2027: Hadakar Atiku da El-Rufai da Obi ba za ta iya kayar da APC ba — Shekarau
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa babu wata haɗakar ‘yan siyasa da za ta iya sauke Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.
Matsayar Shekarau na zuwa ne kasa da sa’o’i 48 bayan wasu manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, suka soki matsayar Gwamnatin Tarayya game da rikicin siyasa a Jihar Ribas a wani taron manema labarai da suka gudanar a Abuja.
A wata sanarwa da Dr. Sule Yau ya fitar a madadin Shekarau, ya jaddada cewa, sabanin abin da wasu ke hasashe, wannan haɗaka kawai wata tarayya ce ta masu niyyar tsayawa takarar shugaban ƙasa ko mataimakin shugaban ƙasa, ku...








