Fasarar Jawabim Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Na Murnar Cikar Nijeriya Shekaru 25 A Mulkin Dimokradiyya
RANAR DEMOKARADIYA.12/JUNE/2024.
Ya ku yan uwanayan Najeriya bari mu fara da taya juna murnar sake ganin zagayowar ranar Demokaradiya a yau, ranar sha biyu ga watan Yunin shekara ta dubu biyu da ashirin da hudu. Wannan ranar ta zo dai dai da cikar kasar mu shekaru Ashirin da biyar a cikin mulkin Demokaradiya ba tare da katsewa ba.
A rana irin ta yau, shekaru talatin da daya baya, muka kaddamar da kudirin mu na zamowa al`ummar da ta yi cikakkiyar amincewa da Demokaradiya.
Ba abu ne mai sauki ba, kusan ma cike yake da hadarin gaske ta inda cikin shekaru shida da suka biyo baya sai da duk muka rikide muka zamoyan gwagwarmayar kwatan yancin kanmu a matsayin mu nayan kasa kuma halittun Allah a ban kasa.
A cikin wannan gwagwarmayar, mun rasa rayukan gwaraza maza da mata. Ciki kuwa ha...