Wani mutum da aka yi wa duka saboda zargin wulakanta Ƙur’ani a Pakistan ya rasu
Ƴansanda a Pakistan sun ce wani mutum Kirista da wasu Musulmi suka yi wa dukan tsiya, saboda zarginsa da saɓo, a watan da ya wuce ya rasu sakamakon raunukan da aka ji masa.
An kwantar da Nazir Masih, a asibiti a birnin Rawalpindi, bayan da gungun mutanen ya far masa tare da wasu a lardin Sargodha, bayan zarginsu da wulaƙanta Alƙur'ani.
Gungun mutanen ya kuma cinna wa wani gida wuta a lokacin harin.
An kama mutum ashirin da biyar kan zargin cewa suna da hannu a harin.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'Adam sun ce ana amfani da tsauraran dokokin Pakistan a kan laifukan saɓo ta hanyar da ba ta dace ba, domin biyan wasu buƙatu na ƙashin kai ko ramuwar gayya.