Dubu saba’in din da aka kara mana a matsayin mafi karancin Albashi a yanzu bata da amfani Saboda farashin Man fetur>>NLC
Kungiyar Kwadago ta NLC ta bayyana cewa karin albashin da aka mata na Naira Dubu 70 bashi da Amfani a yanzu saboda tashin farashin man fetur.
Kungiyar ta bayyana hakane ta bakin shugaban ta, Joe Ajaero inda yace Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yaudaresu suka amince da naira 700 a matsayin mafi karancin Albashi.
A yanzu dai,Kungiyar ta Kwadago zata gana da shugaban kasa dan neman mafita kan lamarin.