hadiminsa, Sunday Dare

Yabon Tinubu ya kamata a yi game da cire tallafin man fetur ba zagi ba saboda sauran shuwagabanni Najeriyakasa cirewa suka yi amma shi ya cire>>Inji Hadiminsa, Sunday Dare

Duk Labarai
Hadimin shugaban kasa dake bashi shawara akan harkar sadarwa da wayar da kan al'umma, Sunday Dare ya bayyana cewa kamata yayi a yabi shugaban kasar, Bola Ahmad Tinubu akan cire tallafin man fetur. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV inda yace shuwagabannin kasashe da aka yi a baya da yawa sun kasa cirewa sai shine yayi namijin kokari ya cire tallafin man fetur din sannan ya kuma cire tallafin dala. Yace wasu kalilan ne a kasarnan ke samu makudan kudade da tallafin wanda ke sa gwamnati na tafka mummunar asara. Cire tallafin dai ya sanya farashin man fetur ya tashi daga sama da Naira 200 akan kowace lita zuwa sama da Naira 1000 akan kowace lita kuma man fetur ne hanyar da 'yan Najeriya ke amfani da ita wajan samun makamashi a gidajensu da w...
Mun baiwa ‘yan Najeriya Miliyan 24 tallafi>>Inji Gwamnatin tarayya

Mun baiwa ‘yan Najeriya Miliyan 24 tallafi>>Inji Gwamnatin tarayya

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta sanar da baiwa 'yan Najeriya miliyan 24 tallafi daban daban da suka hada dana bashi dana koya sana'a da dai sauransu. Ministan kudi, Wale Edun ne ya bayyana haka a wata ganawa da manema labarai. Ya kara da cewa tallafin da suka bayar sun hada da bangaren Noma, Makamashi, masana'antu kiwon lafiya da dai sauransu. Hakan na zuwane a yayin da 'yan Najeriya ke ta fama da kokawa da matsin tattalin arziki wanda yasa kayan masarufi suka yi tashin gwauron zabi.
Gwamnatin tarayya ta baiwa masu boye da dalar Amurka a gidajensu watanni 9 su fito da ita

Gwamnatin tarayya ta baiwa masu boye da dalar Amurka a gidajensu watanni 9 su fito da ita

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana baiwa masu boye da dalar Amurka a gidaje su fito da ita su kai banki wata tara. Gwamnatin tace idandai kudaden na halas ne ba na sata ba ko zamba cikin aminci ba,babu wani hukunci da za'a wa mutum idan ya fito dasu. Ministan kudi, Wale Edun ne ya bayyana haka inda ya zargi cewa masu boye dalar na taimakawa wajan kara karancinta da tsadarta a Najeriya.
NAFDAC ta yi gargadin daina Amfani da wani turaren Nivea Roll-On saboda illarsa

NAFDAC ta yi gargadin daina Amfani da wani turaren Nivea Roll-On saboda illarsa

Duk Labarai
Hukumar kula da abinci da magunguna ta kasa, NAFDAC ta yo gargadin daina amfani da wani kalar Turaren Nivea Roll-on saboda illar da yake dauke da ita. Kalar turaren da ta ja kunne kan amfani dashi shine Nivea Black & White Invisible Roll-on deodorant saboda yana dauke da wani sinadari da aka haramta amfani dashi a cikin turaruka. Tuni kungiyar Kasashen Turai ta EU ta fitar da sanarwa akan daina amfani da wannan turare inda tace duk ma wadanda suka sayeshi su mayar dashi ga kamfanin. Shi wannan sinadari dai na taba lafiyar haihuwar masu amfani dashi inda yawan amfani dashi na iya kai ga mutum ya kasa haihuwa sannan yana taba lafiyar yaron da ba'a haifa ba idan mace me ciki na amfani dashi sannan kuma yana sanya kaikai a jikin mutum. Shi wannan sinadari dai sunansa 2-(4-tert...
Ji bayanan Bala me rungumar mata, duk da ya tsufa bai tubaba

Ji bayanan Bala me rungumar mata, duk da ya tsufa bai tubaba

Duk Labarai
Shahararren mutuminnan na jihar Bauchi me suna Bala wanda yayi suna a kafafen sada zumunta saboda bayyanar hotunansa yana rungumar mata a jihar Bauchi an yi hira dashi. A hirar ya bayyana cewa, abubuwan da suka faru wanda ake ta yayata hotunansu a yanzu wasunsu sun kai shekaru 20 da faruwa saidai yace na baya-bayannan shekaru 6 ne da faruwarsa. Yace shi baya rayuwa irin ta addini, rayuwa yake irin ta 'yanci da jin dadi. Saidai yace yana son ya auri mace me aiki wadda ko da bayan ya mutu zata kula da 'ya'yansu. Kalli Bidiyon anan
Da Duminsa: Kungiyar Gwamnonin Najeriya tace bata yadda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kara harajin VAT ba

Da Duminsa: Kungiyar Gwamnonin Najeriya tace bata yadda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kara harajin VAT ba

Duk Labarai
Majalisar zartaswa wadda ta hada da kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF ta bayyana cewa tana baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shawarar ya dakata da maganar kara harajin VAT. Kungiyar gwamnonin ta bakin gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde tace tana baiwa shugaban kasar shawarar ya dakata a wayarwa mutane da kai su fahimci abinda kudirin kara dokar VAT din ke nufi. Sannan ya kamata a tuntubi masu ruwa da tsaki a kan harkokin al'umma dan jin shawarar su kan lamarin. Ko da a baya dai, Kungiyar Gwamnonin Arewa da sarakunan yankin sun bayyana cewa basa tare da shugaban kasar kan karin harajin VAT.
Muna nan akan bakarmu na baiwa shugaba Tinubu shawarar ya ci gaba da kara kudin man fetur>>IMF

Muna nan akan bakarmu na baiwa shugaba Tinubu shawarar ya ci gaba da kara kudin man fetur>>IMF

Duk Labarai
Hukumar bayar da lamuni ta Duniya tace bata canja ba, har yanzu tana nan akan bakanta cewa shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur dana dala. Hukumar tace ta hakane 'yan Najeriya zasu samu saukin rayuwa daga matsin tattalin arzikin da suke fama dashi. Karin farashin man fetur dai yasa kayan masarufi sun tashi sama sosai inda talakawa ke cin abinci da kyar. Lamarin ya jawowa gwamnati tofin Allah tsine tsakanin Talakawa. Hakanan an sha zargin hukumar ta IMF da bankin Duniya da bayar da shawarwarin dake jefa kasashe da yawa cikin wahalar rayuwa.
Kalli Bidiyon matasan Kaduna suna murnar Nepa ta dawo

Kalli Bidiyon matasan Kaduna suna murnar Nepa ta dawo

Duk Labarai
Bayan dawowar wutar lantarki a jihar Kaduna, Matasa sun hau titi inda suka rika wakar cewa Nepa ta dawo. Bidiyon hakan ya watsu sosai a kafafen sada zumunta: https://www.youtube.com/watch?v=caZd7slnLhs Wasu sun bayyana abin da Nishadi inda wasu kuma suka bayyana takaici da cewa 'yan Kaduna sun bayar da kunya da wannan murna. https://twitter.com/Abdool85/status/1851757048075051304?t=oy8qaPAfPahhKBfpfc46Tg&s=19 Kusan sati biyu aka kwashe ana fama da rashin wuta a yankin Arewa kamin a samu ta dawo.