Sunday, January 26
Shadow

Siyasa

Yajin Aikin NLC:Lamura sun tsaya jik a Abuja

Yajin Aikin NLC:Lamura sun tsaya jik a Abuja

Siyasa
Rahotanni sun bayyana cewa tituna da ma'aikatu babu mutane sosai a Abuja saboda yajin aikin da kungiyar kwadago ta NLC ta tsunduma a yau, Litinin. Rahoton yace babbar kotun kasa, ma'aikatar mata ta tarayya, da sauransu duk an kulle saboda yajin aikin. Kungiyar NLC dai ta shiga yajin aikinne saboda nuna rashin jin dadin Naira dubu 60 da gwamnatin tarayya tace zata biyasu a matsayin mafi karancin Albashi.
Gwamnatin Tinubu ta ciwo bashin Naira Tiriliyan 20.1 a shekara daya da ta yi tana mulki, ko me aka yi da kudin?

Gwamnatin Tinubu ta ciwo bashin Naira Tiriliyan 20.1 a shekara daya da ta yi tana mulki, ko me aka yi da kudin?

Siyasa
Masana sun bayyana damuwa game da yawan bashin da gwamnatin tarayya ta ciwo a shekara daya data gabata. Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta ciwo bashin Naira Tiriliyan 20.1 a hannun 'yan Najeriya. Hakan na nuna cewa, yawan bashin da gwamnatin Tinubu ta ciwo ya fi wanda Gwamnatin Buhari ta ciwo a shekararta ta karshe akan mulki da kaso 117. Masana sun bayyana damuwar cewa hakan zai iya kawo karuwar hauhawar farashin kayan abinci da kara kudin ruwa na karbar bashi.
Ku Janye yajin aikin da kuke ku rungumi Sulhu da gwamnati>’Yansanda suka roki kungiyar NLC

Ku Janye yajin aikin da kuke ku rungumi Sulhu da gwamnati>’Yansanda suka roki kungiyar NLC

Siyasa
Hukumar 'yansandan Najeriya sun roki kungiyar kwadago ta NLC da ta rungumi sulhu ta janye yajin aikin data shiga. Hukumar a wata sanarwa data fitar tace tabbas kungiyar kwadago ta NLC na da ikon shiga yajin aikin amma ya kamata a bi dokar da kasa ta tanadar dan kaucewa take doka da oda. Hukumar 'yansandan tace wannan yajin aikin zai jawo fargaba da kuma dumamar yanayin siyasa. Dan hakane 'yansandan ke kira da NLC ta janye yajin aikin ta koma teburin sulhu da gwamnati. Hukumar 'yansandan ta kuma baiwa jama'a tabbacin samar da tsaro inda tace ta kai jami'anta gurare da yawa dan tabbatar da ba'a karya doka ba.
Ba zami iya biyan sama da Naira Dubu sittin(60,000) ba a matsayin mafi karancin Albashi>>Gwamnatin Tarayya

Ba zami iya biyan sama da Naira Dubu sittin(60,000) ba a matsayin mafi karancin Albashi>>Gwamnatin Tarayya

Siyasa
Gwamnatin tarayya ta jaddadawa Kungiyar Kwadago cewa, ba zata iya biyan Sama da Naira Dubu 60 ba a matsayin mafi karancin Albashi ba. Hakan na zuwane a Yau, Litinin da kungiyar ta kwadago ta fara yajin aikin sai baba ta gani. Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi ya bayyanawa kungiyar kwadagon da ma'aikatan gwamnatin tarayya cewa tafiya zuwa yajin aiki sabawa doka ne. Yace kuma zasu iya fuskantar daurin watanni 6 saboda tafiya yajin aikin. Ya bayyana cewa, har yanzu akwai tattaunawa tsakanin gwamnati da kungiyar kwadagon kuma ba'a kammala ba dan haka bai kamata kungiyar ta tafi yajin aiki ba. Ya roki kungiyar kwadagon data sake tunani kan wannan mataki data dauka inda yace bai kamata ba dan zai jefa da yawan 'yan Najeriya cikin halin kaka nikayi da wah...
Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Bauchi Ahmad Jalam ya rasu sakamakon wani hatsarin mota da ya ritsa da shi a kan hanyar Misau-Darazo ranar Asabar a cewar gwamnatin jihar

Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Bauchi Ahmad Jalam ya rasu sakamakon wani hatsarin mota da ya ritsa da shi a kan hanyar Misau-Darazo ranar Asabar a cewar gwamnatin jihar

Siyasa, Sokoto
Gwamna Bala na Jihar Bauchi Ya Halarci Jana'izar Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Allah Ya Karɓi Rayuwarsa A Daren Jiya Gwamna Bala Mohammed ya halarci Sallar Jana’izar Marigayi Alh Ahmad Aliyu Jalam Kwamishinan ƙananan Hukumomi na jihar Bauchi wanda ya Rasu a sakamakon hatsarin Mota Daga Bauchi Zuwa Jalam Gwamna Bala Mohammed ya bayyana shi a matsayin abokin aiki mai himma da kwazo da bayar da gudunmawar ci gaban Gwamnatin PDP a Jihar Bauchi. Ya ƙara da cewa Rasuwar Ahmed Aliyu Jalam ta haifar da zullumi tare da yin zaman makoki, yana mai rokon Allah ya ba shi AlJannati Firdausi, ya kuma baiwa iyalansa kwarin guiwar jure wannan babban rashi. Sai dai ya jajantawa ‘yan uwa da al’ummar Jalam a madadin Gwamnatin jihar da jam’iyyar PDP da daukacin al’ummar jihar Bauchi. Manyan ja...
Tsadar rayuwa: Tsohon Gwamnan jihar Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya ce sai da suka yi wa ‘yan Nijeriya gargadi kar su sake yin kuskuren zaben jam’iyyar APC a zaben 2023

Tsadar rayuwa: Tsohon Gwamnan jihar Sokoto Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya ce sai da suka yi wa ‘yan Nijeriya gargadi kar su sake yin kuskuren zaben jam’iyyar APC a zaben 2023

Siyasa
Aminu Waziri Tambuwal ya ce sun gargaɗi ƴan Najeriya kan sake zaɓen APC a 2023. Tsohon gwamnan na Sokoto ya bayyana cewa halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan yanzu, kin ɗaukar shawara ne ya kawo shi. Tambuwal ya bayyana hakane a wajan wani taron maau ruwa da tsaki na jam'iyyar a jihar Sokoto. Yace sun gayawa mutane, APC mulki kawai take aon samu ta ganta a ofis. Yace gashi yanzu sun samu amma sun rasa yanda zasu yi dashi.
Yanzu-Yanzu: NLC zata ci gaba da yajin aiki gobe bayan zaman sulhu da Gwamnati ya gaza cimma matsaya

Yanzu-Yanzu: NLC zata ci gaba da yajin aiki gobe bayan zaman sulhu da Gwamnati ya gaza cimma matsaya

Siyasa
Rahoton da muke samu na cewa, Kungiyar Kwadago ta NLC zata ci gaba da yajin aikin da ta dauri aniya gobe, Litinin bayan zaman sulhu da gwamnati ya ci tura. A yau lahadi ne dai aka zauna tsakanin wakilan gwamnatin tarayya daga majalisar tarayya da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC dan cimma matsaya kan mafi karancin Albashi, saidai an kare zaman ba tare da cimma matsaya ba. Da misalin karfe 5:50 PM ne dai aka fara zaman inda aka kareshi da misalin karfe 8:45 PM. Kakakin majalisar dattijai, Godswill Akpabio bayan taron, ya gayawa manema labarai cewa gwamnati ta roki kungiyoyin kwadagon kan su janye yajin aikin nasu amma suka kiya. Akpabio yace idan aka yi yajin aiki, abubuwa da yawa hadda asibitoci a kasarnan zasu tsaya cik. Duk da haka dai ya sake rokon kungiyoyin kwadagon da ...