Friday, December 13
Shadow

labaran tinubu ayau

Shugaba Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima basa Najeriya, Saidai Fadar shugaban kasa tace Shugabancin Najeriya ba zai samu Tangarda ba

Shugaba Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima basa Najeriya, Saidai Fadar shugaban kasa tace Shugabancin Najeriya ba zai samu Tangarda ba

labaran tinubu ayau
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa,Kashim Shettima basa Najeriya. A yayin da shugaba Tinubu ya tafi kasar Ingila inda daga can ya wuce Faransa. Shi kuwa mataimakinsa, Kashim Shettima ya tafi kasar Sweden ne. Babban me baiwa shugaban kasa shawara kan yada labarai Bayo Onanuga ya bayyana cewa hakan ba zai kawo tangarda ga shugabancin kasarnan ba. Yace a yanzu da ake da kafafen sadarwa na Zamani duk inda shuwagabannin suke suna gudanar da ayyukansu yanda ya kamata. Yace shugaba Tinubu ya tafi hutun sati 2 ne yayin da shi kuma Mataimakinsa,Kashim Shettima ya tafi kasar Sweden wajan gudanar wa da Najeriya aiki.
Kada wanda ya kara kiran shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da su an banza na T-Pain>>Fadar shugaban kasa ta yi gargadi

Kada wanda ya kara kiran shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu da su an banza na T-Pain>>Fadar shugaban kasa ta yi gargadi

labaran tinubu ayau
Fadar shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu ta yi gargadin kada wanda ya kara kiran shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da sunan banza na T-Pain. Sunan T-Pain dai a kafar sada zumunta aka sakawa shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu shi dan nuna wahalar da mutane ke ciki a karkashin Gwamnatinsa wanda sunan wani mawakin kasar Amurka ne. Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar na daga cikin wadanda suka rika kiran Tinubu da wannan suna. Saidai duk da gargadin da fadar shugaban kasar ta yi,da yawa sun ce ba zasu daina fadar wannan suna ba.
Ji sabon sunan tsokana da ake kiran shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu dashi wanda har Atiku Abubakar ma ya kirashi da sunan

Ji sabon sunan tsokana da ake kiran shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu dashi wanda har Atiku Abubakar ma ya kirashi da sunan

labaran tinubu ayau
A yayin da masu amfani da shafukan sada zumunta suka radawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu sunan T-pain. Sunan dai ya watsu sosai inda har tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar shima ya kirashi da sunan. https://twitter.com/atiku/status/1844369477690970492?t=yfNSmncXV6QvnpVcoUtYJw&s=19 T-pain dai shahararren mawaki ne a kasar Amurka amma 'yan Najeriya sun lakabawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shi. A sakon da ya fitar kan cire tallafin man fetur, Atiku Yace T-pain watau Tinubu be damu da wahalar da 'yan Najeriya ke ciki ba.
Gwamnatin Tinubu ta ranto Dala Biliyan 6.45 daga bankin Duniya

Gwamnatin Tinubu ta ranto Dala Biliyan 6.45 daga bankin Duniya

labaran tinubu ayau
A cikin watanni 16 da suka gabata, Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta ranto jimullar kudin da suka kai Dala Biliyan 6.45 daga bankin Duniya. Bayanai sun nuna an ranto kudadenne dan dan gudanar da ayyuka daban-daban a fadin kasarnan. Kuma ana tsammanin nan gaba gwamnatin zata sake ranto wasu kudaden. Da yawan 'yan Najeriya dai na ganin basukan da gwamnati ke ciyowa basu da wani tasiri sosai musamman ganin yanda gwamnatocin baya ke ciwo bashi amma babu abinda ke canjawa. Lamarin ciwo bashi dai ya zama kamar gasa tsakanin gwamnatocin Najeriya inda duk gwamnatin data hau mulki sai ta ciwo bashi a wasu lokutan ma wanda yafi na gwamnatin data gabata. Abin jira a gani dai shine ko wannan gwamnati zata sha banban da sauran gwamnatocin?
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai sallami ministoci 11 da sauran manyan ma’aikata

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai sallami ministoci 11 da sauran manyan ma’aikata

labaran tinubu ayau
Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai sallami Ministoci 11 daga majalisarsa ta zartaswa. Me baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai,Bayo Onanuga ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar. Saidai bai fadi zuwa yaushene Shugaban kasar zai dauki wannan mataki ba. Amma wata majiya a fadar shugaban kasar tace a cikin satin da mukene ake tsammanin za'a fitar da sanarwar garambawul din. Matsin rayuwa na daya daga cikin abinda 'yan Najeriya ke kuka dashi a gwamnatin Bola Ahmad Tinubu wanda ke da alaka da yanayin mulkin da yake gudanarwa.
Matar Shugaba Tinubu Ta Bada Gudummuwar Naira Milyan 500 Ga Al’ummar Maiduguri

