
Rahotanni sun bayyana cewa, wasu mata 4 sun fito suma sun bayyana cewa malamin jami’ar MAUN dake Kano da aka lakadawa na jaki saboda zargin neman matar aure suna ya nemesu.
Matan sun bayyana hakane ga shahararren mawallafin labarai na kafafen sada zumunta, watau, Abis Fulani.
Saidai Abis Fulani yace ba zai wallafa zargin da wadannan matan suka kai masa ba inda yace baya son shafinsa ya zama wajan tone-tonen Asirin mutane.
Yace matan su kaiwa hukumar makarantarsu korafi.
Sannan ya bayyana cewa jami’ar MAUN dake Kano ta fitar da bayanai cewa malamin da aka lakadawa dukan ya daina mata aiki dama aikin wucin gadi ne ya mata.