Monday, January 13
Shadow

Jihar Jigawa

DA ƊUMI-ƊUMI: Hukumar Hisbah Ta Jihar Kano Ta Cika Hannu Da Kwamishinaɲ Jihar Jigawa yana tsaka da Làląta Da Mątar Aúrê

DA ƊUMI-ƊUMI: Hukumar Hisbah Ta Jihar Kano Ta Cika Hannu Da Kwamishinaɲ Jihar Jigawa yana tsaka da Làląta Da Mątar Aúrê

Jihar Jigawa
Biyo bayan wani sumame da ta kai dangane da bayanan da ta samu, hukumar (HISBAH) ta Jihar Kano ta yi ram! Da kwamishinan ayyuka na musamman na Jihar Jigawa, Auwal Ɗalladi Sankara, a bisa zargin láląta da mátar aúré. A rahoton da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta samu, mijin matar ne ya shigar da ƙara a gaban hukumar yana tuhumar kwamishinan da yin tarayya da matar tasa wanda hakan ya sanya hukumar yi masa ƙofar rago tare da kama shi. Majiya daga Jaridar Daily Nigerian da Sahara Reporters sun tabbatar da cewa yanzu haka kwamishinan yana tsare a hedikwatar hukumar ta (HISBAH) da ke Kano tun daren jiya Alhamis bayan kama shin, wanda kuma bayan kammala bincike ne za a gurfanar da shi a gaban kotu. Me zaku ce?
Akalla Mutane 90 ne Suka Rasu Yayin da Sama 50 Ke Asibiti Bayan Fashewar Tankar Man fetur a Jigawa

Akalla Mutane 90 ne Suka Rasu Yayin da Sama 50 Ke Asibiti Bayan Fashewar Tankar Man fetur a Jigawa

Jihar Jigawa
Rahotanni da ga jihar Jigawa na cewa a kalla mutane 100 sun rasa ransu biyo bayan fashewar tankar mai a garin Majia dake karamar hukumar Taura a jihar Jigawa. An ruwaito cewa fashewar ta auku ne a daren jiya Talata da misalin ƙarfe 11 na dare. Rahotanni na bayyana cewa akalla sama da mutum100 Kuma sun jikata sanadiyar fashewar tankar man, kamar yadda gidan Rediyon Sawaba FM Hadejia suka ruwaito.
Da Duminsa: Farashin litar man fetur ya kai Naira 937 a jihar Jigawa

Da Duminsa: Farashin litar man fetur ya kai Naira 937 a jihar Jigawa

Jihar Jigawa
Rahotanni daga jihar Jigawa na cewa, Farashin Litar mai a jihar ya kai naira 937. Hukumar kididdiga ta kasa,NBS ce ta bayyana haka a bayanan da ta fitar na farashin man fetur a watan Mayu. Hakan ya nuna ci gaba da tashin farashin man fetur din tun bayan cire tallafin man fetur. A cikin jihohin Najeriya,Jihar ta Jigawa itace ke da farashin man fetur mafi tsada sai jihar Ondo na take mata baya da farashin 882.67 sannan sai jihar Benue me farashin 882.22