Bidiyon yanda aka sa wani mace da namiji suka saka wando daya bayan kamasu suna lalata ya karade shafukan sada zumunta.
Rahotanni sunce lamarin ya farune a Garin Duala na kasar kamaru.
https://www.youtube.com/watch?v=8WU_N01deh4
An ga mutane na binsu suna daukarsu hoto da shewa.
Jihohin Kudu maso gabas, watau jihohin Inyamurai ne suka fi biyan masu garkuwa da mutane kudi da yawa dan karbo 'yan iwansu da aka yi garkuwa dasu.
A gaba daya Najeriya, an biya masu garkuwa da mutane jimullar Naira Biliyan 1.048 a matsayin kudin fansa inda jihohin kudu maso gabas na inyamurai suka biya jimullar Naira Miliyan dari hudu da sha tara 419.2 Million.
Wannan shine kaso 40 na jimullar kudij fansar da aka biya a Najeriya.
A jihar Anambra ne aka fi biyan kudin fansar inda aka biya masu garkuwa da mutane jimullar Naira miliyan 350.2 a jihar.
Mutanen jihar Imo sun biya masu garkuwa da mutanen Naira Miliyan 39.
Sai jihar Abia data biya Jimullar Naira Miliyan 25 ga masu garkuwa da mutanen, mutanen jihar Enugu sun biya Naira Miliyan 4 ne ga masu garkuwa da mutanen dan k...
Wutar daji a birnin Los Angeles na kasar Amurka ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 11.
Hukumomin lafiya na birnin Los Angeles sun ce 5 daga cikin anda suka mutu sun mutu ne a yankin Palisades sai kuma guda 6 sun mutu ne a yankin Eaton.
Har yanzu dai mahukunta basu san dalilin tashin wannan gobara ba.
Hakanan an samu karancin ruwan kashe gobarar kuma ma'aikatan kashe gobarar ma sun yi karanci inda makwauciyar kasar Amurka, Mexico ta aike da taimakon masu kashe gobara zuwa birnin na Los Angeles.
Ana dai zargin mahukuntan birnin na Los Angeles, Musamman Gwamnan California, Gavin Newsom da Magajiyar garin da sakaci wajan rashin yin tanadin yanayi irin wannan inda ake zargin basu dauki matakin adana ruwan sama da aka samu me yawa ba dan kashe gobara irin wannan ba.
Hakanan an zargi...
Wata mtashiya ta dauki hankula a kafafen sada zumunta bayan da aka ga tana kokawa a dakin otal saboda abinda abokin lalatarta ya mata.
Tace sun yi alkawarin zai bata dubu goma sha biyar amma ya kare da bata Naira dubu goma bayan ta biya masa bukatarsa ta hanyar tsotsar masa mazakutarsa.
Tace wannan damfara ne kua dolene ya biyata sauran kudinta.
https://www.youtube.com/watch?v=Q1NMdxaj3Ww
Bidiyon nata ya dauki hankula sosai a kafafe sada zumunta inda akaita bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai.
Kwamitin Majalisar dattijai dake saka ido kan yanda ake kashe kudaden gwamnati ya nemi ministan kudi, Wale Edun yayi bayani kan yanda aka kashe kudin tallafin man fetur da aka cire.
Saidai Wale yace wannan magana ta sirri ce, dan haka ne kwamitin suka kori 'yan majalisa daga zaman dan Wale ya musu bayani.
Wannan magana ta taso ne bayan da sanata Senator Abdul Ningi dan PDP daga jihar Bauchi ya bukaci hakan.
Shugaban kwamitin, Senator Olamilekan Adeola ya nemi 'yan jarida su fita daga zaman dan a samu a yi maganar yanda aka kashe kudin tallafin man fetur da aka cire.
Gwamnatin tarayya dai tace ta cire tallafin man fetur ne dan amfani da kudaden wajan yin ayyukan raya kasa.
Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bukaci cewa ya kamata a hukunta Alkalin babbar kotu tarayya da yayi hukuncin cewa sake nada me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi II a matsayin sarki baya kan ka'ida.
El-Rufai wanda abokin Sarki Sanusi II ne ya bayyana hakane a ta shafinsa na sada zumunta inda yake taya Sanusi II murnar tabbatar dashi a matsayin sarkin Kano da kotun daukaka kara tayi.
A baya dai Kotun tarayya ta yi hukuncin cewa, sake nada Sarki Sanusi II baya kan doka amma a yanzu kotun daukaka kara ta soke wancan hukunci.
El-Rufai ya kara da cewa, babbar kotun tarayya bata da hurumin shiga maganar masarauta wadda bata cikin garin Abuja.
An ga dai yanda masoya sarki Sanusi II suka barke da murna bayan da aka tabbatar dashi a matsayin sarkin Kanon.
Karamar ministar kwadago, Nkeiruka Onyejeocha ta bayyana sanda gwammati zata sake yiwa ma'aikata karin albashi.
Ta bayyana hakane ranar Alhamis a ziyarar da ta kai jihar Abia.
Tace a baya sai bayan shekaru 5 ne ake karawa ma'aikata Albashi amma a yanzu, za'a rika yin karin albashinne duk bayan shekaru 3.
Tace nan da kasa da shekaru 2 za'a sake yiwa ma'aikatan karin Albashi.
Hukumar kididdiga ta kasa, NBS ta bayyana cewa zata saka karuwanci a matsayin daya daga cikin alkaluman da take amfani dasu wajan tantance karfin tattalin arzikin Najeriya
Hakanan bayan karuwancin, za'a kuma saka harkar kwaya a cikin hanyoyin da ake samarwa gwamnati kudi da kara karfin tattalin arziki.
Shugaban hukumar, Dr. Baba Madu ne ya tabbatar da hakan i da yace akwai kasashen da kwaya ce babbar hanyar samun kudin shigarsu sannan akwai wanda kuma ke karuwanci kuma suna samun kudi fiye ma da masu aikin yi.
Yace duka wadannan za'a sakasu a cikin masu taimakawa karfin tattalin arzikin Najeriya.
Wata mata me zaman kanta a jihar Adama ta kashe me sayar da giya bayan da rikici ya barke a tsakaninsu akan canjin Naira 200.
Matar me suna Riyanatu Musa ta kashe Yohanna Musa ne ta hanyar caka masa wuka a kirji.
Hukumar 'yansandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace wadda ake zargi ta amsa laifin da ake zarginta dashi.
Tace a lokacin data kashe Yohanna Musa bata cikin maye inda tace amma ta yi nadamar abinda ta aikata.
Kakakin 'yansandan jihar, SP Suleiman Nguroje yace kwamishinan 'yansandan jihar, Morris Dankombo ya bayar da umarnin yin bincike kan lamarin.
Kotun daukaka kara ta Kano a yau Juma’a, ta yi watsi da umarnin babbar kotun da ta soke nadin Sanusi Lamido Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 16.
Wani kwamitin mutane uku na kotun daukaka kara, a hukuncin da ta yanke, karkashin jagorancin mai shari’a Mohammed Mustapha, ya yi watsi da hukuncin da kotun tarayya ta yanke a ranar 20 ga watan Yuni, 2024, ƙarƙashin mai shari’a Abubakar Liman, na babbar kotun tarayya, wanda ya soke dokar masarautar Kano ta 2024 da ta sake nada Sanusi.
A cewar kotun daukaka kara, Mai shari’a Liman ya yi watsi da hurumin soke matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka bisa dokar majalisar masarautu ta 2024.
Ta kara da cewa, karar da wani basarake a jihar, Alhaji Aminu Babba Dan Agundi ya shigar, wanda alkalin babbar kotun ya dogara da ita wajen bayar da wanna...