Sunday, July 5
Shadow

Duk Labarai

Zan kammala gina Titin Jirgin kasan daya tashi daga Fatakwal zuwa Maiduguri kamin in sauka daga mulki>>Shugaba Tinubu

Zan kammala gina Titin Jirgin kasan daya tashi daga Fatakwal zuwa Maiduguri kamin in sauka daga mulki>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, zai kammala ginin jirgin kasan daya tashi daga Fatakwal, Jihar Rivers zuwa Birnin Maiduguri na jihar Borno kamin ya kammala wa'adin mulkinsa. Shugaban ya bayyana hakane a yayin ziyarar da ya kai jihar Enugu yayin ganawa da dattawa daga yankin kudu maso gabas. Kakakin shugaban kasar, Mr. Bayo Onanuga ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar inda yace kuma shugaban kasar yayi Alwashin samar da wata tashar makamashi a jihar Anambra.
Allah Sarki: Mata 3 da aka kama da zargin safarar kwàyà a kasar Saudiyya, an sakesu bayan an gano basu da laifi

Allah Sarki: Mata 3 da aka kama da zargin safarar kwàyà a kasar Saudiyya, an sakesu bayan an gano basu da laifi

Duk Labarai
Mata 3 'yan Najeriya da da aka kama a kasar Saudiyya aka tsare, tsawon watanni 10 bisa zargin safarar miyagun kwayoyi an sakesu bayan an gano basu da laifi. Kakakin Ministan harkokin waje, Kimiebi Ebienfa ya tabbatar da hakan. A watan Maris na shekarar 2024 ne aka kama matan a filin jirgin sama na Prince Muhammad Bin Abdulaziz dake Madina. Matan sune, Hadiza Abba, Fatima Umate Malah, da Fatima Kannai Gamboi. An kama su ne biyo bayan kama wasu 'yan Najeriya biyu da hodar Iblis. An kamasu ne bisa zargin cewa sun taimakawa masu safarar miyagun kwayoyin. Lamarin ya dauki hankula sosai a kasashen Najeriya da Saudi Arabian inda Najeriya ta shiga tsakani har aka sakesu. Bayan sakinsu, an mikasu ga ofishin jakadancin Najeriya dake kasar ta Saudiyya inda jakadan Najeriya a kasa...
MASHA ALLAH: Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Kiyawa Ya Ce Sakon Neman Shamsiyya Da Aure Da Nake Yi Ya Riske Su, Amma Sai Sun Gudanar Da Kwakkwarar Bincike Gudun Kada A Hada Tawagar Da Za Ta Fi Karfinsu Nan Gaba, Inji Dogo Yaro Crypto Yola

MASHA ALLAH: Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Kiyawa Ya Ce Sakon Neman Shamsiyya Da Aure Da Nake Yi Ya Riske Su, Amma Sai Sun Gudanar Da Kwakkwarar Bincike Gudun Kada A Hada Tawagar Da Za Ta Fi Karfinsu Nan Gaba, Inji Dogo Yaro Crypto Yola

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Kakakin 'Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Kiyawa Ya Ce Sakon Neman Shamsiyya Da Aure Da Nake Yi Ya Riske Su, Amma Sai Sun Gudanar Da Kwakkwarar Bincike Gudun Kada A Hada Tawagar Da Za Ta Fi Karfinsu Nan Gaba, Inji Dogo Yaro Crypto Yola A baya dai, Dogo Yaro Crypto Yola ya dauki hankula bayan da ya fito da gaske yace yana son Shamsiyya duk da halin data tsinci kanta. Da yawa sun yi mamaki da wannan karfin hali nashi.
An kaiwa Tawagar Hadimar Gwamnan Kaduna hari

An kaiwa Tawagar Hadimar Gwamnan Kaduna hari

Duk Labarai
Hadimar gwamnan jihar Kaduna dake bashi shawara akan harkokin siyasa, Hon. Rachael Averik ta tsallake rijiya da baya a yunkurin kisheta da aka yi. An kaiwa tawagar Hon. Rachael Averik harin kwantan baunane ranar Alhamis, 2 ga watan Janairu. Harin ya farune a tsakanin kauyukan Tsauni Majidadi da Gani dake karamar hukumar Sanga ta jihar. A ranar tana kan hanyar zuwa Gwantu ne abin ya faru. A ranar taje gaisuwane sannan ta kaddamar da Asibitin da Alhaji Muhammad Umar Numbu ya gina a masarautar Arak. Jami'an tsaron dake tare da ita sun budewa maharan wuta inda anan aka jikkata direbanta da Dansanda daya. Jami'an tsaro a jihar sun fara bincike kan lamarin. Gwamnatin jihar ta yi Allah wadai da harin.
Zan Yi Tattaki Daga Jihar Gombe Zuwa Abuja Domin Kaiwa Maulana Prof. Ibrahim Maqari Ziyara, Inji Rumanatu Sa’ad Abubakar

