‘Gwamnati za ta ci gaba da biyan ma’aikata ƙarin albashin wucin gadi’
Gwmanatin Najeriya ta ce za ta ci gaba da bai wa ma'aikatan ƙasar ƙarin albashin wucin gadi - da ta fara biya wata shida ta suka gabata - har zuwa lokacin da za a kammala cimma matsaya kan mafi ƙarancin albashi a ƙasar.
Cikin wani jawabi da ya yi wa manema labarai ranar Asabar a Abuja, ministan yaɗa labaran ƙasar, Mohammed Idris ya ce wa'adin mafi ƙarancin albashi da aka yi a shekarar 2019 ya ƙare ne ranar, 8 ga watan Afrilun 2024.
Sai dai ministan bai bayyana adadin kuɗin da gwamnatin ke biya a matsayin albashin wucin gadin ba, to a baya gwamnatin ta ce za ta riƙa biyan ma'aikatan ƙarin naira 35,000 a kan albashinsu kowane wata har na tsawon wata shida.
A ranar juma'a ne dai ƙungiyoyin ƙwadogon ƙasar suka ce za su tsunduma yajin aiki daga gobe Litinin, kasancewar wa'adin ranar 31...