
Tauraruwar Tiktok, Rahama Saidu me babban Shago ta bayyana cewa bai kamata malamai su rika katsalandan a rayuwar musamman mata ba.
Tace idan mace ta aikata abin Alheri ba ruwan mutane da ina ta samo kudinta, kamat yayi kawai su yaba mata.
Ta bayyana hakane a Live da ta yi inda take bayyana bacin ranta kan irin maganganun da aka gayawa Momi Gombe bayan data gina Masallaci.
Rahama tace bai kamata ba, dan kuwa ko da mutum na aikata abinda bai dace ba, yana rokon Allah ya yafe masa.