Matar Shugaba Tinubu Ta Bada Gudummuwar Naira Milyan 500 Ga Al’ummar Maiduguri

labaran tinubu ayau, Siyasa
Uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayar da gudunmuwar Naira miliyan 500 ga gwamnatin jihar Borno ta hanyar shirinta na Renewed Hope Initiative domin tallafawa wadanda bala'in ambaliyar ruwa ya rutsa da su a Maiduguri. Uwargidan mataimakin shugaban kasa Hajiya Nana Shettima ta wakilci uwargidan mataimakin shugaban kasa kuma mataimakiyar shugaban kungiyar Renewed Hope Initiative, Uwargidan shugaban kasar ta jajantawa al'ummar Borno bisa bala'in da ya yi sanadiyar salwantar rayuka da dukiyoyi da rayuwa ¹. A yayin bayar da gudummawar a gidan gwamnati, Hajiya Nana Shettima ta yaba wa Gwamna Farfesa Babagana Umara Zullum bisa gaggauwa da gaggawar da ya dauka kan bala’in da kuma tallafin da aka ba wa wadanda abin ya shafa. Gwamnan ya nuna godiya ga Sanata Oluremi Tinubu bi...
Tinubu zai dawo Najeriya bayan ziyarar da ya kai kasashen China, UAE da Ingila

Tinubu zai dawo Najeriya bayan ziyarar da ya kai kasashen China, UAE da Ingila

labaran tinubu ayau
A yau,Lahadi ne shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu zai dawo gida Najeriya bayan ziyarar da ya kai kasashen China, UAE da Ingila. Ranar 29 ga watan Augusta ne shugaban ya bar Abuja zuwa Beijing inda ya dan tsahirta a Dubai, UAE. Ya isa Beijing ranar 1 ga watan Satumba. Ranar 2 ga watan Satumba ne dai shugaban ya fara ziyarar a aikace inda ya gana da shugaban kasar China Xi Jinping sannan aka masa fareti da harbin bindiga na ban girma. A taron, Najeriya da kasar China sun sakawa wasu yarjejeniyoyi guda 5 na ci gaban kasashen biyu hannu kamar yanda kakakin shugaban kasar, Bayo Onanuga ya bayyanar. Hakanan shugaban kasar na China Xi Jinping da matarsa, Peng Liyuan sun shiryawa shugaba Tinubu wata liyafar dare wadda aka nuna al'adun kasar Chinan. Daga nan Shugaba Tinubu ya tafi z...
Ashe Shugaba Tinubu korar me magana da yawunsa Ajuri Ngelale yayi, ji bayani dalla-dalla

Ashe Shugaba Tinubu korar me magana da yawunsa Ajuri Ngelale yayi, ji bayani dalla-dalla

labaran tinubu ayau
Rahotanni na ta kara fitowa kan dalilin ajiye aikin me magana da yawun shugaban kasa,Ajuri Ngelale. A ranar Asabar ne dai Ajuri ya ajiye aikin nasa inda ya bayyana dalilan rashin lafiyar danginsa a matsayin abinda yasa ya ajiye aikin. Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa fada ne ko rashin jituwa tsakanin Ajuri da wasu na kusa da shugaban kasar yasa ya ajiye aikin. Hakanan a wani sabon Rahoto na kafar FIJ, suma sun bayyana cewa, rashin jituwa ne tsakanin Ajuri da dayan kakakin shugaban Bayo Onanuga inda kowa kw ganin shine babba a tsakanin su. Majiyar tace an yi yunkurij sasantasu amma Ajuri yaki yadda a yi musu sulhu wanda haka tasa daga baya aka koreshi daga aiki. Saidai bayan da aka koreshi daga aikin,ya yi rokon a taimaka masa yayi ritaya da kansa dan idan akace an kore...
Ba’a taba shugaban kwarai mutumin arziki iin Tinubu ba>>Kashim Shettima

Ba’a taba shugaban kwarai mutumin arziki iin Tinubu ba>>Kashim Shettima

labaran tinubu ayau, Siyasa
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a matsayin shugaban da ba'a taba yin irinsa ba wajan jajircewa da yiwa Najeriya aiki. Ya bayyana hakane jiya kamar yanda jaridar thisday ta bayyana. Yace shugabanci ba da karfin jiki ake yinsa ba, da kaifin tunani ake yinsa dan haka a daina alakanta lafiyar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da shugabancin da yake. Ya kuma yi Allah wadai da wadanda suka rika yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dariya a ranar Dimokradiyya data gabata.
DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin cire kowanne irin haraji akan magunguna da kayan asibiti da ake shigowa da su ƙasar nan

DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin cire kowanne irin haraji akan magunguna da kayan asibiti da ake shigowa da su ƙasar nan

labaran tinubu ayau, Siyasa
Cire harajin ya shafi kayan asibiti da suka haɗa da magunguna na ƙwayoyi da na ruwa, sirinji da allurai, sanke na rigakafin cizon sauro, abubuwan gwaji na gaggawa, da sauran kayan amfani a asibiti na yau da kullum. Hakazalika, umarnin na shugaban ƙasa zai ƙara ƙarfafawa masana'antun sarrafa magunguna da kayan asibiti na cikin gida wajen kara inganta su da samar da su a wadace. Wannan zai rage farashin magunguna da kuma wadatar su a lunguna da saƙon kasar nan don amfanin ƴan Najeriya.