Trump ya ce ba shi da wani zaɓi illa korar dubun dubatar baƙin haure
Zaɓaɓɓen Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba shi da wani zaɓi "da ya wuce" korar dubun dubatar baƙin haure da ba su da izinin zama a ƙasar.
Cikin wata tattaunawa da NBC ranar Alhamis, shugaban ya ce: "Ba magaanr abin da za mu samu ko rasawa ba ce. Ba haka ba ne - ba mu da wani zaɓi ne. Idan ana kashe mutane, jagororin 'yanƙwaya na lalata ƙasashe, to yanzu za su koma ƙasashensu saboda ba za su zauna mana a nan ba."
Ko da gwamnatin ta yi nasarar koro baƙin a hukumance, to za ta sha fama wajen yadda za ta aiwatar da hakan. Ƙwararru na ganin hakan zai laƙume biliyoyin dala kafin a iya mayar da mutum miliyan ɗaya gida.
A shekarar 2021 aka dakatar da shirin kai samame kan wuraren ayyukan baƙin, wanda gwamnatin Trump ta aiwatar.
Adadin mutanen da ake kamawa a cikin Amurka tare da ma...








