Monday, February 16
Shadow

Duk Labarai

Dama can ba cancanta aka bi ba, an bashi aikinne saboda yana kama da turawa, ya iya irin turancin turawa>>Jafar-Jafar kan ajiye aikin me magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale

Dama can ba cancanta aka bi ba, an bashi aikinne saboda yana kama da turawa, ya iya irin turancin turawa>>Jafar-Jafar kan ajiye aikin me magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale

Duk Labarai
Dan jarida daga Arewa, Jafar-Jafar ya bayyana cewa, dama can ba cancanta aka bi ba wajan baiwa Ajuri Ngelale aikin me magana da yawun shugaban kasa ba. Yace kawai dan yana kama da turawane kuma ya iya turanci irin na turawa shiyasa aka bashi aikin. Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta. Saidai wasu sun yadda da abinda yake amma wasu sunce hassada ce ke damun Jafa-Jafar.
Da Duminsa:Kakakin Shugaban Kasa, Ajuri Ngelale ya yi murabus daga mukaminsa

Da Duminsa:Kakakin Shugaban Kasa, Ajuri Ngelale ya yi murabus daga mukaminsa

Duk Labarai
Kakakin Shugaban kasa,Ajuri Ngelale ya bayyana ajiye mukakinsa na magana da yawun shugaban kasa da kuma zama jakadan shugaban kasar a bangaren dumamar yanayi. A sanarwar da fadar shugaban kasan ta fitar tace Ajuri ya mikawa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa,Femi Gbajabiamila takardar ajiye aiki. Yace dalilinsa shine yana son mayar da hankali wajan kula da lafiyar daya daga cikin iyalansa. Ya bayyana cewa, hutune zai tafi amma wanda babu ranar dawowa sannan kuma wannan mataki ba dan yana so ya daukeshi ba. Yace sai da ya shafe kwanaki kana shawara da danginsa akan lamarin.
Naga yanda kasar China take ta burgeni,Zan mayar da Najeriya kamar kasar China>>Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu

Naga yanda kasar China take ta burgeni,Zan mayar da Najeriya kamar kasar China>>Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, zai mayar da Najeriya kamar kasar China. Shugaban ya bayyana hakane bayan ziyarar da ya kai kasar ta China inda ya gana da shugaban kasar, Xi Jinping. Ya bayyana hakane a taron da yayi da 'yan Najeriya mazauna kasar ta China. Shugaban yace, Najeriya na bukatar da'a da jajircewa irin ta kasar China inda yace a hakane zata cimma burinta kuma a rika girmamata a idon Duniya.
Ba zan iya soyayya da namijin da ba zai wuce mintuna 40 yana jima’i daji ba>>Inji Wannan ‘yar Fim din

Ba zan iya soyayya da namijin da ba zai wuce mintuna 40 yana jima’i daji ba>>Inji Wannan ‘yar Fim din

Duk Labarai
Shahararriyar fim daga kasar Ghana, Efia Odo ta bayyana cewa ba zata iya yin soyayya da namijin da ba zai iya yin jima'i da ita ba na fiye da tsawon mintuna 40 ba. Ta bayyana hakane a cikin wani shiri da take gudanarwa na rediyon yanar gizonta da ake cewa Podcast. Tace hakanan ba zata iya yin soyayya da namijin da ya wuce shekaru 30 ba amma yana zaune a gidan iyayensa ba. Hakanan ba zata iya kasancewa da namijin da bashi da mota ba. Wannan magana tata ta jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta sosai.
Buhari Ya Aika Da Tawaga Zuwa Katsina Domin Yin Ta’aziyyar Dada ‘Yar’Adau A Madadinsa

Buhari Ya Aika Da Tawaga Zuwa Katsina Domin Yin Ta’aziyyar Dada ‘Yar’Adau A Madadinsa

Duk Labarai
Tsohon shugaban kasar Najeriya Muhammad Buhari, ya aika da tawaga mai ƙarfi karkashin jagorancin tsohon ministan sufurin jiragen sama Sen. Hadi Sirika, domin gabatar da ta'aziyar Hajia Dada, mahaifiyar tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar'adua a garin Katsina. Tawagar ta kunshi tsohon ministan Shari'a Abubakar Malami SAN, da Sanata Hadi Sirika da kuma shugaban jam'iyyar APC na jihar Katsina Hon. Sani Aliyu Daura da wasu tsofaffin muƙarraban gwamnatinsa. A cewar, Hadi Sirika, Buhari ya kaɗu a lokacin da sakon rasuwar Haj. Dada ya riske shi a kasar Ingila. Daga Comr Nura Siniya
SHEIK DAHIRU BAUCHI: Malamin Da Ya Fi Kowa Yawan Zuri’ar Mahaddata Alkur’ani A Duniya

