Abubuwan dake kara dankon soyayya
Kara dankon soyayya tsakanin saurayi da budurwa da kuma mata da miji na da matukar amfani domin kamar shukace da aka yi, ya kamata ana bata ruwa.
Ga abubuwan dake kara dankon soyayya kamar haka:
Kyauta: Kyauta na da ya daga cikin abubuwan dake kawo soyayya da kara mata danko. Ko da mutum baya sonka idan ka fara yi mai kayauta yau da gobe, zai so ka. Kyauta ba dole sai ta kudi ba, ka lura da abinda masoyinka yake so ko kake tunanin zai so ka rika kyautata masa dashi
Kyawawan Kalamai: Kyawawan kalamai ko da ba a soyayya ba abune me kyau, ballantana ga masoya. Ya kamata masoya su rika musayar kyawawan kalamai a tsakaninsu, misali ina sonki, ko ina sonka, kana burgeni, kina burgeni, kina sanyani farin ciki, ban gajiya da kallonki, da dai sauransu.
Yabo: Yabo yana da matukar tasiri...