Al’umma na tserewa daga ƙauye a Borno saboda barazanar ISWAP
Mayaƙan ISWAP sun bai wa mazauna Kukawa lga sanarwar su bar kauyensu ko kuma su fuskanci kisa kwanaki huɗu da kashe masunta goma sha biyar a yankin Tumbun Rogo.
Wani mazaunin garin da ya gudu daga al’ummarsa zuwa Maiduguri sa’o’i uku da samun wannan barazana, ya bayyana hakan ga gidan talabijin na Channels.
A yayin da ya ke bayar da labarin yadda lamarin yake, mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa mayakan sun tara jama’ar al’umma daban-daban a ƙaramar hukumar da sanyin safiyar Alhamis, inda suka ce su bar gidajensu kafin ranar Asabar, in ba haka ba za a kashe su.
A cewarsa, bayan da suka samu barazanar ‘yan ISWAP din, al’ummomin suka fara barin yankunansu, yayin da wasu suka tafi Kross Kauwa, wasu kuma suka tafi Monguno.
Kukawa lga ƙaramar hukuma ce a gefe...