Majalisar tarayya ta fara tantance sabbin ministoci
Majalisar tarayya ta dakatar da duk wani aikin da take a ranar Laraba inda ta fara tantance sabbin ministocin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya mika mata sunayensu.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dai ya aikewa da majalisar sunayen sabbin ministocin da ya nada bayan da yawa majalisarsa ta zartaswa garanbawul, inda ya hade wasu ma'aikatun sannan ya kirkiri wasu ya kuma kori wasu ministoci sannan ya nada wasu sabbi.
Senator Opeyemi Bamidele ne ya gabatar da fara tantance ministocin sannan sanata Abba Moro ya goya masa baya.
Daga nan ne sai aka karanto sunayen sabbin ministocin da za'a tantance wanda ciki akwai Dr. Nentewa Yilwatda a matsayin ministan jin kai da rage talauci, Sai kuma Muhammad Maigari Dingyadi a matsayin ministan ayyuka da kwadago, Sai kuma Bianca Odinaka Odume...