Zan Yi Tattaki Daga Jihar Gombe Zuwa Abuja Domin Kaiwa Maulana Prof. Ibrahim Maqari Ziyara, Inji Rumanatu Sa’ad Abubakar

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Zan Yi Tattaki Daga Jihar Gombe Zuwa Abuja Domin Kaiwa Maulana Prof. Ibrahim Maqari Ziyara, Inji Rumanatu Sa'ad Abubakar Wace fata za ku yi mata?
Bayyana Kyautar Motar Da Yara ‘Ýan Maťàñ Nan Śuke Yì, Ya Fi Illa Fiye Da Àbìnda Suke Źuwa Ýi Ake Ba Šu Motar

Bayyana Kyautar Motar Da Yara ‘Ýan Maťàñ Nan Śuke Yì, Ya Fi Illa Fiye Da Àbìnda Suke Źuwa Ýi Ake Ba Šu Motar

Duk Labarai
Daga Jamila Ibrahim Ni Wallahi yaran nan da ake bawa mota fitowa da suke yi suna nunawa ya fi illa akan abinda suke zuwa ýi ake ba su. Yanzu sun yi influencing yara kanana na ťìķțok har ya kai ga burin yarinya kawai ta yi ìşķançì a ba ta kudi, yara sun fara fandarewa. In an basu suyi hakuri su daina zuwa suna posting don yadawa duniya. Ku kuma 'yan mata da kuke kallon wadanda ake bawa gida da mota as role model har suke burge ku ku sani ba haka kawai ake ba su kudin ba, wani abun ya wuce kudin da saurayi zai bawa budurwa sabida soyayya ko sabida ya yi źìñà da ita, yawanci kudin ķùñģiya ce, bayan wasu shekaru za a a nemi wadanan dukiyar a rasa ka zama abun tausayi. Zan iya misalai da 'yan fim dayawa wadnda ma suka tare kasar waje suka yi suna, suka yi kudi amma karshen su yan...
Wata cuta data bullo ta yi sanadiyyar kwantar da mutane dubu biyar a Asibiti

Wata cuta data bullo ta yi sanadiyyar kwantar da mutane dubu biyar a Asibiti

Duk Labarai
Mutane sama da dubu biyar ne aka kwantar a Asibiti a kasar Ingila biyo bayan bullar wata cutar mura. Mutanen sun kamu da cutar ne a makon karshe na shekarar 2025 inda gadaje suka yi kadan a Asibiti sai da aka samar sa sabbin gadaje na gaggawa 1,300. An dai bayyana sunan cutar da norovirus and Respiratory Syncytial Virus (RSV) kuma yawan masu kamuwa da ita din sun fara karuwane daga ranar Kirsimeti. Daraktan hukumar kula da lafiya ta kasar, Julian Redhead ya bayyana cewa, abin damuwa ne ganin cewa mutane 5000 ake kwantara kullun a Asibiti sanadiyyar cutar. Yace kuma nan gaba lamarin zai kara munana saboda ana tsammanin sanyi ya karu. Yayi kira ga mutane su dauki matakan baiwa kansu kariya.
Gwamnatin Nasarawa ta ɓullo da shirin saka wa motocin sufuri sabon fenti

Gwamnatin Nasarawa ta ɓullo da shirin saka wa motocin sufuri sabon fenti

Duk Labarai
Hukumar karɓar haraji ta jihar Nasarawa ta ɓullo da shirin saka wa motocin sufuri sabon fenti da nufin inganta harkokin tsaro. Hukuma ta ce za a yi hakan ne kuma don ƙara yawan kuɗaɗen shiga da ake samu. Yanzu dai za a sauya wa motocin haya da keke-NAPEP launi domin a bambance tsakanin ababen hawa na haya da kuma waɗanda ba na haya ba. Launin ja ko tsanwa. Hon Moses Abeh wanda ya wakilci gwamnatin jihar a taron kaddamar da tsarin, ya ce an ɗauki aniyar yin tsarin ne domin samar da lambobin tsaro da kume fentin ga direbobi domin kare kai daga ɓata-gari da ake kira 'One Chance'. "Lambar tsaron zai kunshi bayanan direba da suka haɗa da wajen da mutum ya fito da kuma inda yake zama," in ji Moses. Ya kuma ce dole sai an san ƙungiya da direba ke ciki domin kaucewa sajewa da ɓata-g...