SHEIK DAHIRU BAUCHI: Malamin Da Ya Fi Kowa Yawan Zuri’ar Mahaddata Alkur’ani A Duniya

Duk Labarai
Malamin Da Ya Fi Kowa Yawan Zuri’ar Mahaddata Alkur’ani A Duniya Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya kafa tarihin zama mutumin da ya fi kowa yawan zuri’ar da ta haddace Alkur’ani a tarihin duniya. Alkaluma sun nuna cewa Shehin Malamin, wanda a kwanan nan ya cika shekara dari a duniya — ranar 2 ga watan Almuharram 1444 Hijiriyya — yana da ’ya’ya da jikoki da ma tattaba-kunne kusan 300 da suka haddace Alkur’ani. A cewar kundin tattara bayanai na Cholan Book Of World Records, wadanda suka karrama malamin da lambar yabo, Sheikh Dahiru Bauchi shi ne mutum na farko da ya taba samun irin wannan baiwar. Bayanai sun nuna mashahurin malamain yana da ’ya’ya 95 da jikoki 406 da tattaba-kunne 100. Daga cikin wannan adadin, ’ya’yansa 77 da jikoki 199 da ku...
WATA SABUWA: Masu Shaidar Ɗan Ƙasa Ta NIN Ne Kaɗai Za Su Samu Shinkafa Mai Rangwamen Farashi Ta Gwamnatin Tarayya

WATA SABUWA: Masu Shaidar Ɗan Ƙasa Ta NIN Ne Kaɗai Za Su Samu Shinkafa Mai Rangwamen Farashi Ta Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Masu Shaidar Ɗan Ƙasa Ta NIN Ne Kaɗai Za Su Samu Shinkafa Mai Rangwamen Farashi Ta Gwamnatin Tarayya Gwamnatin Najeriya ta ce ma’aikatan gwamnati waɗanda suke da lambar ɗan ƙasa ta NIN ne za a bai wa damar sayen shinkafar da gwamnatin za ta sayar a farashi mai rahusa. Ministan Noma, Abubakar Kyari ne ya sanar da hakan, inda ya ce hakan zai taimaka wajen rage ci da zuci da kuma sayen abincin a kasuwa da ma rage tsadar abincin a kasuwannin Najeriya. Ministan Noma Abubakar Kyari, ya ce buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50 za a sayar a farashin Naira 40,000 a cikin shirin gwamnatin na rage raɗaɗin tsadar kayan masarufi. Menene ra'ayinku?
DA ƊUMI-ƊUMI: Ƴáɲ Biɲdiĝa Na Cigaba Da Rąɲtayawa A Na Káre Daga Maboyar Su Tun Bayaɲ Zuwaɲ Ministan Tsaro Jihar Sokoto Bisa Umarnin Shugaban Kasa Tinubu

DA ƊUMI-ƊUMI: Ƴáɲ Biɲdiĝa Na Cigaba Da Rąɲtayawa A Na Káre Daga Maboyar Su Tun Bayaɲ Zuwaɲ Ministan Tsaro Jihar Sokoto Bisa Umarnin Shugaban Kasa Tinubu

Duk Labarai
Ƴáɲ Biɲdiĝa Na Cigaba Da Rąɲtayawa A Na Káre Daga Maboyar Su Tun Bayaɲ Zuwaɲ Ministan Tsaro Jihar Sokoto Bisa Umarnin Shugaban Kasa Tinubu Biyo bayan amsa umarnin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ƙaramin ministan tsaro Bello Matawalle yayi ya tare Jihar Sokoto tare da shugabannin rundunonin tsaro, ƴan bíɲdíĝá suna cigaba da ɗanɗana kuɗarsu a hannun Sojoji Nâjeriya. A rahotannin da suke fitowa na nuna cewa, ƴan biɲdíĝâr masu tarin yawa suna cigaba da rantayawa a na kare suna haurawa ƙasashe maƙota domin nemaɲ tsira da rayúwársu. Wane fata zaku yiwa sojojin Nąjeriya?